'Yara ƙawayena biyar yunwa ta kashe'

Bayanan bidiyo, 'Yadda yunwa ta kashe yara ƙawayena biyar a Somaliya'
'Yara ƙawayena biyar yunwa ta kashe'

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fardhosa yarinya ce ƴar shekara 13 amma ba ta taɓa cin abinci ta koshi ba.

Sannan sau uku tana ganin fari da yunwa a tsawon rayuwarta.

Tsananin yunwa da fari sun tilasta mata koma wa sansanin ƴan gudun hijira a kudu maso yammacin Somaliya don neman abinci.

Mutum miliyan 20 ne ke fama da matsalar yunwa a yankin kusurwar Afirka.