Andrea Brigaglia: Baturen da ya zama 'Bahaushe'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama domin ku kalli bidiyon
Andrea Brigaglia: Baturen da ya zama 'Bahaushe'

Andrea Brigaglia ɗan asalin ƙasar Italiya ya ce ya fara karanta Hausa a shekarar 1994.

Ya ce ya samu sha'awar karanta Hausa ne daga wajen mahaifinsa, wanda ƙwararre ne a ilimin hisabi da ke koyarwa a jami'a, wanda kuma ke da sha'awar al'adu da tarihin ƙasashen Afirka.

Brigaglia ya ce a haka ya samu sha'war koyon Hausa ne bayan da ya tashi ya samu littafan tarihi da al'adun Afirka a wajen mahaifinsa.

Ya ce sakamkon sha'awarsa da Hausa ya sa ya ziyarci Kano har ya musulunta aka sauya masa suna zuwa muhammad Nasirudden, aka kuma ba shi sunan Danjuma a matsayin sunan gargajiya na Hausawa.

s