...Daga Bakin Mai Ita tare da Garzali na shirin Daɗin Kowa
A cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako mun kawo muku tattaunawa da Amir Iliyasu (Mai Rose), wanda aka fi sani da Garzali a cikin shirin Daɗin Kowa.
Amir, wanda darakta ne, ya kuma shirya finafinai da dama tare da tsohon tauraron Kannywood, Rabilu Musa (Ibro).
Ya bayyana cewa Rabilu Musa ya taɓa ba shi wata shawara mai matuƙar muhimmanci gare shi.