Ku San Malamanku tare da Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun
Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikun, yana ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Najeriya, mazaunin jihar Kaduna, amma a wannan zantawa ya ce ya taso ne a garin Funtua, a can ya fara dasa ɗan ba na karatunsa.
An haifi fitaccen malamin a garin Tsibiri cikin ƙaramar hukumar Giwa.
Sheikh Sambo Rigachikun a cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako, ya ce ya koma Zariya ne sanadin gidan jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo.
Daga cikin manyan malaman da ya yi karatu a wajen su akwai Mallam Chado Funtua da Mallam Alu na Rimin Tsiwa da Mallam Adamu da ke Unguwar Ƙofar Doka da marigayi Sheikh Abubakar Muhmud Gumi.
