Me zai hana sojojin Nijar su miƙa mulki a wata 9? - Tinubu
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umaymah Sani Abdulmumin and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙashen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Tinubu ya aike da ta'aziyyarsa ga al'ummar Afirka ta Kudu bisa iftila'in gobara
Asalin hoton, Twitter/Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyarsa da gwamnati da al'ummar Afirka ta Kudu kan mummunar gobarar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutune da dama a birnin Johannesburg.
Cikin wani saƙo da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya sanya wa hannu, Tinubu ya ce yana miƙa ta'aziya da alhinisa ga iyalan mutanen da suka mutu, sakamakon gobarar.
"A wannan mawuyacin lokacin na alhini, al'ummar Najeriya na jajanta muku kan wannan mummunan abu da ya faru".
Tinubu ya kuma yi addu'ar samun sauƙi ga mutanen da suka samu raunuka sakamakon gobarar.
Kimanin mutum 73 ne aka bayyana cewa sun mutu, yayin da 43 suka samu munanan raunuka sakamakon gobarar da tatashi a ƙasar ta Afirka ta Kudu.
Wasu rahotanni na cewa galibin mutanen da ke cikin ginin da gobarar ta rutsa da su baƙin haure ne, da kuma ke zaune a ginin ba bisa ƙa'ida ba.
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 39 tare da kama 159
Asalin hoton, Getty Images
Dakarun sojin Najeriya sun yi wa 'yan ta'adda kwanton ɓauna, inda suka kashe 39 daga cikinsu tare da kama 159 a jihohin Borno da Yobe.
Daraktan yaɗa labarai na shalkwatar tsaron ƙasar Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin wani taron manema labarai a shalkwatar tsaron ƙasar da ke Abuja.
Manjo Janar Edward Buba, ya ce dakarun ƙasar sun sha alwashin ci gaba da fatattakar mutanen da ke yi wa zaman lafiyar ƙasar zagon ƙasa.
Daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron ya ce dakarun sojin saman ƙasar sun ƙaddamar da hare-hare ta sama kan gungun 'yan ta'adda a dajin Sububu da ke Kankara a jihar Katsina, tare da wargaza sansanoninsu.
Ya ƙara da cewa dakarun rundunar Hadin Kai da ke aiki a yankin arewa maso gabashin ƙasar, sun kama manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a garuruwan Gwoza da Tarmuwa da ke jihohin Borno da Yobe.
Manjo Janar Buba ya ce farmakin da sojojin suka kai ya tilasta wa wasu 'yan ta'addan ajiye makamansu tare da kuɓutar da wasu mutane da mayaƙan suka kama da ƙwato makamai masu yawa.
Rasha za ta sake farfaɗo da yarjejeniyar fitar da abinci
Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce farfaɗo da yarjejeniyar fitar da kayan abinci ta tekun Bahar Rum na da muhimmanci sosai ga tabbatar da wadatar abinci a duniya.
Mista Fidan na jawabi ne a lokaci da yake ganawa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a Moscow.
To sai dai Mista Lavrov ya ce za a dawo da yarjejeniyar ne idan ƙasashen yamma suka bayar da tabbacin cewa ba za a sake hana Rasha fitar da nata kayan abincin da taki ba.
A watan Yuli ne Moscow ta ƙi sabunta yarjejeniyar.
Ministocin biyu sun ce shugaban kasashensu za su gana nan ba da jimawa ba,
kuma akwai yiwuwar batun safarar kayan abincin ta tekun Bahar Aswad ya kasance abin da za su mayar da hankali a kai.
Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin tallafa wa 'yan jihar
Gwamman jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya ƙaddamar da wani shiri da nufin tallafa wa al'ummar jihar, a wani yunƙuri na inganta tattalin arzikin jihar tare da ƙarfafa gwiwwa don samar da sana'o'i.
Malam Umar Namadi ya ce shirin na da nufin samar da miloniyoyi 150 a tsawon wa'adin mulkinsa.
Yayin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da bai wa mata 1000 jari domin dogaro da kansu, gwamnan ya ce shirin na daga cikin sauye-sauyen tattalin arziki da ci gaba da gwamnatinsa ta ɓullo da su.
