Bankwana
Nan za mu kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.
Buhari Muhammad Fagge ke fatan sake haɗuwa da ku a gobe idan Allah ya kaimu.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza
Nan za mu kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.
Buhari Muhammad Fagge ke fatan sake haɗuwa da ku a gobe idan Allah ya kaimu.
Asalin hoton, HB
A Najeriya, an kai wa magoya bayan jam'iyyar Labour hari yayin da suke halartar gangamin yaƙin neman zaɓe na ɗan takarar shugabancin ƙasa, Peter Obi.
'Yan sanda sun ce suna bincike game da harin da aka kai a Jihar Legas, inda aka jikkata mutum huɗu kuma aka lalata motar da suke tafe a cikinta.
Mista Obi na fatan lashe zaɓen a matsayin ɗan takara na farko da ke gaba-gaba a wata jam'iyya, wadda ba waɗanda aka saba ba da su ba; wato PDP da kuma APC mai mulki a yanzu.
Yayin da ya rage saura mako biyu a fara kaɗa ƙuri'a, shi ne ke kan gaba a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta intanet, amma wasu na kokwanto game da ko zai iya samun ƙuri'u a zaɓen.
Hukumomin Thailand a Bangkok sun kama wani ɗan Birtaniya wanda ya tserewa shari'a shekara biyar da suka gabata.
Richard Wakeling mai shekara 56, ya tsere daga Birtaniya ne a 2018, gabanin wata shari'a da zai fuskanta kan tuhumar da ake masa ta fasaƙwaurin ƙwaya cikin ƙasar da ta kai darajar dalar Amurka miliyan 10.
A wani hukunci da wata kotu ta yanke wa Wakeling a shari'ar da aka yi baya nan, ta yanke masa hukuncin shekara 11 a gidan yari.
Yayin da 'yan sandan Thailand suka kama shi a ranar Juma'a, yana ɗauke da wasu fasfo na bogi da yake neman miƙawa hukumomin burtaniya domin yi musu ɓaddakama.
Jami'an lafiya a Falasɗinu sun ce wani yaro ɗan shekara takwas da aka raunata sakamakon hari da mota a ranar Juma'a a Gabashin Birnin Ƙudus ya rasu.
An kashe wani yaron - mai shekara shida - a wurin, yayin da wani matashi kuma ya rasu daga baya sakamakon raunuka.
An harbe Bafalasɗinen da ya kai harin a wat tashar motocin bas.
A wani lamarin daban, wasu Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun harbe wani Bafalasɗine a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Wata ƙungiyar kare haƙƙi a Isra'ila ta ce an yi kisan ne yayin harin da 'yan bindiga suka kai wa Falasɗinawa.
Gwamnatin Belgium ta yi alƙawarin bai wa mutanen da girgizar ƙasa ta shafa a Turkiyya da Syria cikin gaggawa
Ministar cikin gida da lura da neman mafaka da cirani, Nicole de Moor, sun ce sun ɗauki wannan hukunci ne domin taimakawa mutanen Belgium da ke da 'yan uwa a kasashen biyu.
An bayar da umarnin cewa duk wanda ya nemi biza a cikin waɗanda lamarin ya ritsa da su a gaggauta ba su, tana cewa hakan zai taimaka waɗanda suke da burin taimako ba kuma za su iya zuwa ƙasashen da balahirar ta faru ba.
Waɗanda aka bai wa bizar kuma za a iya ƙara tsawaita masu ita a duk lokacin da suke so.
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal da ke matsayi na ɗaya a gasar Premier Ingila ta tashi kunnen doki a wasan da ta buga da Brentford a ranar Asabar.
Wannan ne karo na biyu da Arsenal ɗin ta yi ɓarin maki, a wasan farko ta yi rashin nasara a hannun Everton, da wannan dai ƙungiyar ta yi barin maki biyar a jere.
Har yanzu dai ƙungiyar na matsayin ta na ɗaya da maki 51 a saman teburi, yayin da Manchester City ke biye mata a matsayi na biyu da maki 45.
