...Daga Bakin Mai Ita tare da Asma'u Wakili
A wannan makon mun kawo muku tattaunawa tare da tauraruwar fim ɗin Hausa Asma'u Abdullahi Wakili wadda aka fi sani da Asmee Wakili.
Ƴar asalin Jos, Asmee ta ce ta fara fim ne lokacin da take neman sana'ar da za ta yi bayan kammala karatunta na sakandare.
Ta kuma ce burinta shi ne ta zama hamshaƙiyar jaruma mai faɗa a ji a masana'antar Kannywood.