"Gwamnatinmu ta fahimci muradun al'ummarmu, don haka muna buƙatar tallafa musu domin ba su damar cimma muradunsu''.
Gwamnan ya kuma yi kira ga mata kan irin rawar da za su iya takawa wajen haɓakar tattalin arzikin jihar.
"A bayyane take cewa mata na iya bakin ƙoƙarinsu wajen raino tare da inganta sana'o'i, don haka za mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwwa, muna sane da irin gudunmowar da suka ba mu a lokacin yaƙin neman zaɓe da bayan zaɓe'', in ji gwamnan na Jigawa.
Gwamnatin Jigawa ta rage kuɗin takin zamani daga dubu 26 zuwa 16
Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Jigawa
Tinubu ya ware naira biliyan 50 don aikin sake gina yankunan arewa - Kashim Shettima
Asalin hoton, Twitter/Kashim Shettima
Mataimakin shugaban Najeriya ya ce shugaban ƙasar ya ware naira biliyan 50 don aikin sake gina yankuna arewa maso yamma da arewa maso gabashin ƙasar, da ke ci gaba da gudana.
Sanata Kashim Shettima ya ce matakin wani yunƙuri ne na magance matsalar tsaro da yankunan ke fama da ita.
Yana wannan jawabin ne a lokacin da Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci - ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar lll - ta kai ziyara fadar shugaban ƙasar.
Tun da farko shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da ke haifar da matsin rayuwa da gwamnatinsu ke yi, sakamakon cire tallafin man fetur za su amfani 'yan ƙasar da dama a nan gaba.
Tinubu ya ce yana da yaƙinin sauye-sauyen za su amfani 'yan ƙasar a nan gaba musamman a fannonin Ilimi da ayyukan yi da lafiya da abubuwan more rayuwa.
“Najeriya ta ɗauki alƙawari, kuma sauye-sauyen za su kawo mana ci gaba mai ɗorewa, za mu gina ƙasarmu, ta yadda 'ya'yanmu za su yi alfahari da ita", in ji shugaban ƙasar.
Shugaban ya shaida wa majaliar ƙolin cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da gwamnatocin jihohi domin bunƙasa harkokin noma da kiwon dabbobi, domin fara fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare, lamarin da zai samar da ayyukan tare da samar da kudin shiga ga ƙasar.
EFCC ta mayar wa wata 'yar Birtaniya naira miliyan 25 da aka damfare ta
Asalin hoton, EFCC
Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tatalin Arzikin Najeriya Ta'annati EFCC ta mayar wa Christine Brown wata 'yar Birtaniya da aka yi zambata ta intanet, kudinta dala 26,000 kimanin naira miliyan 25.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwajaren ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, yana mai cewa ofishin hukumar reshen jihar Benin ya mayar da kuɗaden ranar Litinin
Ya ce Misis Brown ta bayyana jin dadinta tare da godiya ga hukumar bisa namijin ƙoƙarin da ta yi wajen mayar mata da kuɗaɗenta bayan ta fitar da rai da su a baya.
Mista Uwujaren ya ce matar mai shekara 70 ce ta miƙa kokenta ga hukumar bayan an damfare ta.
Matar da shaida wa hukumar cewa ta hadu da mutumin da ya damfare tan wanda ya ce sunansa John Barrowman a shafin intanet.
Da fari ya buƙaci yin ƙawance da ita, inda daga baya ya riƙa aike mata da buƙatar kuɗi, inda kuma ta riƙa tura masa maƙudan ƙaɗaɗe.
Daga ƙarshe Mista Uwajeren ya yi kira ga mutane su riƙa lura da mutanen da suke mu'amala da su a intanet, domin kauce wa faɗa wa hannun mazambata.
Jadawalin Champions League: Man United na rukuni ɗaya da Bayern Munich
Labarai da dumi-dumi, Me zai hana sojojin Nijar su miƙa mulki a wata 9? - Tinubu
Asalin hoton, Twitter/Dolusegun
Jagoran ƙungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a Nijar, su mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a cikin wata tara, kamar yadda Najeriya ta yi a shekarun 1990.
Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar na cewa a zamanin Janar Abdulsalami Abubakar cikin 1998, an kafa kwamitin miƙa mulki cikin wata tara, kuma kwamitin ya yi nasarar mayar da ƙasar kan tafarkin dimokradiyya.
Don haka, Shugaba Tinubu ya ce bai ga dalilin da zai sa a kasa yin haka a Nijar ba, matuƙar sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar, da gaske suke yi.
Tinubu na wannan jawabi ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji sa'ad Abubakar lll.
''Mai Alfarma, kada ka gaji don Allah, za ka sake koma wa Nijar. Ba za a amince da halayyar sojojin ba.
Idan suka yi sauye-sauye cikin gaggawa, to mu ma cikin hanzari za mu sassauta takunkuman da muka ƙaƙaba musu, domin rage wahalhalun da muke gani a ƙasar'', in ji shugaban na Ecowas.
Ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumai, tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi ranar 26 ga watan Yuli.
Asalin hoton, STATE HOUSE
Tun farko dai, shugabannin soji na Nijar da suka hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed sun bayyana cewa ba za su wuce tsawon shekara uku a kan mulkin ƙasar ba.
Sai dai, ƙungiyar Ecowas ta yi watsi da wannan matsayi.
Gwarzon ɗan wasa na Uefa
Erling Haaland ya zama gwarzon dan wasan Uefa na kakar 2022/23.
Haaland ya taimaka wa kungiyarsa lashe kofuna uku a kakar wasa da ta wuce, inda ya zura kwallaye 52
Asalin hoton, Getty Images
Gwarzuwar 'yar wasan Uefa
Aitana Bonmati 'yar wasan Sifaniya ce ta zama gwarzuwar 'yar wasa tsakanin takwarorinta mata
Asalin hoton, Getty Images
Gwarzuwar kocin mata ta 2022/2023
Asalin hoton, Getty Images
Sarina Wiegman kociyar tawagar mata ta IUngila ce ta lashe kyauta bayan jagorantar tawagar zuwa wasan karshe na gasar cin Kofin Duniya ta Mata, sannan ta dauki kofin Finalissima bayan doke Brazil a filin wasa na Wembley
Gwarzon koci na kakar 2022/23
Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola na Manchester City ne ya lashe kyautar gwarzon kocin maza mafi ƙwazo na Uefa na kakar wasa ta 2022/23.
Kocin na Manchester City ya taimaka wa kungiyarsa lashe kofuna uku a kakar wasa da ta wuce.
Kotun Ghana ta buƙaci a mayar wa tsohuwar minista kuɗin da aka riƙe mata
Asalin hoton, MINISTRY OF SANITATION AND WATER RESOURCES/ FACEBOOK
Babbar kotun Accra a
Ghana ta umarci ofishin mai shigar da ƙara na musamman (OSP) da ya mayar wa tsohuwar ministar ruwan sha da tsaftar muhalli Cecilia Dapaah kuɗaɗen da aka ƙwace daga hannunta, cikin kwanaki bakwai.
A halin yanzu dai
tsohuwar ministar tsaftar na ƙarƙashin
kulawar ofishin babban mai shigar da ƙarar, kan zargin cin hanci da rashawa, sakamakon ganin wasu kuɗade sama da dala miliyan ɗaya a gidanta.
Ofishin na OSP ya gabatar da buƙatar kotu na neman amincewar ta ci gaba da kula
da ƙuɗaɗen da aka kama a gidan tsohuwar ministar tare toshe asusun
ajiyarta na banki a lokacin da suke gudanar da bincike.
Shugaban Ghana Nana
Akufo-Addo, ya amince da murabus ɗin da ministar ta yi.
Wannan shawarar ta
biyo bayan ƙorafe-ƙorafen jama’a kan zargin karkatar da dala miliyan ɗaya a
gidanta na Acraa.
Sukar da ta riƙa sha ne ya sa ta yi murabus saboda yadda ta zargi wasu ma’aikatan gidanta biyu da sace wasu maƙudan ƙuɗaɗe a gidanta.
Ga ƙarain bayani daga Ibrahim Isa
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton