Bidiyon Ku San Malamanku tare da Muhammad Nasir Adam limamin Masallacin Shehu Tijjani na Kofar Mata

Bayanan bidiyo, Muhammad Nasir Adam limamin Masallacin Shehu Tijjani na Kofar Mata

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

An haifi Mallam Muhammad Nasir Adam, wanda a yanzu shi ne shugaban majalisar limaman masallatan Juma'a na jihar Kano, a Unguwar Malamai da ke garin Batsari na jihar Katsina da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Malamin ya soma karatun allo a wurin mahaifinsa, har ma ya yi karatun littattafai iri su Ahlari da Qurdubi da Ishmawi.

Akwai kuma surukin mahaifinsa Mallam Abdulkadir wanda shi ma ya karantar da shi yana yaro.

Ya kuma tafi wani kauye da ake kira Dankar a jihar Katsina inda nan ma ya yi karatun allo .Baya ga wannan ya kuma yi karatu a kofar 'Yan daka Katsina.

Mallam Nasir ya kuma yi karatu a birnin Kano a makarantar Sheik Mallam Abdullahi Salga a Magoga.

Ya ce ko da yake bai kai matsayin da zai yi karatu a gaban Mallam ba a lokacin, wasu daga cikin manyan almajiran Mallam ne irin su Mallam Abdulmajidi da Mallam Mudi Muhammadu Salga da Mallam mai sunan Mallam.

Akwai kuma Mallam Muhammadu Kamba, cikin wadanda mallam ya yi karatu a wurinsu a Najeriya.