Waɗanda suka rasu a ruftawar benen Legas sun ƙaru zuwa biyar
Adadin waɗanda suka rasu a ruftawar bene a yankin Ojodu Berger da ke jihar Legas a kudancin Najeriya ya ƙaru zuwa biyar.
Haka kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce an ceto ƙarin mutum uku a cikin baraguzan ginin.
Kodinetan yanki na NEMA mai kula da yankin kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye ne ya sanar da haka a safiyar Lahadi, inda ya ce mutum biyar ne suka rasu, amma sun ceto mutum 20 jimilla.
Farinloye ya ce daga cikin waɗanda aka ceto akwai mata da maza.
"Sai dai mun ciro gawarwakin mutum biyar - mata uku maza biyu," in ji shi.