Yadda masarautar Hausawa ta Amurka ke tafiyar da ayyukanta

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda masarautar Hausawa ta Amurka ke tafiyar da ayyukanta

A tarihi, an san al'ummar Hausawa da kakkafa ƙungiyoyin da suke kira masarautu a ƙasashen duniya daban-daban inda sukan je domin aiki, karatu ko kasuwanci domin hada kai da taimakon juna.

Irin waɗannan masarautun dai ana samun su har a manyan ƙasashen Turai da Asiya da Gabas ta tsakiya ballantana ƙasashen Afrika.

Kan haka ne yayin wata ziyara da ya kai ƙasar Amurka a makonnin baya, Haruna Shehu – Tangaza ya ziyarci fadar Sarkin Hausawan Amurka da ke birnin New York inda ya zanta da sarkin Hausawan Alhaji Muhammadu Umaru Daure Ajiya.