...Daga Bakin Mai Ita tare da mawaƙi Habu Tsoho

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama domin kallon bidiyo
...Daga Bakin Mai Ita tare da mawaƙi Habu Tsoho

Abubakar Said - wanda aka fi sani da Habu Tsoho - mawaƙi ne kuma makaɗi da ke gudanar da ayyukansa da hannu ɗaya sakamakon larura.

Haifafen jihar Katsina ne kuma a nan ya yi rayuwarsa, har ma da karatunsa.

Ya ce tun yana ƙarami waƙa ke burge shi. "A kwana a tashi ni ma sai ga shi na fara rubutawa, har zuwa lokacin da na fara rerawa waƙa," a cewarsa.

Ya ce babban abin da ke bai wa mutane mamaki game da shi shi ne yadda yake iya yin kiɗa da hannu ɗaya kamar yadda mai hannu biyu ke yi.