Tinubu ba ya katsalandan a ayyukan EFCC - Olukoyede

Asalin hoton, EFCC/Facebook
Shugaban hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukoyede, ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Shugaban Ƙasar Bola Tinubu, na yin amfani da hukumar wajen muzguna wa jam'iyyun adawa.
Yayin wata zantawa da gidan talbijin na Channels ta cikin shirin 'Politics Today' a ranar Laraba, Mista Olukoyede ya bayyana zarge-zargen da yunƙurin kawar da hankalin shugaban ƙasar daga ''kyawawan ayyukan da yake yi.''
Shugaban EFCCn ya ce babban abin da ke gaban shugaban ƙasar bai wuce yadda manyan ma'aikatu da hukumomin gwamnati ke gudanar da ayyukansu ba.
“Shugaban ƙasa ba shi da lokacin ɓatawa, mutane ne kawai ke son kawar da hankalinsa. Amma waɗanda ke kusa da shi za su faɗa maka cewa babu abin da yake son ji illa ƙoƙarin ingantuwar gwamnati'', in ji Mista Olukoyede.
A Najeriya dai an jima ana zargin hukumomi irin EFCC da zama karen farautar gwamnatocin da ke kan mulki da jam'iyyunsu wajen muzguna wa ƴan hamayya.
To sai dai Mista Olukoyede ya kare zarge-zargen da cewa hukumar EFCC ta kama mambobin jam'iyyar APC mai mulki masu yawa da suka aikata ba daidai ba fiye da na jam'iyyun hamayya.