Harkokin kasuwanci na komawa Maiduguri sanadin lafawar Boko Haram

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Harkokin kasuwanci na komawa Maiduguri sanadin lafawar Boko Haram

Maiduguri, babban birnin Borno, na samun habakar harkokin kasuwanci bayan kwashe shekaru masu dama jihar ta arewa maso gabas, na fama da rikicin Boko Haram.

Sashen Hausa na BBC ya kai wata ziyarar aiki ta musamman inda ya leka Monday market, babbar cibiyar harkokin saye da sayarwa da yawan hada-hada da kuma kasuwar Gamboru duka a cikin birnin.