Rufewa
A nan muka zo karshen kawo muku labarai a shafinmu na Kai-tsaye.
Da fatan kun ji dadin labaran da muka kawo muku.
Sai da safe.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Shafin da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Fauziyya Tukur and Jabir Mustapha Sambo
A nan muka zo karshen kawo muku labarai a shafinmu na Kai-tsaye.
Da fatan kun ji dadin labaran da muka kawo muku.
Sai da safe.
Asalin hoton, Getty Images
Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga zanga da ke goyon bayan sojoji, wadanda suka taru a rana ta uku a Khartoum.
Masu boren na kira a maye gurbin gwamnatin riko, wadda suka ce ita ce ta fi dacewa wajen tunkurar rikicin siyasa da na tattalin arzikin kasar.
Rahotanni sunce masu zanga zangar sun taru a gaban gidan Shugaban kasa suna kiran a kifar da gomnatin riko.
Firaminista Abdalla Hamdok ya yi taron gaggawa da majalisar ministocinsa, inda ya bayyana tashin hankalin a matsayin rikicin da yafi kowane tun bayan da aka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Albashir shekaru biyu da suka gabata.
Sai dai masu suka sun ce jami'an tsaro ne suka shirya zanga zangar domin kawo cikas ga kokarin da ake yi don mayar da kasar kan tafarkin mulkin dimokradiyya.
Asalin hoton, Reuters
Ingila za ta buga wasa daya ba tare da yan kallo ba a matsayin hukuncin nuna rashin da'a da magoya bayanta suka nuna a wasan karshe na Euro 2020 da aka yi a filin wasa na Wembley.
Hukumar shirya kwallon kafa ta Turai wato UEFA ta kuma ci tarar tawagar Three Lions fam 84,560.
Sai dai a martanin da ta yi, hukumar kwallon kafa ta Ingila ta nuna rashin jin dadinta da hukuncin na UEFA, amma kuma duk da haka ta ce ta yi na'am da shi.
Yan kallo sun rika fada da masu kula da filin Wembley da kuma yan sanda, a kokarinsu na shiga filin wasan ta karfi a ranar 11 ga watan Yuli, inda Ingila ta yi rashin nasara a wasan na karshe a hannun Italiya.
Lamarin ya sa wasu yan kallo sun jikkata, da suka hada da mahaifin kyaftin din Ingila kuma mai tsaron bayan Manchester United Harry Maguire.
Kuma a lokacin yan sandan Burtaniya suka sanar da kama mutun 51.
Asalin hoton, AFP
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa takwaransa Joe Biden na Amurka kan mutuwar tsohon ministan harkokin waje Colin Powell.
Sanarwar wadda mataimaki na musamman ga Shugaban kan yada labarai Garba Shehu ya fitar, ta bayyana marigayin a matsayin mutun nagari da duniya ta yi alfahari dashi.
Hakama Shugaba Buhari ya bayyana marigayi Powell a matsayin ba'amurike dan asalin Afrika na farko da ya rike mukami mafi girma a harkar tsaron Amurka, kuma ya yi amfani da matsayinsa wurin kulla kyakkyawar hulda da kasashen waje.
Shugaban na Najeriya ya kuma ce duniya ba za ta mance da rawar da Colin Powell ya taka ba wurin yaki da cutar shan inna da kuma takaita yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS a nahiyar Afrika.
Collin Powell ya mutu yau Litinin yana da shekaru 84.
Iyalinsa sun ce ya mutu ne sakamakon kamuwa da cutar korona.
Janar Powell soja ne da ya yi fice a aikinsa wanda ya sa ya zama jigo a gwamnatocin jam'iyyar Republicans da dama, da suka hada da babban mai ba da shawara kan tsaron kasa karkashin mulkin Ronald Regan.
Mista Powell ya kuma rike mukamin hafsan hafsoshin soji da sakataren harkokin wajen Amurka.
Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Gwamnatin Najeriya za ta kashe naira biliyan 863 wurin gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al'umma na karshen shekara.
Shirye-shirye ne na musamman da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo dasu da nufin rage wa yan kasar radadin talauci.
Shirin National Social Investments Programmes (NSIP) da ya kunshi shirin N-Power da Conditional Cash Transfer Programme (CCT), da kuma shirin raba basussuka ga kananan yan kasuwa zai lakume naira biliyan 410.
Za a kuma kashe karin naira biliyan 300 kan wasu shirye-shiryen na daban ga al'umma.
Tun a shekarar 2016 ne gwamnati mai ci a Najeriya ta bullo da shirye-shiryen tallafa wa yan kasarta don rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki.
Kuma a 2020 abubuwa sun dada nauyi ga yan Najeriya bayan bullar annobar korona, da ta yi illa ga tattalin arziki.
Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga kudancin Indiya sun ce mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya da ta kashe mutum 26 a jihar Kerala.
Daga cikin wadanda suka mutu akwai kananan yara biyar, kuma ana fargabar adadin wadanda suka mutu ya karu don har yanzu ana kan neman da dama da suka bata.
Hakama ambaliyar ta yi awon gaba da gidaje tare da datse hanyoyi.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda ake ta kokarin ceto mutane da ruwa suka jaye motocinsu.
Gundumomin Kottayam da Idukki na daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa, inda har an sami zabtarewar kasa.
Gwamnatin Najeriya ta shigar da sabbin kararraki 7 kan jagoran 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.
Kararrakin sun kunshi cin amanar kasa da ta'addanci wadanda suka kasance kari kan tuhume-tuhume da ake masa tun 2016.
Kotu ta sanar da Alhamis 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar sauraron kararrakin.
Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Ibo ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar an kai Kanu kotu.
Jaridar Vanguard a Najeriya ta ruwaito cewa ƙungiyar ta Ohanaeze ta ce bayyanar Kanu a kotu na da muhimmanci don nuna wa duniya cewa Nnamdi Kanu na ciki ƙoshin lafiya kuma za a yi masa adalci a lokacin shari'a.
Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Burtaniya ta gargadi 'yan kasar da su guji zuwa jihohi 12 a Najeriya, inda ta ce akwai yiwuwar kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan kasashen waje.
Ofishin jakadancin Burtaniya da ke Abuja ya ce akwai bayanan da ya samu cewa ana shirin kaddamar da satar 'yan kasashen waje da sunan neman kuɗin fansa ko kuma siyasa.
Jihohin sun haɗa da Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da Katsina da Zamfara da Delta da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da kuma Cross River.
Ofishin ya kuma kara da cewa an hari ma'aikatan jin-kai a wasu hare-hare da aka kaddamar arewa maso gabashin Najeriya, da suka haɗa da na garin Manguno a ranar 13 ga watan Yunin 2020.
Wani ɓangaren sanarwar ya kuma ce "yanayin tsaro ya kara tabarbarewa a arewa maso gabashin Najeriya tun 2018, kuma akwai yiwuwar sace ma'aikata 'yan kasashen waje".
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta gurfanar da wata matashiya mai shekaru 19 a gaban kotu a Yenagoa da laifin yada hoton bidiyon tsiraicin wani tsohon kusa a gwamnatin jihar Bayelsa.
Ana zargin Charlotte Delhi da yada hoton bidiyo da ya nuna tsiraicin Dr Walton Liverpool a kafafen sada zumunta da nufin tatsar naira miliyan 15 a hannunsa.
Mr Liverpool ya rike mukamin sakataren din-din-din a ma'aikatar ilimin jihar Bayelsa.
Kotu ta tuhumi Miss Charlotte da laifin yada hotunan tsiraici da nufin bata sunan Walton Liverpool,sai dai matashiyar ta musanta zargin da kotun ke mata.
Wani binciken jmai'an tsaro ya nuna cewa layin da ta yi amfani da shi wurin yada hoton bidiyon a WhatsApp na dauke da lambobin fitattun yan siyasa a jihar Bayelsa.
Asalin hoton, @OKEZIEIKPEAZU
Manyan tituna sun zama wayam, sannan shaguna da ma'aikatun gwamnati sun kasance a rufe a fadin Umuahia babban birnin jihar Abia da ke kudancin Najeriya, sakamakon kullen da kungiyar 'yan awaren Biafra ta IPOB ta saka.
Ko a baya IPOB ta saka irin wannan doka ta zama a gida, da ya hada da rufe makarantu da kasuwanni amma ba ta yi tasiri ba.
A Litinin din da ta gabata mazauna birnin Umuahia sun ce mambobin IPOB sun rika yawo da bindigogi kan tituna, suna hantarar mutane su shige gidajensu.
To sai dai mazauna babban birnin jahar ta Abia sun sami kansu cikin tsaka mai wuya, bayan da gwamnatin jahar ta yi gargaɗin cewa duk ma'aikacin da bai fito aiki ba zai fuskanci hukunci.
To amma bayanai daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa kashi 80 basu fita aiki ba a yau Litinin.
Asalin hoton, EPA
Jami'an tsaron Najeriya sun kashe 'yan bindiga 10 a kusa da Fatika da ke karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.
Hakama rahotanni sun ce wasu maharan sun jikkata a musayar wuta da jami'an tsaron.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce jami'an tsaron sun yi nasarar kubutar da wani Alhaji Abubakar Usman da aka yi garkuwa da shi.
Aruwan ya kara da cewa 'yan bindigar da suka tsere sun bar mashunan su da wata babbar bindiga da wayoyi da fitilu da kuma layu.
Ya kuma shaida cewa an kona wasu daga cikin wuraren da suke ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.
A karon farko cikin shekaru masu yawa, Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta fara aikin rigakafin cutar shan inna a fadin kasar a Afghanistan.
UNICEF ta ce suna da cikakken goyon bayan shugabannin Taliban kan aikin wanda zai fara a farkon watan Nuwamba.
Hukumar ta UNICEF ta ce kungiyar Taliban ta kuma kuduri aniyar ba da damar sanya ma'aikatan mata cikin kamfen da kuma samar da tsaro ga kungiyoyin.
A baya 'yan Taliban sun yi adawa da kamfen na allurar rigakafin zargin cewa yana daga cikin wata makarkashiya da kasashen yamma ke yi don hana Musulmai haifuwa.
Asalin hoton, Getty Images
Bakar fata na farko da ya taba rike mukamin sakataren harkokin wajan Amurka wanda kuma ya rike mukamin hafsan hafsohin kasar mafi kankantar shekaru Collin Powell ya mutu yana da shekaru 84 da haihuwa a duniya.
Iyalinsa sun ce ya mutu ne sakmakon kamuwa da cutar korona.
Janarar Powel soja ne da ya yi fice a aikinsa wanda ya sa ya zama jigo a gomnatocin jamiyyar Repbulcans da dama da suka hada da babban mai ba da shawara kan tsaron kasa karkashin mulkin Ronald Regan.
Mista Powell ya kuma rike mukamin hafsan hafsoshi sojin da sakataren harkokin wajen Amurka.
Shugaban hukumar NDLEA mai yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya, Buba Marwa, ya ce ana daf da kawo karshen matsalolin safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
Buba Marwa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya na NAN cewa da tallafin gwamnatin Najeriya da manyan masu ruwa da tsaki, Najeriya za ta yi nasara kan fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ya bayyana matsalar miyagun ƙwayoyi a Najeriya a matsayin wata annoba, sai dai ya ce hukumarsa na yin dukkan mai yiwuwa don ganin an magance matsalar kuma suna samun goyon bayan da ya dace gwamnatin tarayya.
