Labarin ɗalibi ɗan Saudiyya da ya sauya halitta zuwa mace - Binciken BBC

Asalin hoton, X
- Marubuci, Katy Ling
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
A lokacin da wani dan Saudiya da ya sauya halittarsa zuwa mace ta wallafa sakon halaka kanta a shafin X, masu bibiyarta sun bayyana kaduwarsu.
Miliyoyin mutane da suka karanta sakon nata sun bayyana cewar, wani lauya da ke Amurka da take ta kokarin neman samun mafaka ya shawarce ta da ta koma gida, zuwa ga ahalinta, da kasarsu, a cewarsa ba za su amince da jinsinta ba.
BBC ta gano mutumin mai suna Bader Alomair, wanda ke aiki a ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Washington DC da ke Amurka, kamar yadda bincikenmu ya nuna. Yana da alaka da komawar daliban yan Saudiyya daga Amurka mai cike da sarkakiya, ciki har da wasu mutum biyu da aka zarge su da aikata kisan kai, a lokacin da suke jami'a.
Mr. Alomair bai mayar da martani ba kan, zarge-zargen da aka yi masa ba, a binciken.
Eden Knight wanda ya futo daga masarautar ta Gabas ta tsakiya, daga iyalai masu daraja. Bayan da ya koma birnin Virginia a 2019 , a tsarin tallafin karatu na gwamantin Saudiya, a jami'ar George Mason, Eden ya yanke hukuncin sauya halittarsa daga namiji zuwa mace, ta hanyar sanya kayan mata, da dabi'u na mata.
Eden ya sami wani dandali a kafar sadarwa ta X inda ya kasance yana jin ya sami karbuwa, sannan ya fara girma a kafafen sada zumunta. Ya wallafa hoton katinta na zama ƴar Saudiyya kasar Saudiyya, kusa da sabuwar fuskarta ta mata, wadda kuma hakan ya sa hoton ya karade sassa.

Asalin hoton, X
Kasancewa masu sauya halitta a Saudiya abu ne da ba a amince da shi ba a kasar, ko dai daga banagren al'umma ko daga banagren gwamantin kasar- mun yi magana da wadan da suka sauya halitta yan kasar, da yanzu suke zaune a wajen kasar, sun shaida mana yadda suka fuskanci tsangwama, da cin zarafi ta wani banagren.
Komawa Saudiya, ka iya zama abu mai matakur wuya ga Eden. Mun kuma fahimci cewar visarta ta dalibta ta kare, a lokacin da sakon da ta wallafa ya karade duniya, wanda hakan yasa ta yanke shawarar neman mafaka a Amuka, don zama a chan din-din-din.
Eden ta ce ta sami sako daga wani tsohon abokinta, wanda ya hada ta da wani mai bicike mai zaman kansa a Amurka Michael Pocalyko. Ya sanar da ita cewar zai taimaka mata ta sami mafaka, sannan ta gayara alakarta da danginta - a cewar abokinta Hyden, wanda Eden ke zaune tare da shi a Georgia a lokacin.

