Bai wa yara kayan zaki na saka su kazar-kazar in ji likitoci
Ku danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Likitocin yara kanana suka ce bai wa yaran kayan zaki madaidaici na saka su kazar-kazar da kuma kara musu kuzari.
Kwararriyar likitar yara Dakta Naja'atu Hamza ce ta fada wa BBC haka a cikin bidiyonmu na yau Talata wanda daya ne daga cikin jerin rahotanni da muka fara kawo muku daga ranar Litinin kan camfe-camfen da mutane suke yi a kan yara kanana.
Dakta Naja'atu ta ce bada kayan zaki ga dan karamin yaro kamar su lemu da kayan marmari ya na sanya shi watssakewa da kuma karin kuzari.
"Idan zaka bai wa yaro kayan zaki, ya kamata ka bashi wanda ba zallar sukari bane a ciki, a bai wa yaro kayan zaki wanda cikin shi zai dan sarrafa kafun sukarin ya wuce cikin jini".
Daktar ta ce "misali, kayan marmari suna taimakawa wajen karawa yara kuzari madaidaici".