Ku San Malamanku tare da Sheikh Umar Garba Ibrahim (Dokaji)
Filin Ku San Malamanku na wannan mako, ya tattauna da malamin addinin Musulunci, Sheikh Umar Garba Ibrahim wanda aka fi sani da suna Umar Dokaji.
An haifi Sheikh Umar Dokaji ne a 1977 cikin unguwar Nassarawo da ke birnin Gombe a cikin jihar Gombe.
Ya fara karatu a Nassarawo Firamare, sannan ya yi ƙaramar sakandire ta Gandu kafin ya kammala a Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Gwamnati cikin 1996.
Ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Musulunci ta Madina, inda ya karanta fannin shari'ar Musulunci, daga nan ya koma karatu a Jami'ar American Open University, sannan ya yi karatu a Jami'ar Al-azhar da ke birnin Alƙahira.
Haka zalika, ya yi kwasa-kwasai a fannin harshen Ingilishi a Jami'ar Cambridge.
Cikin malaman da ya yi karatu a hannunsu, akwai mahaifinsa, Mallam Garba a unguwar Nassarawo, cikin birnin Gombe da Mallam Ahmadu Mai tafsiri da Mallam Sabitu. Ya yi karatun Alƙur'ani a Makarantar Laddo. Kuma ya yi karatu a hannun mahaifiyarsa.
