Yadda zamani ke yi wa majemar Kano barazana

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallo
Yadda zamani ke yi wa majemar Kano barazana

Dubban fatu Najeriya take fitar wa ƙasashen waje a Afirka da ma ƙetare bayan an jeme su, wasu ana ƙarasa sarrafa su zuwa abubuwan amfani daban-daban kamar jakunkuna da takalma da sauransu.

Babbar majemar Kano wadda ta samo asali tun kafin mulkin mallaka har yanzu tana ci gaba da aiki, inda majema suke wanke dubban fatu a kullum.

Fatun dabbobi kamar raƙumi da shanu da rago da kuma akuya, sai zaki da damusa da kura da jakunan dawa da macizai da sauransu ake jemewa a masana'antar.

Shugaban masu jima, Mallam Mustapha Umar ya ce a duk mako suna iya jeme fatu kamar 50,000 kuma akwai gomman matasa da ke cin abinci ta hanyar wannan sana'a.

Ya ce duk da ci gaban zamani, majemar tana fama da matsaloli kamar na rashin ruwa da gurɓata muhalli da rashin tsaro da ƙarancin samun tallafi da sauransu.