…Daga Bakin Mai Ita tare da daraktan fim Hassan Giggs
Daga Bakin Mai Ita, shiri ne da ke hira da taurarin fina-finan Hausa da wasu fitattun mutane, domin yin bayani game da rayuwarsu.
A shirin na wannan makon mun tattauna da fitaccen daraktan fina-finan Hausa, Hassan Giggs wanda ya tsara fina-finai da dama a Kannywood.
Na haifi Giggs a Jihar Kano inda ya soma harkar fim da tace fina-finai a shekarar 1992. Ya ce tun lokaci ya yi ta faɗaɗa ilimi a fannin ɗaukan hoto da tsarawa da kuma shirya fina-finai.
Ya kuma bayar da labarin yadda laƙaninsa na Giggs ya samo asali da kuma yadda ya tsinci kansa a harkar fim.