Yadda dinkin hula ya zama sana'ar mata a sansanin 'yan gudun hijira
Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Dinkin hula tun asali sana'ar mata ce a yankin Borno amma duk da hakan ba kowacce mace ke yi ba.
''Na koyi dinkin hulan ne daga 'yan uwa na mata a wannan sansanin, Ina gani ana yi kullum ta haka na koya'' inji wata mai dinkin hula.
Sana'ar dinkin hular da matan suke yi ta zama babbar hanyar samun kudaden shiga ga daruruwan mata da iyalan 'yan gudun hijira a yankin Borno.
''Ina sayar da hula dubu biyar, shida har dubu goma. Ta haka nake samun kudin siyan abubuwan da nake bukata''... In ji mai sana'ar.
Wasu matan sun dorawa kan su alhakin dinka hulunan da mazajensu ke sakawa a sansanin. ''Ina jin dadi idan na ga mijina ya sa hular da na dinka masa.''