Arsenal za ta yi wasan ta na gaba ne a ranar Laraba da Manchester City da ke biye mata, karon farko kenan da za su kara tsakaninsu a wannan kakar.
Asalin hoton, Dal
Mutum ɗaya ya mutu yayin da aka kama wasu mutum biyar na daban bayan wani rikici da ya ɓarke tsakanin magoya bayan PDP da APC a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma'a lokacin da ɗan takarar PDP ke yaƙin neman zaɓe a Karamar Hukumar Maigatari.
A daidai lokacin da tawagar ta kai sakatariyar APC sai yamutsi ya ɓarke.
Cikin wata sanarwar 'yan sanda, "mutumin da aka kashe mai suna Abdullahi Isyaku ɗan shekara 37 ne da ya fito daga Gangare a Maigatari, wasu mutanen PDP ne suka kai masa hari".
"An garzaya da shi babban asibitin garin Gumel, amma daga baya ya rasu sakamakon raunukan da ya ji."
An fara gabatar da wani binciken kwakwaf kan lamari a sashen bincike da ke Dutse, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Kakakin 'yan sandan na jihar DSP Lawal Shisu Adam ya ce, an shawo kan lamarin kuma 'yan sanda na ƙoƙarin kamowa da gurfanar da waɗanda suka aikata wannan laifi gaban shari'a.
Asalin hoton, FX
Adadin waɗanda suka mutu a Turkiyya sakamakon girgizar ƙasar da ta faru ya kai 21,848, a cewar shugan ƙasar Erdogan.
Aƙalla mutum 3,553 ne aka rawaito sun mutu a Syria, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.
A wannan ƙarin adadin da aka samu a ƙasashen biyu, adadin waɗanda suka rasa rayuwarsu ya kai 25,401.
Asalin hoton, Getty Images
Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta rahotonnin da ke cewa gwamnan bankin Godwin Emefiele ya alaƙanta rashin wadatattun takardun buga sababbin kuɗi a ƙasar, kan ƙarancin takardun buga kuɗin.
Jaridar TIMES a ƙasar ce dai ta ruwaito wata majiya na shaida mata cewa Godwin Emefiele ya bayyana wa taron majalisar magabatan ƙasar cewa rashin isassun takardun buga kuɗi ne ya haddasa ƙarancin takardun sababbin kuɗin a ƙasar.
To amma a wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar ya ce babu inda gwamnan banki ya faɗi haka a lokacin da yake yi wa majalisar magabatan jawabi ranar Juma'a a fadar shugaban ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa abin da Mista Emefiele ya faɗa wa majalisar shi ne hukumar da ke lura da buga kuɗin na aikin buga kuɗin domin wadata 'yan ƙasar da takardun kuɗin da suke buƙata domin harkokinsu na yau-da-kullum.
''Hukumar da ke Lura da Buga Kuɗi ta Ƙasa tana da isassun kayan aikin da take buƙata wajen buga sabbin kuɗin da za su wadatar. Dan haka CBN ke kira ga jama'a da su yi watsi da rahotonnin da ke cewa babu isassun takardun buga kuɗin tare da kiran jama'a su ƙara haƙuri, kasancewar muna bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ƙara yawan kuɗin da ke yawo a hannun mutane'', in ji sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta ce akwai wani sautin murya da ke yawo a shafukan sada zumunta wanda ke zargin cewa CBN na shirin rufe wasu bankuna a ƙasar, musamman a wasu yankunan ƙasar.
Dan haka sanarwar ta ce CBN ba shi da wannan shiri, kuma saƙon da ke cikin muryar ya saɓa wa dokar tsarin banki na ƙasar.
Dan haka CBN ɗin ya shawarci 'yan ƙasar da su yi watsi da saƙon sautin muryar kasancewar ba daga bankin yake ba.
Asalin hoton, others
Kotun Ƙolin Najeriya ta gargaɗi masu sukarta game da hukuncin da ta yanke da ya bai wa shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmada Lawan da Sanata Godswill Akpabio, nasara a matsayin halastattun 'yan takarar sanata a jam'iyyar APC.
Kotun Ƙolin dai ta umarci hukumar zaɓen ƙasar INEC da ta amince da sunayen sanatocin biyu a matsayin 'yan takarar kujerun sanata a jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar a babban zaɓen ƙasar da ke tafe ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Tun bayan wannan hukunci ne dai mutane ke ciki gaba da sukar kotun da ɓangaren shari'ar ƙasar, ciki har da fitaccen marubucin nan Farfesa Faroq Kperogi, ɗan Najeriya mazaunin Amurka.
A wata sanarwa da Kotun Ƙolin ƙasar ta fitar da hannun daraktan yaɗa labaranta Dakta Festus Akande ta gargaɗi masu sukar kotun da su guji aikata hakan.
Kotun ta jadadda cewa ''Mu ba 'yan siyasa ba ne, kuma ba za mu zama 'yan siyasa ba, dan haka bai kamata a ɗauke mu a wannan matsayi ba. Babu ra'ayin wani mutum da zai fi ra'ayin kowa. Najeriya gaba take da kowa- da-kowa, dan haka waɗannan kalamai sun isa haka''.
Asalin hoton, Katsina Gov. House
Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yamacin Najeriya Aminu Bello Masari ya kafa kwamiti mai mambobi 13 da zai gudanar da bincike kan kisan 'yan sa kai sama da 100 da aka yi a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Kankara da Bakori a jihar.
A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Al-amin Isa, ya aike wa manema labarai, ya ce ana sa ran kwamitin ƙarkashin jagorancin Hon. Justice A.B. Abdullahi, zai gudanar da bincike domin gano abun da ya haddasa kashe-kashen a waɗannan garuruwa.
Sauran ayyukan da ake sa ran kamitin zai gudanar sun haɗa da yin bincike domin gano adadin rayuka da dukiyoyin da ka rasa a lokacin kashe-kashen.
Tare da gano yawan mutanen da harin ya shafa sannan da gano ƙungiyoyi ko mutanen da ke da suka aikata ko suke da hannu wajen wannan aika-aika.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na duba yiyuwar tallafa wa waɗanda lamarin ya rusta da su tare da iyalan mamatan, da bayar da shawarar ɗaukar matakan kare kai da bai saɓa wa doka ba, tare da ɗaukar matakai domin kare aukuwar makamancin wannan hari a nan gaba a jihar.
A makon da ya gabata ne dai rahotonni suka ce 'yan bindiga sun yi wa wasu 'yan sakai waɗanda ke ƙoƙarin ƙwato wasu shanun sata, kwanton ɓauna tare da kashe sama da 100 a wasu garuruwa a ƙananan hukumomin Kankara da Bakori a jihar.
Asalin hoton, Reuters
Duk da raguwar fatan da ake da shi na samun mutanen da suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin da ransu, ana ci gaba da samun abubuwa na ban al'ajabi a yankin da ake ceton waɗanda girgizar ƙasar ta rutsa da su.
Kwanaki biyar tun bayan afkuwar mummunan bala'in girgizar ƙasa da ya kai maki 7.8 a Turkiyya, har yanzu ana ci gaba da zaƙulo mutane da ransu daga cikin ɓaraguzan gini.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta a ƙasar ya nuna lokacin da aka ceto wata mace mai ciki tare da ƙaramar 'yarta daga cikin wani gini da ya ruguje a birnin Gaziantep na Turkiyya bayan kwashe sa'o'i 115 maƙale cikin ginin.
An dai samu rahotonnin kuɓutar da wasu mutane ciki har da wani matashi, a wasu yankunan Turkiyya bayan sa'o'i 110 maƙale cikin ɓaraguzai.
