Da gaske ne sanyawa yaro zare a kai na tsayar da shakuwa?
Al'umma da dama a sassa daban-daban na nahiyar Afirka sun yarda da wasu camfe-camfe a kan yara kanana da kuma sauran abubuwa da suka shafi rayuwarsu.
Akasarin wadannan camfe-camfen basu da tushe bare makama a kimiyyance.
Daga ranar Litinin har zuwa Juma'a ta karshen wannan makon, BBC Hausa za ta kawo muku jerin bidiyo kan wasu camfe-camfe da iyaye mata ke yi ga jarirai.
Bidiyonmu na farko ya mayar da hankali ne kan camfin da wasu ke yi na sanyawa yaro zare a kansa idan yana shakuwa.
Likitoci suka ce wannan camfin ba shi da tushe bare makama a kimiyyance.