Burinmu shi ne a bar yara su je makaranta a Kebbi - Zainab Nasir Idris
Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Zainab Nasir Idris ta ce ofishinta ya duƙufa wajen ganin an samar wa iyaye abin dogaro domin su riƙa bari yara na zuwa makaranta.
Ta bayyana hakan ne a tattaunawa da BBC yayin da maigidanta gwamna Nasir Idris ke cika shekara ɗaya da hawa mulki.
Jihar Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar rashin zuwan yara makaranta duk kuwa da matakan da gwamnatocin da suka gabata suka ce sun ɗauka.