...Daga Bakin Mai Ita tare da Maryam Usman
A wannan mako za mu kawo muku tauraruwa Maryam Usman Na'ibawa wadda aka fi sani da Antima.
Maryam Usman wadda ƴar asalin jihar Adamawa da Borno ce an haife ta a barikin sojoji na Bukavu da ke birnin Kano.
Ta yi makarantun firamare da sakandirenta a jihar Kano, inda kuma ta je kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya - Federal Polytechnic Yola domin samun babbar difloma.