Matar da ta haihu kan hanyar tsere wa yaƙin Sudan

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Matar da ta haihu kan hanyar tsere wa yaƙin Sudan

Bayan kashe mata yara uku, wata mai gabatar da shirin rediyo da ke ɗauke da juna-biyu ta tsere wa yakin da ake yi a yankin Darfur a ƙasar Sudan tare da yin tafiyar kafa - inda ta haifi ɗa namiji a kan iyakar ƙasar da Chadi.

"Na haihu a kan hanya. Babu ungozoma ko wani a kusa da zai taimake ni. Kowa na tunanin kansa. Kowa na gudu domin tsira da ransa."

...