Abin da ya kamata ku sani kan ruwan Zamzam

Saudi men offer Muslim pilgrims Zamzam water upon their arrival in the holy city of Mecca on August 7, 2019, ahead of the annual Hajj pilgrimage

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mazan Saudiya na raba Zamzam
  • Marubuci, Tanvee Ferdaus
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Rijiyar Zamzam na cikin masallacin Harami da ke birnin Makka na ƙasar Saudiyya.

Masallacin Harami shi ne wanda ya fi kowane masallaci girma a duniya, kuma a cikinsa ne Ka'aba yake.

Miliyoyin al'umma ne suka ɗauki ruwan Zamzam a matsayin ruwa mai tsarki wanda suka yi amannar yana warkar da cutuka.

Ziyartar masallacin wani ɓangare ne na aikin Hajji da musulmai ke yi, kuma yawanci suna ɗibar ruwan domin tafiya da shi gida domin rabawa ga ƴan'uwa da abokan arziƙi. An yi amannar cewa ruwan Zamzam na da wata baiwa ta musamman kasancewar rijiyarsa ba ta ƙafewa.

Mutane kusan miliyan biyu ne duk shekara ke zuwa aikin Hajji daga dukkan sassan duniya, koda yake an yi ƙiyasin cewa mutanen da ke zuwa aikin Hajjin ya zarce haka idan aka yi la'akari da ƴan ƙasar da waɗanda ke zuwa ta ruwa da ta ƙasa daga ƙasashe masu maƙwaftaka da Saudiyyar.

Officials provide Zamzam water to prospective pilgrims at Masjid al-Haram (Grand Mosque), where the Islam's holiest site the Kaaba is located

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahajjata na shan ruwan Zamzam bayan sun gama ɗawafi

Me ya sa Zamzam ke da muhimmanci ga Musulmai?

Ruwan Zamzam na da mahimmanci saboda tarihinsa a addinance.

Imam Bukhari Abdullah Ibn Abbas ya ruwaito littafin hadisi wanda aka fi sani da Sahih al-Bukhari a 860, wanda shi ne na biyu bayan Ƙur'ani da ke ɗauke da koyarwa da ƙa'idojin addinin musulunci.

An yi amannar cewa Hadisin na Sahih al-Bukhari na ɗauke ne da koyarwar Annabi Muhammad SAW wanda sahabbansa suka ruwaito da waɗanda ke da kusanci da shi.

Addinin muslinci ya yarda cewa hadisi na bayani ne kan koyarwa da kuma ɗabi'un annabi Muhammad SAW.

Sahihancin hadisan ya danganta da mahangar da kowane ɓangare na Sunna da Shi'a ke kallonsa

A mahanga ta addinin Musulunci, Allah ya samar da rijiyar Zamzam dubun-dubatar shekarun da suka gabata, a lokacin da Allah ya amsa addu'ar matar Annabi Ibrahim - Hajara a lokacin da ya bar ta a cikin rairayin hamada, ita da ɗanta ba tare da abinci ko ruwa ba.

Bayanin hakan ya zo ne a cikin Al-Qur'ani, cikin surah Ibrahim an kuma yi ƙarin bayani kan hakan a cikin litattafan addini da dama.

A cikin hadisin Sahih al-Bukhari, an yi bayanin cewa Hajara ta shiga yanayin da ta riƙa yawon neman ruwa, inda ta riƙa hawa da sauka kan wasu duwatsu biyu wato Safa da Marwa har zuwa lokacin da mala'ika Jibril ya daki ƙasa da duga-duginsa, inda ruwa ya fara ɓulɓulowa.

Fargabar kada ruwan ya ƙare ya sanya Hajara ta riƙa cewa 'zam-zam' da larabci, hakan yana nufin ruwan ya daina fitowa ya tsaya kada ya ƙare, kuma a nan ne aka samo sunan Zamzam.

A pilgrim drinks Zamzam water at the Grand Mosque in the holy city of Mecca on June 25, 2023

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ruwan Zamzam mai yawa kullum ake kai wa Madina daga Makka

Mene ne alaƙar Zamzam da aikin Hajji?

Akwai alaƙa tsakanin aikin Hajji da ruwan Zamzam. Aikin Hajji shi ne na biyar cikin shika-shikan musulunci kuma na ƙarshe. Ana yin aikin hajji ne a cikin watan Dhul Hijjah, wata na 12 na musulunci.

A wannan shekarar an fara aikin Hajji ne a mako na biyu na watan Yuni kuma za a gama a watan Yuli. Duk wani baligi musulmi wanda yake da halin zuwa kuma ya na da lafiya ya na wajabta a kansa aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa. Ana iya yin Umara a kowane lokaci.

Bayan sake gina Ka'aba, Ubangiji ya umarci annabi Ibrahim ya gayyaci mutane domin su je su yi aikin Hajji, kamar yadda Muhammad Abdur Rashid na jami'ar musulunci ta Bangladesh ya bayyana.

Matakan aikin Hajji sun haɗa da ɗawafi da Safa da Marwa wato Sa'ayi, wadannan matakan na da laƙa da matakan da Hajara ta bi a lokacin da aka samar da rijiyar Zamzam.

Shan ruwan Zamzam ba wajibi ba ne amma sunna ce, wato koyarwa ce ta annabi Muhammad, kuma yawanci mahajjata na shan ruwan Zamzam bayan kammala ɗawafi da kuma bayan kammala sa'ayi.

A Saudi worker loads carboys of "zamzam" water containers at the Zamazemah United Office in Mecca, on November 7, 2010

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, ..

Zuwan Zamzam wasu ƙasashe

Ana bai wa mahajjata ruwan Zamzam idan suka kammala ziyarar Makka.

Ana kuma ba masu ziyarar ƙwarin gwiwar tafiya da Zamzam zuwa gida, sai dai hukumomin Saudiya sun haramta tafiya da shi domin sayarwa.

Duk da wannan mataki da hukumomin ke ɗauka, an samu rahoton sayar da Zamzam ba bisa ƙa'ida ba a Birtaniya.

A watan Mayu, 2011, wani bincike na BBC ya gano yadda aka riƙa sayar da ruwan da ba na Zamzam ba a cikin robobi inda aka maƙala masu sunan Zamzam, lamarin da ya sanya Saudiyya ta ƙara tsaurara matakan tabbatar da samar da Zamzam na asali.

Cibiyar Nazarin Yanayin ƙasa ta ƙasar Saudiyya wadda ke kula da ingancin ruwan rijiyar Zamzam, ta ce ana fitar da shi daga rijiyar ta cikin bututun ƙarƙashin ƙasa domin rabawa a wuraren da ake kai wa, inda ake fitar da dubun dubatar litoci na ruwan.

Ana kai ruwan Zamzam mai yawa sosai kullum zuwa birnin Madina domin tabbatar da samar da shi a koda yaushe a masallacin annabi Muhammad.