'Masu shirin zanga-zanga su ɗan ƙara haƙuri Tinubu ya san da matsalarsu'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
'Masu shirin zanga-zanga su ɗan ƙara haƙuri Tinubu ya san da matsalarsu'

Ministan yaɗa labaran Najeriya ya ce nan gaba kaɗan 'yan ƙasar za su ganin sauƙin rayuwa sakamakon matakan da gwamnatin Bola Tinubu take ɓullo da su ciki har da motoci masu amfani da iskar gas na CNG domin sauƙaƙa sufuri da kammala shimfiɗa bututun gas na AKK domin samar da makamashi da farfaɗo da masana'antu. Mohammed Idris ya ce matakan wani ɓangare ne na kyautata rayuwa ga 'yan Najeriya ciki har ma da waɗanda ba ma'aikata ba, bayan ƙara mafi ƙanƙantar albashi zuwa N70,000.