Buba Marwa ya ce hukumar na shirin shiga ƙananan hukumomi don wayar da kan mutane.
Asalin hoton, AFP
Gabanin gurfanar da Nnamdi Kanu, shugaban ƴan awaren Biafra na IPOB a gaban kotu ranar Alhamis, ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Ibo ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar an kai Kanu kotu.
Jaridar Vanguard a Najeriya ta ruwaito cewa ƙungiyar ta Ohanaeze ta ce bayyanar Kanu a kotu na da muhimmanci don nuna wa duniya cewa Nnamdi Kanu na ciki ƙoshin lafiya kuma za a yi masa adalci a lokacin shari'a.
Idan ba a manta ba, ƙungiyar IPOB ta yi barzanar rufe duka ayyuka a Kudu masu gabashin ƙasar idan ba a kai shugaban nasu gaban kotu ba aranar.
Asalin hoton, Getty Images
Mijin yar tseren nan ta Kenya da aka kashe a gidanta, Agnes Tirop ya bayyana a kotu kan zargin kisa.
Alƙalin majistire ɗin ya ce zai ba ƴan sanda damar tsare Ibrahim Rotich tsawon kwanaki ashirin, wanda a lokacin ne za a gudanar da bincike a gani idan yana da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwar fuskantar shari'a.
An kama Mista Rotich a watan da ya gabata a birnin Mombasa da ke bakin teku.
Ƴan sanda sun ce yana ƙoƙarin tserewa ne daga ƙasar.
An gano Agnes Tirop a mace da alamun raunukan wuka a jikinta a gidanta da ke Yammacin kenya.
A watan da ya gabata ne ta yi zarra a matsayin macen da ta yi fice a tseren kilomita goma.
Asalin hoton, AFP
Wani jami'i a lardin Cabo Delgado mai arziƙin iskar gas a arewacin Mozambique ya alaƙanta ƴan bindiga masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci da suka addabi yankin, da safarar miyagun ƙwayoyi bayan gano wasu miyagun ƙwayoyin a sansanoninsu na da.
Kwanan nan ne dakarun gwamnati suka ƙwace kilogram 250 na miyagun ƙwayoyi ciki har da kilogram 42 na hodar iblis, a yankunan da a baya suke hannun yan bindigar.
Sai dai ba a bayyana wurin da ranar da aka yi kamen ba.
Ana ganin yankin a matsayin wata mashigar masu fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi.
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International ta ce an daɗe ana cin zarafin al'ummar Musulmi tsawon shekaru kusan goma a kasar.
Sun zargi gwamnatin da amincewa da hare-haren da ake kai masu a kaikaice, da kuma ƙarfafa wa masu tsananin kishin kabilar Sinhala Buddhist.
Rahoton ya nuna kin jinin Musulmi da ake yi ne ya sa gwamnati ta ɗauki matakin tursasa ƙona gawarwakin Musulmi da suka rasu sanadiyyar cutar korona, al'adar da addinin musulunci ya haramta.
Tuni dai aka sauya wannan manufar.
Hukumomin Sri Lanka ba su ce komai ba game da rahoton ba kawo yanzu.
Gabanin zaɓukan 2023 a Najeriya, Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya yi kira ga shugabanni a yankin arewa maso yammacin kasar da su ajiye bambancin siyasa don ciyar da yankin gaba.
Haka kuma, ya ƙalubalance shugabannin siyasa su 'sauya' matasa, mafi yawa waɗanda ake yi wa kallon yan bindiga, alhali halayyar aikata manyan laifuka da ake zarginsu da nunawa ana ganinta a matasan ko wane ɓangare a Najeriya ba a arewa ba kawai.
Haka kuma, ya yi kira ga iyaye da shugabannin a yankin na arewa maso yammaci su sama wa matasan yankin da ke ci gaba da ƙaruwa, ayyukan yi don gujewa barace-barace da aikata laifuka kamar ƙwace.