Ku San Malamanku tare da Sheikh Ɗahir Inuwa Ibrahim

Ku San Malamanku tare da Sheikh Ɗahir Inuwa Ibrahim

Sheikh Ɗahir Inuwa Ibrahim ya fara karatu a makarantar Alhaji Mallam (Alhaji Maidawa) a unguwar Hero Gana, inda ya yi saukar Alƙur'ani, daga nan kuma aka sanya shi makarantar firamare a garin Pantami a cikin jihar Gombe a yanzu.

Ya fara karatun digirinsa na farko a fannin harkokin kasuwanci a Jami'ar Bayero Kano, sai dai a shekarar karatunsa ta biyu sai ya samu tallafin karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina.

Cikin abokan karatunsa har da tsohon ministan Najeriya, Sheikh Ibrahim Isah Pantami.

Sheikh Ɗahir Inuwa Ibrahim ya yi karatun digirinsa na uku a ƙasar Malaysia.

Malamin ya ce ya yi karatu a gaban malamai kamar Mallam Adamu Liman na Pantami, ya kuma karanta tajwidi da fiƙihu da tauhidi da sauran ilimin Hadisai a hannun Mallam Binyamin Adam da Usman Mahmud da Marigayi Mallam Saleh Sadauki da sauran malamai.