Dan majalisar da ya fasa wayarsa don adawa da ƙudurin hana yaɗa labaran ƙarya

Bayanan bidiyo, Dan majalisar da ya fasa wayarsa don adawa da kudurin hana yada labaran karya
Dan majalisar da ya fasa wayarsa don adawa da ƙudurin hana yaɗa labaran ƙarya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani ɗan majalisar dokokin Turkiyya ya ragargaza wayarsa da guduma a yayin da yake jawabi a gaban majalisar.

Burak Erbay, wanda tsohon ɗan majalisa ne a jam'iyyar adawa ta Republican People's Party, ya yi hakan ne don nuna adawa da wani ƙudurin doka da gwamnati ke goyon baya na yaƙi da yaɗa labaran ƙarya a intanet.

A ƙarƙashin dokar, dole shafukan sada zumunta su ringa bayyana bayanan masu yaɗa labaran ƙarya.

Dokar za ta iya sa a ɗaure mutum tsawon shekara uku idan aka kama shi da laifi.

Masu suka sun ce, idan har ƙudurin ya zama doka, to zai tauye ƴancin faɗin albarkacin baki.