Asalin hoton, Supplied
Sauran abokan ta, da suka bayyana sakon Eden gare mu, na cewar Mr. Pocalyko ya sanar da ita cewar akwai bukatar ta koma Georgia zuwa Washington DC don samun damar shigar da bayanan ta.
A cewar sako na karshe da ta wallafa a shafinta na X, a cikin watan Octoba na 2022, mai binciken sun hadu da Eden, a jirgin kasa a babbn birin Amurka. Ta sami rakiyar wani lauya dan Saudiya mai suna Bader, kamar yadda ta wallafa.
"Ina da yakinin cewar wannan zai iya yin tasiri," Eden ta bayyana a sakon da ta wallafa na karshe. Ta ce Bader ya ajiye ta a wani gida mai kyau, a kusa da Washignton DC ya kuma zaga da ni don ganin gari.
Sai dai bayan wasu lokuta, ta fara jefa ayar tambaya kan manufarsa akanta. Eden ta aikwa da kawayenta wani sako da kuma BBC ta gani cewar, Bader yana kokarin sa ta ta 'koma halittarta' ta baya.
Ta sanar da ni cewar Bader na kokarin ganin ta bar sanya kayan mata, kuma sannan ya hanata zuwa wajen koyan dabi'un mata.
Eden ta kuma sanar da abokanta da su bata shawara, ko za ta iya neman mafaka a Amurka, kuma wai tilas ne sai ta koma Saudiya, sannan zata iya samun hakan. Wani kwarare kan harkokin shige da fice a Amurka ya shaida mata cewar hakan ba da-dai bane.
A cikin watan Disambar 2022, Eden ya aikawa sako ga abokansu cewar: "Zan koma Saudiya, da lauya, tare da yi musu fatan alheri. "Sakon ta na kashe kanta da ta wallafa a shafin X ya futo karar cewar, lauyan da ake magana akai, shi ne mutumin mai suna Bader".
Ba a jima ba, Eden ta sanar da abokanta cewar komawar babban kuskure ne.
Ta aika musu sakon cewar Iyayenta, sun karbe mata fasfo, kuma gwamanti ta ta bayar da umarnin da a rufe shafinta na X. Eden ta sanar da abokata cewar tana da sahidar cewar iyayenta su ne suka dauki hayar wasy mutane don mayar da ita Saudiya, sai dai bata iya bayyana shaidar ba.
"Lauyan da ke taimaka mun da samun mafakar, na aiki ashe tare da iyaye na, a bayan ido na," tana shaida daya daga cikinsu.
"nan da wattanin masu zuwa, abokin Eden ya ce ta fara karaya da yunkurinta na tserewa daga Saudiyya.
Tana aiki ne a msatyin karamar ma'aikaciya, a wani kamfanin fasaha, kuma a cikin mutane tana bayyana kanta a mastayin namiji.
Eden ta aikawa da abokinta sako cewar tana ci gaba da koakrin ta ci gaba da dabi'un mace, amma iyayenta a lokuta daban daban suna hanata atre da kwace mata kayan matan. Abokan Eden sun shaida cewar ta yi fama da cin zarafi ta hanyar tsangwama, da kyara, inda ta kan aika vidiyon hakan ga abokanta. wadan da muka gani shi ne wand ata dauka a boye, na daya daga cikin yan uwanta na yi mata ihu, da turawa sun sauya masa tunani.
Eden ta halaka kanta a ranar 12 ga watan Marsi din 2023.
Mun so mu nemi "Bader" lauyan da Eden ta zarga da kokarin sa ta ta koma halittar ta ta baya, tare da bata shawarar komawa gida, don tambayar sa karin wasu bayanai da ke da alaka da mutuwar ta.
Mun yi ta nemansa a wajen lauyoyi daban-daban a birnin na DC, sai wani ya bayyana: Bader Alomair. Akwai takaitacen bayanai akansa, a kafafen sada zumunta, amma sai dai tsofafi bayanai ne na kwararu da ke aiki a Riyad suka bamu cikaken sunan sa da larabci, wanda daga karshe ya kai mu ga wani shafin sada zumunta na FAcebook da ya dai na amfani, kuma yana buna hotonsa a lokacin da ya ke karatu a Havard.
Sai dai majiyar ta ce wani hoto da Eden ta dauka da ke da matukar mahimmanci shi ne wanda ta dauka a gidan Mr Alomair ya ajiye ta. mun yi kokarin amfani da manhajar gano wurare ta internet don gano gidan da ke wajen Washigton DC.
Wani mutum ya shaida mana cewar ya san Eden kuma ya taba ganin ta tare da Mr Alomair.
Ya ce Eden ce ke da kayan matan, da yan kunnaye, da kayan kwalliyar, amma sai dai takan boye su don kar Mr Alomair ya gansu. Ya sanyata aske gashin kanta, sannan ya fada mata kar ta aske gemunta, a cewar shaidar.
Mun yi ta kokarin jin ta bakin Mr Alomair, amma sai dai bai ce komai ba. A lokacin da muka ziyarci adareshin da aka bamu wurin aikin lauyansa da ke DC, mun ga wani mutum da ya yi kama da shi, yana shiga cikin wata bababr motar SUV yana fita.

