window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Isiyaku Muhammed, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Juma'a.

    Muna nan tafe da sababbin rahotonni gobe da safe.

    Kafin lokacin, Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Jami'o'in Jamus fiye da 60 sun dakatar da amfani da dandalin X

    Dandalin X

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'o'in ƙasar Jamus fiye da 60 sun daina amfani da dandalin sada zumunta na X saboda yadda suka ce yana ƙara zama na masu ra'ayin riƙau.

    Daga ciki akwai manyan jami'o'i kamar Jami'ar Heidelberg, da Free University of Berlin.

    Sun ce yadda dandalin ke aiki a yanzu haka ya saɓa da aƙidunsu, da fayyace abubuwa ƙarara, da gaskiya, da muhawarar siyasa, da kuma yarda da sauran al'adu a faɗin duniya.

    Mamallakin dandalin na X, Elon Musk, yana yawan nuna goyon bayansa ga jam'iyyar AfD mai ra'ayin riƙau kafin gudanar da zaɓe a Jamus ɗin cikin wata mai zuwa.

  3. Mutum huɗu sun mutu a wurin karɓar abincin sadaka a Syria

    Kafar yada labaran gwamnatin Syria ta ce aƙalla mutum huɗu ne suka mutu sannan 16 suka jikkata sakamakon turmutsutsun da ya faru a wani masalaci a birnin Damascus.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da aka sanar za a raba abinci kyauta a cikin masallacin na Ummayed.

    Jami'an tsaro sun dinga harbi a sama domin tartwatsa dandazon mutane.

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce fiye da rabin al'ummar kasar na wahala wajen samun abinci sakamakon yaƙi na tsawon shekaru kuma mutane da dama sun rasa matsugunansu

  4. EFCC ta kama 'yan China da 'yan Najeriya 105 kan zargin zamba ta intanet

    Mutanend da ake zargi da zamba a Abuja

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta kama matasa 105 a Abuja da take zargi da zambatar mutane ta intanet.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X ta ce daga cikinsu akwai 'yan China huɗu da da 'yan Najeriya 101 da ta kama yayin samamen da dakaru suka kai ranar Alhamis a Abuja.

    Ta ce gungun masu aikata laifi ne da ya ƙware wajen zambatar akasari 'yan Birtaniya ta hanyar ɗaukar matasan Najeriya aiki a matsayin ma'aikatan kula da otel-otel a faɗin duniya ta intanet.

    "Akan biya matasan dala biyar kan kowane bayani da suka yi nasarar bayarwa kan wani otel, inda daga baya zai iya kaiwa dala 10," in ji sanarwar.

    EFCC ta ce shirin wata "hanya ce mai sarƙaƙiya da ake amfani wajen zambatar mutane a Turai da sauran sassa".

  5. An fara tattaunawar kafa sabuwar gwamnati a Austria

    Austria

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masu zanga-zanga ma jerin gwano a Austria kan kafa gwamnati.

    An fara tattaunawar kafa sabuwar gwamnati a kasar Austria karkashin jagorancin jam'iyyar Freedom mai ra'ayin rikau.

    Tana kokarin kulla kawance da jamiyyar People Party mai matsakaicin ra'ayin rikau.

    Kwararru daga bangarorin biyu za su fara mayar da hankali ne kan yadda za su shawo kan ƙalubalen da gwamanti za ta fuskanta sakamakon giɓi a kasafin kudin kasar.

    Wakiliyar BBC ta ce jamiyyun biyu na da matsayi iri ɗaya kan batun da ya shafi kaura amma ra'ayinsu ya banbanta kan tallafin da ake bai wa Ukraine da kuma Tarayyar Turai.

    Jagoran jam'iyyar Freedom Party, Herbert Ka-kle, wanda ya lashe zaben da aka yi a bara, an ba shi damar kafa gwamnatin hadin kai bayan tattaunawar da suka yi da wasu manyan jam'iyyu ta gamu da cikas.

  6. IGP ya ba da umarnin kamo maharan da suka kashe 'yansanda a jihar Borno

    'Yansandan Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Babban Sufetan ‘Yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin ɗaukar matakan murƙushe waɗanda suka kai hari a hedikwatar ofishin 'yansanda na Nganzai da ke jihar Borno.

    A jiya Alhamis ne wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai wani mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar ‘ya sanda biyu, sannan wani jami’in ya samu munanan raunuka.

    "IGP Egbetokun ya bai wa AIG Kenechukwu Onwuemelie mai kula da Zone 15 umarnin tattara ƙarfi da ma'iakata da kuma aiki tare da sauran jami'an tsaro wajen tabbatar da kama miyagun da kuma gurfanar da su a gaban kotu," in ji wata sanarwa.

    Wata sanarwa da rundunar 'yansandan ta Borno ta fitar ta ce dakarunta sun yi musayar wuta da ‘yansandan da ke bakin aiki a ofishin, kafin daga bisani aka ci karfin mayakan tare da taimakon rundunar hadin gwiwa ta 'yan sa-kai da aka fi sani da JTF.

    Ta ƙara da cewa maharan sun afka wa ofishin ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, inda bayan dakaru sun hana su kutsawa ne suka jefa gurneti wanda ya kashe dakarun biyu.

    An gano ƙarin wasu makaman gurneti biyu da ba su fashe ba a wurin bayan binciken da aka gudanar bayan guduwar maharan, in ji kakakin rundunar ASP Nahum Kennel Daso.

  7. Alƙali ya yanke wa Trump hukuncin sallama ba tare da wani sharaɗi ba

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Trump ya bayyana a kotun ta bidiyo domin jin hukuncin da aka yanke masa

    Alƙalin da ke yi wa zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump shari'a kan ba da toshiyar baki ga wata 'yar fim ɗin batsa ya yanke masa hukunci.

    Mai Shari'a Juan Merchan ya yanke masa hukuncin sallama ba tare da wani sharaɗi ba a kan duka tuhuma 34 da ake yi masa.

    "Ina yi maka fatan gamawa lafiya yayin da kake shirin fara wa'adin mulki na biyu," in ji alƙalin yayin da yake zayyano hukuncin.

    Merchan ya faɗa wa kotun cewa ya fahimci sallamar Trump ita ce "hukunci ɗaya kacal da ya dace da doka ba tare da an ci mutuncin ofis mafi girma ba".

    Hukuncin na nufin Trump ba zai biya wata tara ba, ko zaman gidan yari duk da kama shi da laifi a duka tuhuma 34 da ake yi masa game da yin ƙarya a bayanan harkokin kasuwancinsa.

    Duk da haka Trump ya ce zai ɗaukaka ƙara.

  8. Amurka za ta ba da tukwuicin dala miliyan 25 ga duk wanda ya kamo Shugaban Venezuela Maduro

    Maduro

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta sanar da ƙara yawan tukwuici zuwa dala miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama shugaban Venezuela, Nicholas Maduro a ranar da za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa karo na shida.

    Ranstar da Maduro dai na cike da hamayya daga ƙasashen duniya da jagororin jam'iyyun adawa

    An kuma sanya tukwuici ga duk wanda ya bayar da bayanan da ka iya sa a kama ministan cikin gida na Venezuela, Diosdado Cabello.

    Har wayau, an sanya dala miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayani dangane da yadda za a kama ministan tsaron ƙasar, Vladimir Padrino.

  9. Kotu ta ba da sabon umarnin kama tsohon Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol

    Kotu a Koriya ta Kudu ta ba da sabon sammacin kama tsohon Shugaba Yoon Suk Yeol da aka tsige daga muƙaminsa a watan da ya gabata.

    Hukumar binciken cin hanci da rashawa ta ce a shirye take ta kama da kuma tsare Mista Yoon, bayan kusan mako ɗaya da ɗaruruwan masu gadin shugaban ƙasa da sojoji suka kafa shingayen da suka hana su karasawa fadar shugaban kasa domin kama shi.

    Masu bincike na son yi masa tambayoyi kan wasu zarge-zargen ciki har da kokarin kafa dokar soji da bai yi nasara ba a watan Disamba da ya wuce.

  10. Amurka ta mayar wa Najeriya dala miliyan 52 da aka ƙwato daga Diezani

    Diezani Madueke

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Diezani ce ministan albarkatun man fetur daga 2010 zuwa 2015

    Gwamnatin Amurka ta mayar wa Najeriya dala miliyan 52.88 da ta ce ta ƙwato daga tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta ƙasar, Diezani Alison Madueke da wasu abokanta.

    A ranar Juma'a ne Jakadan Amurka a Najeriya, Mr. Richard M. Mills, Jr, ne ya jagoranci tawagar da ta mayar da kuɗin zuwa ofishin ma'aikatar shari'ar ƙasar da ke Abuja.

    Alsion-Madueke - wadda ra riƙe muƙamin ministar albarkatun man fetur a tsohuwar gwamnatin GoodLuck Jonathan daga 2010 zuwa 2015 - an zargeta da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnati masu yawan gaske, zargin da ta sha musantawa.

    Haka kuma tana fuskatar shari'o'i masu alaƙa da cin hanci da rashawa a lokacin da take riƙe da muƙamin.

    Amurka ta ce tsohuwar Ministar tare da abokanta sun sayi rukunin gidajen alfarma a biranen California da New York da kuma mallakar jirgin ruwa na alfarma a tsibirin Galactica Star.

    Yayin da yake jawabi a wurin karɓar kuɗin, a madadin gwamnatin Najeriya, Ministan shari'ar ƙasar Lateef Fagbemi SAN ya ce mayar da kuɗin, wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa.

    A watan Nuwamban 2022 ma ƙasar ta mayar wa gwamnatin Najeriya dala miliyan 20.6 da ake zargin wani tsohon shugaban mulkin sojin ƙasar da sacewa.

  11. 'Yansanda sun kama matar da ake zargi da azabtar da 'yar kishiyarta

    'Yansanda

    Asalin hoton, Nigeria Police/X

    Rundunar 'yansandan Najeriya ta kama wata mata da ake zargi da azabtar da wata 'yar kishiyarta.

    Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a 'yan kwanakinnan an ga yadda matar ta ji wa ƙaramar yarinyar mai shekara biyar raunuka sakamakon dukan da take yi mata.

    Cikin wani saƙo da rundunar 'yansandan ta wallafa a shafinta Facebook, ta ce ta kama matar a ranar Alhamis, sannan za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kanta.

  12. Bala Mohammed ɗan siyasar jagaliya ne - Tinubu

    hotuna

    Asalin hoton, Social Media

    Fadar shugaban Najeriya, ta yi kira ga gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya daina amfani da sukar gwamnatin Tinubu a matsayin hanyar wanke kansa.

    A farkon makon nan ne wani bidiyon gwamnan ya ɓulla a shafukan sada zumunta, inda a ciki ya zargi gwamnatin Tinubu da bijiro da wasu manufofi da suka haifar da wahalhalu a ƙasar, musamman batun haraji.

    A wata ziyara ta shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ga gwamnan na jihar Bauchi, Bala Mohammed ya buƙaci Shehin malamin ya faɗa wa Tinubu cewa manufofin gwamnatinsa ba sa aiki.

    Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya fitar, ya zargi gwamnan da gudanar da "siyasa irin ta jagaliya, maimakon mayar da hankali wajen magance matsalolin da jiharsa ke fuskanta".

    Ya ƙara da cewa "burin Shugaba Tinubu shi ne gina ƙasar ta hanyar haɗa kai da gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

    ''Shugaba Tinubu mutum ne mai sauraron jama'a, wanda ya aminta da gwamnatocin jihohi,'' in ji shi.

    Dangane da batun ƙudirin haraji kuwa, Sunday Dare ya ce shugaban ya bayyana ƙarara cewa duk wanda ke da magana kan ƙudirin to yana gaban majalisar dokokin ƙasar.

    ''Kuma yin fatali ko sukar wannan tsari ya saɓa wa dimokraɗɗiya'', in ji shi.

    A saboda haka ne Sunday Dare ya buƙaci gwamnan na jihar Bauchi ya sauke nauyin da ke kansa na al'ummar jiharsa, maimakon tsayawa sukar gwamnatin Tinubu.

    ''Surutu da ihu da siyasar jagaliya ba za ta bari ya sauke nauyin mutanen Bauchi da ke wuyansa ba''.

    Tun bayan ɓullo da batun harajin, gwamnan na Bauchi na daga cikin gwamnonin arewacin ƙasar da suka riƙa suka a kansa, saboda zargin zai cutar da yankin.

  13. Habasha ta ƙaddamar da sabon tsarin hada-hadar hannayen jari

    Habasha ta ƙaddamar da sabon tsarin hada-hadar hannayen jari, shekara 50 bayan da aka rufe ta ƙarshe.

    Wannan na zuwa ne yayin da Firaministan Abiy Ahmed ke ƙoƙarin tayar da komaɗar tattalin arzikin ƙasar bayan yaƙin basasa na tsawon shekaru.

    Wani masanin tattalin arzikin Habasha ya ce saƙon da ake son a isar shi ne ƙasar na fuskantar ƙalubalen siyasa, amma tattalin arzikin ƙasar zai iya bunƙasa.

    Ofishin kasuwar hada-hadar hannayen jarin ƙasar zai kasance a benen wani katafaren gini da ke Addis Ababa babban birnin ƙasar.

    A baya-baya nan ne gwamnatin Habasha ta yi wa dokokin musayyar kuɗaɗen waje sasauci ƙarƙasin sharaɗin samun lamunin dala biliyan uku da rabi daga asusun ba da lamuni na IMF

  14. Tinubu zai tafi taron ɗorewar tattalin arziki a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

    tinubu

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tafi ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron ɗorewar tattalin arziki na duniya ta 2025 (ADSW 2025).

    Shugaban ƙasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu domin halartar taron - wanda zai gudana tsakanin 12 zuwa 18 ga watan Janairu.

    Taron - wanda zai samu halartar manyan shugabannin duniya, da masana da ƙungiyoyin fararen hula da 'yan kasuwa da masu ruwa da tsaki - zai tattauna nasarorin da aka samu a fannin tattalin arziki da zamantakewa, tare da lalubo hanyoyin ɗorewar ci gaban da aka samu.

    Cikin sanarwar bulaguron da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta ce a taron Shugaba Tinubu zai jaddada manufofin gwamnatinsa, ciki har ci gaban tattalin arziki da makamashi da sufuri da fannin lafiya.

    Haka kuma tawagar Najeriya a taron za ta gana da fadar sarkin ƙasar domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu.

    Ministan harkokin wajen ƙasar, Ambassador Yusuf Tuggar na daga cikin manyan jami'an gwamnatin da za su yi wa shugaban rakiya a taron, a cewar sanarwar.

    Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya bayan kammala taron ranar 16 ga watan Janairu.

  15. Sake ɓarkewar rikici ya haifar da asarar rayuka a jigawa

    Umar Namadi

    Asalin hoton, Jigawa State Government

    Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin wasu ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Miga a jihar Jigawa, da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan irin wannan rikici wanda ya haifar da asarar rayukan mutum tara.

    Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa rikicin - wanda ake yi wa kallon na ramuwar gayya - tsakanin ƙauyukan Gululu, da Gidan Nagare da kuma Ƴan kunama ya sake ɓarkewa ne a daren Juma'ar nan.

    Shugaban ƙaramar hukumar Jahun, Jamilu Danmalam ya tabbatar wa BBC cewa maharan sun kashe mutum 11.

    Haka nan mazanuna yankin sun ce an ƙona ƙona gidaje da kuma kashe dabbobi a lokacin harin.

    Sai dai har yanzu ba a tantance yawan mutanen da suka samu raunuka ba.

    Yanzu haka an kai waɗanda suka samu raunuka asibiti a ƙaramar hukumar Jahun da kuma Kano inda za a yi musu magani.

    Jigawa na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ta fi kasancewa cikin zaman lafiya a baya-bayan nan, sai dai ta daɗe tana fama da rikice-rikice na manoma da makiyaya.

  16. Ina shirye-shiryen ganawa da Putin - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ana shirya yadda zai gana da shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin.

    Sai dai Mista Trump bai bayyana lokacin da za a yi ganawar ba

    Yayin da yake jawabi a jihar Florida, shugaban Amurkan mai jiran gado ya ce "Putin na so mu gana, kuma muna shirya yin hakan."

    Kamfanin dillancin labarai na Rasha, Tass ya ambato kakakin gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov na cewa, har yanzu Amurka ba ta gabatar da buƙatar ganawar a hukumance ba.

    Trump ya alƙwarta tattaunawa da Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da zarar an rantsar da shi ranar 20 ga watan Janairu, sannan ya bayyana shakku kan tallafin soji da Amurka ke bai wa Ukraine.

    "Putin na son ganawarmu, kuma ya bayyana ƙarara cewa ya kamata mu kawo ƙarshen wanann yaƙi, wanda ke zubar da jinin al'umma,'' in ji shi.

    Mista Trump ya naɗa Keith Kellogg, tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, kuma tsohon babban janar a rundunar sojin ƙasar a matsayin Jakadan Amurka na musamman kan Rasha da Ukraine.

    Tuni dai Kellogg ya fara zayyana wasu tsare-tsaren da Amurka za ta bi don kawo ƙarshen yaƙin na Ukraine, ciki har da batun cewa Ukraine za ta samu ƙarin tallafin soji ne kawai idan ta amince da da tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.

  17. Nan gaba kaɗan zan fasa ƙwai - Baffa Bichi

    Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi

    Asalin hoton, FB/Abdullahi Baffa Bichi

    Bayanan hoto, Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi

    Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya yi barazanar cewa zai "fallasa maciya amana" a jihar.

