Yadda zafi da rashin wuta ke sa Kanawa warwason ƙanƙara

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Yadda zafi da rashin wuta ke sa Kanawa warwason ƙanƙara

A yayin da ake azumi a cikin yanayin zafin rana a wasu yankunan arewacin Najeriya, mutane na rububin sayen ƙanƙanra a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Mutanen sun kuma koka kan rashin samu ƙaƙarar sakamakon ƙarancin wutar lantarki da suka ce ana samu a birnin.

Lamarin ya sa farashin ƙanƙarar ya yi tashin gwauron zaɓo.