Ban taɓa wani abu don cutar da Ganduje ba, kuma ba zan yi ba - Kwankwaso

Bayanan bidiyo,
Ban taɓa wani abu don cutar da Ganduje ba, kuma ba zan yi ba - Kwankwaso

Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce abin da ya faru game da shari'ar zaɓen gwamnan Kano - wadda ta kai ga zuwa har gaban Kotun Ƙoli kafin a warware ta - babban darasi ne a gare su.

Kwankwaso wanda shi ne jagoran NNPP mai adawa, da ta samu gwamna ɗaya tak a zaɓen 2023, ya ce yanzu kuma lokaci ne da za a bar waɗanda Allah ya ba mulki su tafiyar da al'amuran da za su inganta rayuwar jama'a.

A ranar Juma'a 12 ga watan Janairun 2024, ne Kotun Ƙolin Najeriya ta jingine hukunce-hukuncen ƙananan kotuna kan zaɓen jihar Kano, sannan ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.