Abin da ya sa ba ma zuwa duba marar lafiya - Mai sana'ar haƙar kabari

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Abin da ya sa ba ma zuwa duba marar lafiya - Mai sana'ar haƙar kabari

Masu sana'ar haƙar kabari a jihar Kano, sun koka kan yadda mutane ke yi musu kallon masu mugun fata

Isah Garba Tudun Wada, mai sana'ar a unguwar Tudun Wada da ke birnin Kano ya ce duka da cewa suna yin sana'ar ne domin taimaka wa al'umma, amma mutane na tsangamarsu saboda sana'ar tasu.

''Wasu za su riƙa cewa mu masu mugun fata ne, masu mugun tanadi''.

Ya ƙara da cewa yawanci ko dubiyar marasa lafiya ba su zuwa saboda yadda mutane ke yi musu kallo.

''Idan muka je dubiyar marasa lafiya sai su ce mun zo ne mu ja su kabari, kwanan nan ma kanwar mahaifiyata ba ta da lafiya, da na je dubo ta, bayan kwana biyu sai ta rasu, daga nan ƴan'uwa suka fara cewa ai dama na je ne domin na janyota maƙabarta'', in ji shi

''Suka riƙa cewa ai dama tunda muka ga ka zo, mun san baba ta kusa tafiya (mutuwa)''.

Mai sana'ar haƙar kabarin ya ce yakan ɗauke shi minti 20 domin haƙa kabari guda.

''Wannan idan wuri mai laushi ne kena, amma idan wuri na da tauri yakan ɗauke mu sa'a guda ko minti 50,'' in ji shi.

Ya ce sukan tona ƙaburburan da yawa su bar su, koda babu wanda za a binne, ta yadda idan an yi mutuwa sai kawai su gyara kabari domin binne gawa.

''Amma duk da haka wata rana, sai a zo maƙabartar ba a samu ko kabari guda ba'', kamar yadda ya bayyana.

Mai sana'ar haƙar kabarin ya ce a lokacin annobar korona ne suka fuskanci ƙaruwar aiki sakamakon mace-macen da aka samu saboda annobar.

A lokacin mukan wayi gari da binne mutum 25 zuwa sama

Isah Garba ya ce a kowace rana suna tona ƙaburbura aƙalla 10 ko kusa da haka, kuma a kowace rana akan binne mutum uku zuwa huɗu.

Mutumin ya ce a yanzu an fi samun mace-macen mutane fiye da shekarun baya.