    Bichi ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, duk da a ciki bai bayyana waɗanda yake nufi da 'maciya amanar' ba.

    Ya ce, "na gama aiki lafiya, sun yi mana butulci, amma yanzu ba lokacin magana ba ne. Maganganu akwai su, akwai su a rubuce, akwai muryoyi da bidiyo kuma za a fito da su sala-sala.

    "Allah ya haɗa mu da mutane marasa amana, suna kiran amana, amma ba su da ita. Mun taimake su, amma sun mana butulci.

    "Lokaci zai zo da za mu fito da zantuttuka da mutane za su ji su gane waɗanne irin al'umma ne, mutane su gane ba mutane ba ne da za a ba amana ba saboda ba su san komai ba sai butulci da cin amana," in ji shi.

    Wannan ne karo na faro da Bichi ya fito ya magana tun bayan cire shi da aka yi daga muƙamin sakataren gwamnati, wanda gwamnatin jihar Kano ta ce bisa rashin lafiya.

  18. Ƴanbindiga sun kashe jami'an sa-kai 15 a Katsina

    Dikko Radda

    Asalin hoton, Dikko Radda/Facebook

    Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta tabbatar da kai wani hari kan wasu jami’an ƙungiyar tsaro ta Community Watch Corps a jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 25.

    Lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da jami’an tsaron na Community Watch Corps, suka yi zango a garin Ɓaure na jihar ta Katsina, bayan ziyarar ta’aziyar ɗaya daga cikin abokin aikinsu da ya mutu sakamakon harin ’yanbindigar.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka shida lamarin ya shaida wa BBC cewa kwantan ɓunar-da ‘yanbindigar suka yi wa jami'an ya janyo mutuwar fiye jami'an na Community Watch Corps 10.

    ‘’Bayan sun tsaya ne, sai kwatsam ‘yanbindigar suka buɗe musu wuta, kuma sun kashe aƙalla mutum 15’’, in ji shi.

    Ya kuma ce bayan kashe mutanen ‘yanbidigar sun hana a ɗauki gawarwakinsu har sai ranar Alhamis da safe.

    Bayan kashe jami’an tsaron na ‘Community Watch Corps’, mutanen gari sun fantsama kasancewar ranar kasuwar gari ne, lamarin da ya sa aka kashe wasu daga cikinsu, inda har yanzu ba a ga wasu mutanen ba kamar yadda wasu mazauna yankin suka bayyana wa BBC.

    ‘’Sun kashe mutanen ƙauyukan yankin masu yawa, aƙalla mutanen da suka kashe sun kai mutum 25’’, a cewar wani da ya shaida lamarin.

    Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina,Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sai dai ya ce suka ci gaba da tattara bayanai.

    Yankunan ƙananan hukmomin Safana da Batsari na daga cikin yankunan jihar Katsina masu mafa da matsalar tsaro.

  19. Ƴan sa-kai sun kuɓutar da ma'aikatan gwamnati 8 da aka yi garkuwa da su a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, AFP

    Ƴan sa-kai a Pakistan sun kuɓutar da wasu ma'aikatan gwamnati twakwas da aka yi garkuwa da su a kusa da wurin hakar ma'adinai da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Laraba.

    Har yanzu ana tsare da wasu da dama a wurare daban-daban na yankin.

    Rahotanni sun bayyana cewa an jikkata uku daga cikin mazan da aka kuɓutar lokacin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da masu garkuwa da mutanen.

    Hukumomi na cewa mayaƙan Taliban na Pakistan ne suka yi garkuwa da mutanen a yankin Lakki Marwat da ke gundumar Khyber Pakh-tun-khwa.

  20. Gwamnatin Zamfara ta koka kan sare bishiyoyi domin yi gawayi

    Zamfara

    Asalin hoton, others

    Gwamnatin jihar Zamfara da ke yankin arewa masu yammacin Najeriya, ta koka kan yadda jama’a ke sare bishiyoyi domin samun gawayi ta hanyar ƙona itacen.

    Gwamantin dai ta ce hakan na barazana ga shirin da take yi na magance kwararowar hamada da zaizayar ƙasa a faɗin jihar.

    Kassim Sani Shantalin Kaura, shi ne kwamishinan muhalli da ma’adanai da albarkatun ƙasa a jihar Zamfara, ya bayyana wa BBC cewa hakan na matuƙar illa ga muhalli.