Mun bi bayan sa, ta hanyar bibiyar lambar motarsa, lambar na nuni da cewar ofishin jakadancin Saudiya ne da ke Washington DC ta bayar da ita, kuma mallakain motar ma'aikacin ofishin jakadancin ne.
Aikin Mr Alomair a ofishin jakadancin shi ne taimakawa dalibai yan Saudiya da ke Amurka, a cewar wani lauya da ya taba aiki da shi ya shaida mana.
Mun gano labarai da aka wallafa, na rawaito yadda Mr Alomair ya taimakawa wadan suka rasa mastugunen su a sanda aka fuskanci guguwar Hurricane a Florida. Sai dai mun kuma gano yadda taimakon nasa ke cike da sarkakiya.
A ranar 13 ga watan Octoba na 2018, wasu dalibai yan Saudiya, sun amsa tambayoyi kan mutuwar wani mai fatan zama shararen dan gambarar na zamani a North Caroline, da aka daba masa wuka, bayan sabani da ya shiga tsakaninsu.
Bayan wattani biyu da suka gabata, an sami Abdullah Hariri, da Sultan Alsuhaymi da laifin kisa.
Kwanaki 4 kawai da daba masa wukar, Mr hariri na cikin jirgin don komawa Saudiya, wani sakon imel da ya aika mana nuna cewar, ya hada da jirgin da zai koma gida, wanda shi ne majiyar mu ya sanar da mu cewar mr Alomair shi ne ya shirya wa Mr Hariri da Mr Alsuhaymi komawa gida.
Dukkan daliban biyu basu ce komai ba kan shari'ar.
Mr. Alomair ya aiko mana da takar shaidar biyan kudin jirgin a watan da ya gabata, haka kuma wani sakon na imel, wanda majiyar mu ta ce yaso a ce an sakamar sa da kudaden daga ofishin jakadancin Saudiya.

Asalin hoton, Supplied
Wata majiya ta shaida mana cewar ya yi aiki tare da shi, ya wakilici gwammon wasu dalibai yan Saudiya, da ke zaune a Amurka, kan zargin da aka taba yi musu kan gudun wuce sa'a da shaye-shaye.
"Bader kan zo taro da wani form na larabci daga ofishin jakadancin Saudiya, ya baiwa dalibai don sanya hannu, inda ya ke yi musu alkawarin cewar zai biya kudaden da suka kamata na ganin sun sami damar komawa gida."
Majiyar ta fada mana cewar daliban sun bayyana a farkin saurara tuhumar da ake yi musu, amma daga nan sai su yi batan dabo a zaman kotun na gaba, sai dai ba mu sani ba ko Mr Alomair ya taka rawa a wannan.
A 2019, hukumar tsaro ta FBI a Amurka, ta gargadi jai'an Saudiya da ke taimkawa yan kasarta tserewa daga zaman kotun da ake tuhumar su da aikata wani laifi.
"Hukumar tsaro ta FBI, ta lura da yadda jami'an kasar Saudiya, ke taimakawa yan kasarta mazauna Amurka, kaucewa dukkan wasu shari'u da ake yi musu, wanda hakan zagon kasa ne ga tsarin shari'ar Amurka. An dai yi wannan bincike ne cikin matukar sirri."
Wasu majiyoyi sun shida mana cewar Mr Alomair na ci gaba da zama tare da aiki a Amurka. Ya malaki gine gine da ake kasuwaci a birnin Washington DC, kuma a cikin watan Agusta, na 2024, da alama ya kafa wani sabon afishin aikin shari'a a Virginia, inda aka sa shi cikin jerin abokan aiki a wajen.
Michael Pocalyko, Bader Alomair da ofishin jakadancin Saudiyar da ke Washington DC, basu mayar da maratani ba kan tambayoyin da muka yi musu.
Mun tuntubi iyayen Eden, don ji daga gare su ko suna son a sanya su cikin labarin, sai dai suma basu ce uffam ba.
