Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben gwamnan jihar Kano

Abba Kabir

Asalin hoton, Family

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir, wanda ake yi wa da laƙabi da Abba Gida-gida ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna.

Gawuna shi ne mataimakin gwmnan jihar Kano.

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar PDP ce ta zo ta uku, inda Sadik Wali ya samu ƙuri'u 15,957, sai kuma Sha'aban Ibrahim Sharaɗa na jam'iyyar ADP ya samu ƙuri'u 9,402.

A shekarar 2019 ne Abba Kabir ya fara takarar gwamnan kano inda ya yi takara da Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC.

Jam'iyyar NNPP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, ta kuma lashe biyu cikin uku na kujerun sanatocin Kano, sannan da mafi yawancin kujerun majalisar wakilai dag jihar ta Kano.

'Dokar hana fita'

Gwamnatin jihar Kano ta kakaba dokar hana zirga-zirga a fadin jihar na tsawon awa 24.

A wani bayani da ya fitar, mai magana da yawun gwamnan jihar Muhammad Garba, ya ce dokar ta fara aiki ne daga karfe takwas na safiyar Litinin zuwa karfe takwas na safiyar Talata.

An dai sanya dokar ce jim kadan gabanin sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara.