window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 200 a Gaza zuwa yanzu

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Nan muka zo karshe a rahotanni kai-tsaye, inda za mu rufe shafin.

    Sai kuma gobe da safe za ku iske mu da sabbin rahotannin.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. An sace farfesa da mijinta a Jihar Filato

    Bindiga

    Asalin hoton, AFP

    Rahotanni daga Jihar Filato a Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace wata malamar Jami'ar Jos da mijinta.

    Masu garkuwar sun sace Farfesa Grace Ayanbimpe da mijinta a Jos, babban birnin jihar da misalin ƙarfe 12:00 na daren Lahadi a gidansu da ke Lamingo kuma har yanzu babu labarinsu, a cewar Kwamishinan Yaɗa Labarai, Dan Manjan.

    Jihar Filato ta yi ƙaurin suna wajen rikicin ƙabilanci da na addini amma ba a fiya jin ta ba wajen ayyukan sace-sace don neman kuɗin fansa.

    Kwamishinan ya faɗa wa BBC Hausa cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen ceto malamar, yayin da tuni suka kafa dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin sace mutane don karɓar kudin fansa.

  3. Microsoft ya fara bincike kan soyayyar Bill Gates da wata ma'aikaciyar kamfanin

    Bill Gates

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Microsoft ya fara binciken ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa shi, Bill Gates, game da mu'amala da ya yi da wata mata shekara 20 da suka wuce kafin ya sauka daga muƙamin shugabancin kamfanin a 2020.

    Katafaren kamfanin na komfuta ya tabbatar cewa ya ƙaddamar da binciken ne bayan wani ƙorafi da aka yi game da halayensa tun a 2019.

    Ya ce ya ƙulla yarjejeniya da wani kamfanin shari'a sannan yana mai tallafa wa ma'aikacin da ya yi ƙorafin.

    Mai magana da yawun Mista Gates ya musanta batun cewa saukar da mai gidan nasa ya yi daga muƙamin nasa na da alaƙa da binciken.

    Labarin binciken ya zo ne bayan Bill da matarsa Melinda sun sanar da rabuwar aurensu bayan zaman shekara 27.

    Kamfanin ya faɗa a yau Litinin cewa ya samu ƙorafi a ƙarshen 2019 cewa Mista Gates "ya so ya fara soyayya" da wata ma'aikaciyar kamfanin a shekarar 2000.

  4. 'Yan sanda sun kama ɗumbin miyagun ƙwayoyi a Afirka da Gabas ta Tsakiya

    Miyagun ƙwayoyi

    Hukumar 'yan sadan ƙasa da ƙasa ta Interpol ta ce ta kama ƙwayoyi masu ɗumbin yawa a nahiyoyin Afirka da Gabas ta Tsakiya a wani samame da ta kai ƙasashe fiye da 40.

    Ƙwayoyin da aka kama a watan Maris da Afrilu sun haɗa da ƙunshin hodar ibilis kusan 1,000 da aka samu a cikin wani jirgin ruwa a kusa da gaɓar ruwan Afirka ta Kudu.

    Interpol ta ce babban kamun da ta yi shi ne na Yamai, babban birnin Nijar a samamen da ta yi wa laƙabi da Operation Lionfish.

    'Yan sanda sun buɗe wani gidan ajiyar kaya, inda suka tarar da tan 17 na tabar wiwi, wadda ta kai darajar dala miliyan 35 - ko kuma kusan naira biliyan 14.

    Ta ce da farko an ɗauko ƙwayoyin ne daga Lebanon zuwa gaɓar ruwan Lome da ke ƙasar Togo. Sannan bayan an yi tafiyar fiye da kilomita 1,000 da su zuwa Nijar, za kuma a kai su Libya.

    Interpol ta ce ayyukan masu safarar ƙwayoyi na ƙaruwa a Libya, wadda aka mayar da ita tashar sayar da ƙwaya daga Kudan Amurka.

  5. Tashin farashin kayayyaki ya ragu a Najeriya

    Naira

    Asalin hoton, Getty Images

    Tashin frashin kayayyaki a Najeriya ya ɗan ragu zuwa kashi 18.12 cikin 100 a karon farko cikin kusan shekara biyu, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasa.

    Hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar da alƙaluman ne duk da faɗuwar da darajar Najeriya ke yi a 'yan kwanakin nan.

    A watan da ya gabata ne tashin farashin ya kai ƙololuwar tashi da kashi 18.17 cikin 100, abin da ya sa masana ke ganin faɗuwar darajar Naira za ta iya ta'azzara lamarin.

    Babban Bankin Najeriya (CBN) yana so tashin farashin ya kasance tsakanin kashi 6 zuwa 9.

    Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Najeriya za ta ƙyale darajar naira ta sake karyewa a farashin gwamnati daga ranar Juma'a mai zuwa a wani yunƙuri na CBN da babu mamaki yana son ya daidaita mabambantan farashin canji ne da ake da su.

  6. Za a samar wa Yahudawa tsaro a Landan - Sadiq Khan

    Sadiq Khan

    Asalin hoton, Getty Images

    Magajin garin Landan Sadiq Khan ya ce ‘yan sanda za su je unguwannin da Yahudawa ke zaune domin ba su kariya tare da ja wa mutanen da ke shirin aikata laifukan kyamar Yahudawa kunne.

    Sadiq Khan ya ce "ina ganin babu laifi idan an yi zanga-zanga kan abin da yake faruwa mil dubu biyu daga nan, da yawa ba su ji dadin abin da ke faruwa a Gabas Ta Tsakiya ba, amma wannan ba ya nufin a nuna kyama ga Yahudawa, ba za mu yarda da haka ba a Landan.

    An kama mutum hudu a ranar Lahadi, bayan wata mota dauke da tutar Falasdinawa ta shiga wata unguwa da mafi yawan mazaunanta Yahudawa ne, kuma fasinjojin cikinta na ta zage-zage kan rikin da ke faruwa.

  7. Jami'an lafiya a Gaza na rokon a samar da magunguna don yi wa mutane magani

    Jami'an lafiya a Gaza sun yi roko a samar magunguna domin yi wa mutum sama da 1,250 magani, wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila.

    A ranar Lahadi Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fuskantar karancin man fetur, wanda kuma hakan barazana ce ga ayyukan ceto.

    Dama tuni aka samu katsewar lantarki a yankin.

    Isra'ila ta shaida wa MDD cewa babu tsaron da za a fara shiga da tankokin mai yanki kawo yanzu.

    Masar ta aika tankoki Gaza amma har yanzu ba su samu tsallaka iyakar Rafah ba.

    Ta kuma aika likitoci sama da 1,200 yankin domin bayar da agaji.

  8. 'Yan jarida a Ghana na son a kafa kwamatin bincike kan cin zarafin abokin aikinsu

    @CalebKudah

    Asalin hoton, @CalebKudah

    Ƙungiyoyin farar hula ciki har da kungiyar` yan jarida ta Ghana na kira a kafa wata hukuma ko kwamiti mai zaman kansa wanda zai gudanar da bincike dangane da zargin cin zarafin wani ɗan jarida da ake yi wa babbar hukumar tsaro ta ƙasa wato National Security.Kiraye-kirayen na zuwa ne bayan wasu jami`an hukumar sun cafke tare da sanya wa ɗan jarida Caleb Kudah na kafar yaɗa labarai ta CITI FM da ke birnin Accra ankwa.

    Jami'an na zargin ɗn jaridar da ɗaukar hoton wasu motocin alfarma da aka wofintar a farfajiyar hukumar ta National Security.

  9. Harin Isra'ila ya lalata wutar lantarki a birnin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, @Rushdibbc

    Mai shirya shiri na BBC a birnin Gaza, Rushdi Abualouf, na bayyana yadda wani harin Isra'ila a daren jiya ya lalata wutar lantarki a birnin, a ci gaba da rikici tsakaninta da ƙungiyar Hamas.

    Ya ce hukumomi na bakin ƙoƙarinsu wajen gyara wutar.

    Ya ƙara da cewa Hamas, wadda ita ce ke iko da Gaza, ta ce harin ya haifar da gagarumar matsala ga birnin.

    Yanzu haka yawan lantarkin da ta rage a Gaza ba ta wuce megawatts 107 ba yayin da ake buƙatar aƙalla 450.

    Sannan babu mai da za a iya gudanar da tashar lantarki ɗaya tilo da ake da ita a Gaza saboda kulle harkokin kasuwanci da Isra'ila ta yi zuwa cikin birnin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 200 a Gaza zuwa yanzu

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar lafiyar Falasɗinu da Hamas ke gudanarwa ta ce zuwa yanzu waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila sun kai mutum 200.

    An fara rikicin na baya-bayan nan tun ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, inda Isra'ila ke kai hari ta sama a kan birnin gaza, ita kuma ƙungiyar Hamas ke harba makaman roka zuwa biranen Isra'ila.

    Wata sanarwa ta ce yara 59 da mata 35 na cikin waɗanda suka mutu, sannan kuma an raunata 1,305.

    Isra'ila ta ce ta kashe mayaƙan Hamas guda 130 a Gaza.

    Mutum 10, ciki har da yara biyu da soja ɗaya, aka kashe a Isra'ila sakamakon harin rokar da Hamas ke harbawa daga Gaza.

  11. Ma'aikatan Kaduna sun ƙara da zanga-zanga a kan yajin aiki

    Ƙungiyar ƙwadago

    Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa a Najeriya wato Nigeria Labour Congress (NLC) ta gudanar da zanga-zanga a Jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar game da korar ma'aikata da Gwamna Nasir El-Rufa ya yi.

    Matakin ƙari ne a kan yajin aikin da ma'ailkatan suka fara a ɗaukacin jihar na kwana biyar a matsayin jan kunne ga gwamnatin jihar kan ta janye aniyarta ta korar ma'aikata 7,000.

    NLC

    Ma'aikatan sun yi cincirundo a ƙofar sakatariyar NLC kafin daga bisani suka yi maci zuwa sakatariyar gwamnatin jihar sannan suka rankaya zuwa majalisar dokoki.

    Suna ɗauke da kwalaye masu saƙonni iri-iri da ke kiran gwamnati ta janye yunƙurin korar ma'aikatan.

    Wakilin BBC a Kaduna, Yusuf Tijjani, ya ce yajin aikin ma'aikatan ya yi tasiri sosai, inda asibitocin gwamnati suka kasance babu ma'aikata sannan aka rufe tashar jirgin ƙasa da kuma filin jirgin sama.

    Kazalika, tasirinsa ya shafi mutanen gari yayin da gidajen mai suka kasance a garƙame tun a daren jiya Lahadi duk da irin kiraye-kirayen da gwamnati ta yi wa mazauna jihar da su bijire wa kiran na NLC.

  12. Faransa za ta ranta wa Sudan dala biliyan 1.5 don ta biya bashin da IMF ke bin ta

    Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Faransa ta ce za ta ara wa Sudan dala biliyan daya da rabi domin taimaka wa kasar ta biya bashin da Asusun Lamuni na Duniya ke bin ta.

    Watakila wannan ya share hanya a yafe wa kasar bashin da ake bin ta na dala biliyan 50 karkashin shirin Asusun Lamuni na Duniya da kuma Bankin duniya na yafe bashi ga kasashen da bashin ya yi musu katutu.

    Idan aka yafe wa Sudan bashin dala biyan 50 da ake bin ta, Firaiministan kasar Abdallah Hamdok zai samu kwarin gwiwa cewa kasar za ta fita daga matsin tattalin arzikin da take fama da shi.

    Sudan na fita daga takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba mata na gomman shekaru, ga kuma wariyar da ta yi fama da ita karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Omar al-bashir.

  13. Isra'ila ta kai harin da ya hallaka wani babban kwamandan Falasdinawa

    isra'ila/gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai, ya yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan Falastinawa a Gaza a dai-dai lokacin da rikici tsakanin ɓangarorin biyu ya shiga mako na biyu.

    An kai wa kwamandan mai suna Hussam Abu-Harbeed hari ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke Jabalia, haka kuma jirgin yaƙin Isra'ila ya yi wa gidajen kwamandojin Hamas tara luguden wuta.

    Sai dai kuma a ɓangaren mayaƙan na Falastinu, sun mayar da martani ta hanyar harba ƙarin rokoki zuwa birnin Isra'ila.

  14. Ƴan bindiga sun kashe mutum 4 a wani hari a jihar Rivers

    Police

    Wasu ƴan bindiga sun auka wa garin Kono Boue a karamar hukumar Khana a jihar Rivers inda suka kashe mutum huɗu.

    Jaridar Daily Trust ta ce wasu shaidu sun ce ƴan bindigar waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun shiga ƙauyen ne ɗauke da bindigogin AK47 da tsakar daren Asabar inda suka riƙa harbi har suka kashe mutum huɗun.

    Mai magana da yawun kwamitin ci gaban ƙungiyar Golden Nwibakpo ya bayyana cewa an samu ƙaruwar kashe-kashe a yankin Kono Boue.

    Nwibakpo ya bayyana cewa mutanen da aka kashen ba ƴan ƙungiyar asirin ba ne kuma mutane ne masu bin doka da oda.

    Haka kuma ya bayyana cewa lamarin ya janyo zaman ɗar-ɗar a yankin.

  15. Buhari na halartar taron tattalin arziƙi da shugabannin Afrika a Faransa

    Shugabanni daga wasu kasashen Afirka na wani taro a kasar Faransa don tattaunawa a kan hayoyin farfado da tattalin arzikin nahiyar, bayan galabaitar da ta yi daga annobar kwarona.

    Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ne ya shirya taron, inda wasu shugabanni daga nahiyar Turai da wasu hukumomi da cibiyoyin kudi, irin su bankin duniya ke halarta.

    Tuni dai shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya isa birnin Paris domin halartar taron.

    Saurari hirar da Ibrahim Isa ya yi da Mallam Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labarai.

    Bayanan sautiBuhari na halartar taron tattalin arziƙi da shugabannin Afrika a Faransa
  16. An kama mai sayar da na’urar iskar Oxygen ta hanyar cuwa-cuwa

    mace da oxygeb

    ‘Yan sanda a Delhi babban birnin Indiya sun kama wani dan kasuwa da ake zargi da sayar da na’urar tace iskar Oxygen ta hanyar cuwa-cuwa.

    Mutumin mai suna Navneet Kalra ya fara wasan buya ne da 'yan sanda bayan sun kai wani samame cikin uku daga cikin gidajen sayar da abincinsa makonni biyu da suka gabata.

    'Yan sanda sun zarge shi da shigo da na’urar tace iskar Oxygen daga China kan farashi mai sauki, sannan ya sayar da ita kan farashi mai tsada a Indiya.

    Sai dai Mista Kalra ya musanta wannan zargi.

    A baya-bayan nan kafafen yada labarai a Indiya sun ta ruwaito karuwar sayar da na’urar tace iskar Oxygen din ta hanyar cuwa-cuwa.

  17. An kama wani direba kan tsafi da sassan jikin yara ƙanana

    Binciken BBC ya gano cewa ana yankar jikin wasu yara a ɗebi jininsu a yi tsafi
    Bayanan hoto, Binciken BBC ya gano cewa ana yankar jikin wasu yara a ɗebi jininsu a yi tsafi

    Ƴan sanda a Uganda sun ce sun kama wani da ake zargi da safarar yara ƙanana yana tsafi da sassan jikinsu.

    BBC ta naɗi mutumin a wani binciken ƙwaƙwaf da ta yi a shekarar 2011.

    An kama mutumin da ake zargi, wani direban babbar mota, a garin Elegu da ke iyakar arewacin Uganda a ƙarshen makon nan.

    Mai magana da yawun ƴan sanda Fred Enanga ya tabbatar da cewa za a miƙa mutumin ga hedikwatar ƴansanda a Kampala, babban birnin kasar.

    Ya ce ƴan sanda sun san da ayyukan mutumin ne bayan da wani bidiyo da aka naɗa shekara 10 da ya wuce, ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka nuna mutumin yana cewa shi ne shugaban wata ƙungiya mai sace yara su mika su ga ƴan kungiyar asiri.

    A wani rahoto, mutumin da ake zargi ya yi wa tawagar BBC da suka yi ɓadda kama bayani kan yadda za su iya samun yaran sata.

    Mista Enanga ya ce ƴan sanda za su yi bitar zarge-zargen sannan yana kira ga duk wani wanda yake da bayani dangane da lamarin ya taimaka.

    Har zuwa wannan watan, dokokin Uganda ba su sa amfani da sassan jikin mutum a matsayin babban laifi ba.

    A farkon watan nan ne majalisar dokoki ta sa hannu kan wani ƙudirin doka wadda idan aka sa wa hannu za ta ba da damar yanke hukuncin kisa ga wanda aka kama yana amfani da sassan jikin mutum ko taimakawa wajen amfani da su.

  18. Saudiyya ta yi tir da hare-haren Isra'ila kan Falasɗinawa

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Saudiyya ta jagoranci ƙasashen Musulunci wurin yin tir da hare-haren Isra'ila kan Falasɗinawa a yayin wani taron ministocin harkokin ƙasashen waje na Ƙungiyar Haɗin-kan Musulunci (OIC).

    A lokacin da ya ke jagorantar taron don tattauna harin Isra'ila a Falasɗin musamman a Birnin Ƙudus, a cewar ministan harkokin ƙasashen wajen Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan.

    Ya zargi Isra'ila da tauye haƙƙin Falasɗinawa kuma ya yi kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankalin.

    Ministan ya ce ayyukan Isra'ila na yi wa yunkrin samar da zaman lafiya zagon ƙasa a yankin.

    Yarima Faisal ya ce kasashen duniya su yi gaggawar ɗaukar matakan dakatar da ayyukan soji sannan su ba da agaji ga wadanda abin ya shafa kuma su yi aiki wajen dawo da tattaunawa don samar da zaman lafiya.

    Ya kuma ce Saudiyya na goyon bayan duk wani yunƙurin tsagaita wuta.

  19. An naɗa ɗan shugaban ƙasa minista a Congo-Brazzaville

    An naɗa ɗan Shugaban Congo-Brazzaville Denis Sassou Nguesso a matsayin minista.

    Denis Christel Sassou Nguesso zai jagoranci sabuwar ma'aikatar haɗin kan kasashen duniya.

    Firai Minista Anatole Collinet Makosso ya sanar da sabuwar gwamnatin wadda ke da ministoci 36 ciki har da ministoci huɗu da mata takwas.

    An yi sabbin naɗe-naɗe ne bayan sake zaɓen shugaban a watan Maris.

    Shugaban ya hau mulki ne tun a shekarar 1979, in ban 1992 da ya faɗi zaɓe tsawon shekaru biyar.

  20. An kashe ƴan sanda biyu tare da ƙona ofishinsu a jihar Abia

    Gunmen

    Asalin hoton, Reuters

    Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan IPOB ne sun kashe ƴan sanda biyu tare da ƙona wani ofishin ƴan sandan a jihar Abia, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    An kai harin ne a ofishin ƴan sanda na Apumiri Ubakala da ke ƙaramar hukumar Umuahia ta Kudu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani ɗan sanda ya shaida mata cewa kafin kai harin, rundunar ƴan sanda a jihar ta samu bayanan sirri kan harin kuma an ba su shawarar rufe ofishin ko kuma su ƙara ƙarfin tsaro amma ba a yi ko daya daga ciki ba.

    Wannan ne hari na baya-bayan nan a yankin na Kudu maso gabashin Najeriya.

    Ƴan kwanaki da suka wuce an kai hari ofishin ƴan sanda na Bende a jihar ta Abia da ofishin ƴan sanda na Uzuakoli inda aka sa abin fashewa a ofishin.