Ku San Malamanku tare da Sheikh Isa Ali Arzai

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Sheikh Isa Ali Arzai

An haifi Sheikh Isah Ibrahim Ali Arzai ne a unguwar Madigawa a birnin Kano.

Ya fara karatu a wajen Malam Muhammdu da Malam Hamza, kafin ya koma wajen kakansa a unguwar Arzai duk dai a birnin na Kano.

Ya ci gaba da karatu a wajen Sheikh Malam Manzo Arzai inda a nan ne ya sauke Alqur'ani har sau uku, sannan ya haddace shi.

Shehin malamin - wanda ke cikin manyan limaman Kano - ya ce yana da ilimi a kowane ɓangare na ilimin addini, musamman ilimin Fiqihu da Hadisi da tauhidi da nahawu da sauran fannoni.

''Abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba''

Malamin addinin ya ce babban abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba, a rayuwarsa shi ne yadda yawon ilimi ya kai shi har ya shiga cikin ɗakin Ka'aba.

''Wanan abu ya sa an martaba mu, an mutunta mu, domin kuwa a lokacin da muka shiga, mu kaɗai aka bari muka shiga, duk masu ɗawafi ma a lokacin korarsu aka yi''.

''Haƙiƙa wannan abu na daga cikin abubuwan da ba zan mace da su ba'', in ji shehin malamin.

Alaƙarsa da Sheikh Ja'afar

Sheikh Arzai ya ce Malam Ja'afar almajirinsa ne domin kuwa ya yi karatu a wajensa tun yana yaro.

''Ya yi karatu a wajena a GATC Gwale musamman ɓangaren ilimin Tajwidi''.

Ya ƙara da cewa baya ga makarantar GATC Gwale, Sheikh Ja'afar ya kuma yi karatu a wajen a wasu lokuta a gidansa, idan an taso daga makarantar.

Sheikh Arzai ya bayyana Sheikh Ja'afar da cewa mutum ne mai biyayya da hazaƙa, don haka ya ce har ya mutu yana ganin mutuncinsa tare da yi masa addu'a.

'Surar da nake son karantawa'

Malamin ya ce akwai surorin al'qur'ani mai girma da dama da yake jin daɗin karanta su, amma ya fi jin daɗin karanta kamar ''suratul Yusuf''.

'Abin da ke faranta mini rai'

Shehin malamin ya ce babban bain da ke faranta masa rai shi ne ya ga mutane sun zauna lafiya da junansu, kuma a kula da harkar ilimi, sannan yara su riƙa yin biyayya ga na gaba da su