Wani bidiyo da tawagar ceto ta Jamus ta fitar ya nuna yadda aka zaƙulo wata yarinya da ranta ƙarƙashin ɓaraguzai a birnin Kahramanmaras bayan kwashe sama da sa'o'i 110.
Haka kuma hukumar jin kai ta Turkiyya ta saki bidiyon wani mutum cikin motar ɗaukar marasa lafiya, da ta kuɓutar da ransa a kusa da Kahramanmaras.
Asalin hoton, ATIKU FACEBOOK
'Yan bindiga sun yi wa tawagar jami'an tsaron ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP Ifeanyi Okowa kwanton ɓauna tare da kashe 'yan sanda uku.
Mista Okowa shi ne gwamnan jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Rahotonni sun ce maharan sun far wa tawagar jami'an tsaron lafiar gwamnan, da suka hada da 'yan sanda huɗu a daidai garin Ihiala da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Wasu majiyoyi sun ce jami'an tsaron na kan hanyarsu ta zuwa jihar Abia, inda tsara mista Okowa zai je domin ganawa da wasu mambobin jam'iyyar PDP a jihar gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe ranar 25 ga watan da muke ciki.
Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin.
A jerin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar Ifeanyi Okowa ya miƙa sakon ta'aziyyar gwamnatin jihar da iyalansa zuwa ga iyalan mamatan, waɗanda ya bayyana a matsayin 'jajirtattu'.
Tare da yin addu'ar samun rahama a gare su, sannan kuma yi alƙawarin nema wa iylansu haƙƙinsu
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan tawagar daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP na jihar Rivers a birnin fatakwal.
Asalin hoton, NIGERIAHAJJCOM
Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, ya yi kira ga maniyyata aikin hajjin bana a jihar da su ƙara yawan kuɗin ajiyarsu.
Domin ya kai naira miliyan 2.5 mafi ƙarancin kuɗin kujera, kafin ranar 20 ga watan Fabrairun da muke ciki
Dakta Yusuf, ya faɗi hakan ne a lokacin ganawa da manyan jami'an hukumar na ƙananan hukumomin jihar 23.
Babban sakataren ya ce hakan zai taimaka wajen samun damar tura kuɗin zuwa Hukumar Alhazai ta ƙasar da wuri domin tabbatar da yawan kujerun da hukumar Alhazan ta ware wa jihar
Ya ƙara da cewa a yanzu hukumar alhazan ƙasar ta ware wa jihar Kaduna yawan kujeru 5,982 a aikin hajjin bana, yana mai cewa jihar na buƙatar ƙarin kujeru.
Asalin hoton, Getty Images
Gwaman Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin ba shi da isassun takardun da zai ishe shi buga sababbin kuɗin da ake buƙata a ƙasar.
Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron majalisar magabata ta ƙasar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa Jaridar TIMES a ƙasar.
Gwamnan Babban Bankin ya shaida wa majalisar magabatan cewa hukumar da ke lura da buga takardun kuɗin ƙasar ba ta da isassun takardun buga sababbin kuɗin, abin da ya sa aka kasa buga wadatattun takardun kuɗi da aka sabunta a ƙasar.
“Hukumar ba ta da takardun da za ta buga 500 da 1,000. Amma sun yi odar takardar daga ƙasashen Jamus da Birtaniya, to sai dai har yanzu layi bai zo kansu ba kasancewar akwai layi a odar, dan haka odarsu ba za ta samu yanzu ba'', in ji Emefiele.
Ya ƙara da cewa “CBN ya buƙaci hukumar da ke buga kuɗin da ta buga kofin takardu miliyan 70, abin da zai isa a buga naira biliyan 126 da za a sake su, su zagaya hannun mutane a wannan rana ta Juma'a, to amma hukumar ba ta da isassun takardun da za ta yi wannan aiki''. Kamar yadda majiyar ta shaida wa jaridar TIMES.
A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya alƙawarta cewa za a shawo kan matsalar cikin kwana bakwai.
Tuni dai wasu jihohin ƙasar sun shigar da ƙarar gwamnatin tarayya da Babban Bankin domin ƙara wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.
Lamarin da ya sa Kotun Ƙolin ƙasar ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗin har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun da muke ciki, lokacin da za ta yanke hukunci kan lamarin.
Shirin Gane Mini Hanya a wannan makon ya tattauna ne kan matsalar fyaɗe da ke ci wa wasu al'umomin arewacin Najeriya tuwo a ƙwarya
Asalin hoton, ZAMFARA STATE GOVERNMENT
Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Muhammad Bello Matawalle ya bayar da umarnin kama duk mutumin da ya ƙi karɓar tsofaffin takardun kuɗi a jihar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya fitar, gwamnan ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har zuwa lokacin da kotun ƙolin ƙasar za ta bayar da hukuncin ƙarshe game da ƙarar jihohin arewacin ƙasar uku suka kai gabanta suna ƙalubalantar matakin.
A makon da ya gabata ne dai jihohin Kaduna da Kogi da kuma zamfara suka kai Babban Bankin ƙasar da gwamnatin tarayya ƙara gaban kotun ƙolin ƙasar kan batun wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.
Gwamna Matawalle ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake rantsar da alƙalan babbar kotun jihar da sabbin masu ba shi shawara na musamman a Gusau fadar gwamnatin jihar..
Gwaman ya ce sun je kotun ƙolin ne shi da takwarorinsa gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, inda suka buƙaci kotun da ta bayar da umarnin ƙara wa'adin amfani da tsofafin takardun kuɗin.
Ya ƙara da cewa ''Wannan mataki da kotun ƙoli ta ɗauka ya taimaka wajen kare ƙasar nan daga faɗawa cikin rikice-rikice, waɗanda ka iya shafar zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar, lamarin da zai iya shafar babban zaɓen ƙasa da aka shirya gudanarwa cikin wannan wata''.
Gwamnan ya kuma bayyana farin cikinsa game da ci gaba da amfanin da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar a harkokin kasuwanci da hada-hadar yau da kullum.
"Muna gode wa Allah kasancewar mutane za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin a harkokin kasuwanci domin samun abun biyan buƙatunsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba'' in Matawalle.
Adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar kasar da aka yi a Turkiyya da Syria ya ƙaru zuwa sama da 24,000
Miliyoyin mutane sun rasa gidajensu a yankunan kuma masu aikin ceto suna ƙara mayar da hankali kan wadanda ke bukatar abinci da muhalli.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum dubu dari tara ne ke buƙatar abinci cikin gaggawa a sassan Turkiyya da Syria.
Babban jami'in jin kai na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya ce zuwa yanzu tawagar agaji biyu ce kaɗai ta isa yankunan da 'yan tawaye ke riƙe da su a Syria.
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce tana ƙoƙarin tattara tarkacen wani abu mai kama da jirgi jirgi da ba a san asalinsa ba bayan da ta harbo shi kan tekun Arctic.
Abin wanda aka ce ya kai girman ƙaramar mota, yana shawagi ne a sama kuma ana ganinsa a matsayin barazana.
A yanzu dai babu wani abu da ya nuna cewa abin da aka harbo din yana aikin sa ido ne.
Wani kakakin Pentagon bai yi wa yan jarida ƙarin bayani ba, game da inda jirgin ya fito ko ma maƙasudin kasancewarsa a sararin samaniyar Amurka.
Ministar tsaron Canada Anita Anand ta ce za su taimaka wajen tura jiragen da za su bi diddigi.
An dai fara ganin abun ranar Alhamis da daddare, to sai dai jami'ai ba su bayyana lokaci ba.
Hakan na zuwa ne mako guda bayan da Amurkan ta harbo wani balan-balan ɗin ƙasar China da aka zarga da leƙen asiri, da aka gani yana shawagi a sararin samaniyar Amurkan.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar, Abdullahi Bello Diginza ke muku sallama da fatan an wayi gari lafiya.
Ku kasance da mu a wannan rana ta Asabar domin kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.