Abubuwan da rahoton Oronsaye ya ƙunsa

Bayanan bidiyo, Abubuwan da rahoton Oronsaye ya ƙunsa
Abubuwan da rahoton Oronsaye ya ƙunsa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu a taron majalisar zartarwar tarayya na ranar Litinin 26 ga watan Fabrairu ya amince a aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye.

A 2011 ne shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin da zai yi nazari kan hanyoyin yin gyaran fuska ga tsarin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ma'aikatan tarayya, Stephen Oronsaye.