Masu bin shafin BBC Hausa nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
An yi arangama tsakanin dakarun DR Kongo da mayaƙan M23
An yi arangama tsakanin sojojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 a arewacin lardin Kivu.
Kakakin M23 ya ce mayaƙan ƙungiyar sun kare kansu ne bayan da dakarun gwamnati suka kai masu hari a mazauninsu da ke Kirumba a yau Lahadi.
Rikicin ka iya yin barazana ga ƙoƙarin da ake na kawo ƙarshen lamarin ta hanyar diplomaisyya.
Anyi tsammanin cewa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Kongo da jami'an Rwanda a Angola zai sama wa fararen hular Kongo sauƙi.
Sai dai M23 da aka yi amanna cewa na samun goyon bayan Rwanda, na ci gaba da karɓe iko da wasu yankuna.
'Yan siyasar Najeriya na siyasantar da matsalar tsaro a ƙasar - Okonjo-Iweala
Asalin hoton, Getty Images
Babbar daraktar Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta zargi wasu 'yan siyasar Najeriya da siyasantar da matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Yayin da take jawabi a taron shekara-shekara da ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta shirya a birnin Legas a ranar Lahadi, tsohuwar ministar kuɗin ƙasar ta ce tsaro ne ginshiƙin samun kowane irin ci gaba a ko'ina.
“Ba za mu samu ci gaban tattalin arziki idan babu tsaro, haka kuma ba za mu samu tsaro ba dan ba mu da ci gaba'', in ji shugabar ƙungiyar WTO, kamar yadda rahotonni suka ambato ta.
Ta kuma yi zargin cewa akwai 'yan siyasa a Najeriya da ke tunanin cewa hanyar da kawai za su bi wajen hana abokan hamayyarsu jin daɗin mulki, shi ne ƙirƙirar musu matsalar tsaro, ba tare da la'akari da asarar rayuka da dukiyoyin mutanen da ba su ji ba su gani ba.
“Abin da muka sani shi ne 'yan siyasar ƙasarmu sun siyasantar da matsalar tsaro a ƙasarmu don cimma burinkansu na ƙashin kai, wannan kuma shi ne ya jefa ƙasarmu halin da take ciki a yanzu''.
Sanna kuma ta yi kira ga 'yan siyasar ƙasar su daina siyasantar da matsalar tsaro ta hanyar alaƙanta ta da abokan hamayyarsu an siyasa.
Tana mai cewa dole ne 'yan siyasar su dakatar da wannan ɗabi'a
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojanta guda a arewacin ƙasar
Rundunar sojin Isra'ila, IDF ta ce an kashe wani jami'an sojin ruwanta mai shekara 21, a lokacin wani gumurzu a arewacin ƙasar.
To sai dai rundunar ba ta yi karin haske kan yadda aka kashe sojan ba.
IDF ta bayyana sojan da suna David Moshe Ben Shitrit, daga yankin Geva Binyamin.
Ya ya ƙarfin Hezbollah yake?
Asalin hoton, EPA
Ƙungiyar Hezbollah mai bin mazhabar Shi'a na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin masu ƙarfin makamai waɗanda ba na gwamnati ba.
Ƙasar Iran ce ke bai wa ƙungiyar tallafin kudi da kayan aiki.
Shugaban ƙungiyar, Sheikh Hassan Nasrallah ya yi iƙirarin cewa tana da mayaƙa aƙalla 100,000, to sai dai wani ƙiyasi mai zaman kansa ya nuna cewa tana da mayaƙa tsakanin 20,000 zuwa 50,000.
Da yawa daga cikin mayaƙanta na da ƙwarewar yaƙi, kuma sun goyi bayan shugaban Assad na Siriya a lokacin yaƙin basasar ƙasar.
Ƙungiyar na da makaman roka da na linzami kimanin 120,000 zuwa 200,000, kamar yadda cibiyar tsare-tsare ta duniya ta yi ƙiyasi.
Mafi yawan makamanta ƙanana ne. To amma ana zargin tana da makaman harbo jiragen sama da na kakkaɓo makami mai linzami, sannan ana zargin tana da makamai masu linzami da za su iya kai wa cikin Isra'ila.
Tarin makaman Hezbollah ya zarta ƙarfin makaman da ƙungiyar Hamas ke da su.
Hezbollah ta yi barazanar sake kai hare-hare
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila sun ce sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa da Hezbollah ta harba
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ƙungiyar Hezbollah na cewa za ta yi nazarin hare-haren da ta kai yau.
Shugaban ƙungiyar Hassan Nasrallah, ya ce ƙungiyar za ta sake kai hare-hare a wasu lokutan idan buƙatar hakan ta so.
Ya yi iƙirarin cewa ƙungiyar na dab da ƙaddamar da babban harin da ta shirya, bayan ya yi watsi da sanarwar sojojin Isra'ila na dakatar da babban harin da ƙungiyar ke yunƙurin kaiwa.
A baya-bayan ne dai Hezbollah da Isra'ila sun yi ta musayar hare-haren makamai masu linzami da rokoki
Tinubu ya yi alhinin rasuwar sarkin Ningi
Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.
Cikin wani saƙo da kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaba Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga al'ummar masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi kan rasuwar sarki.
Marigayin mai shekara 88 ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin sarkin mai daraja ta ɗaya a matsayin jajirtaccen shugaba da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimta wa al'ummarsa.
Tuni dai aka yi jana'izar marigayin a fadarsa.
MDD ta damu kan sabuwar dokar gyaran tarbiyya da Taliban ta ɓullo da ita
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya ce ya damu da dokar gyaran tarbiyya da ta hukumomin ƙasar suka ɓullo da ita, wadda ta saɓa wa 'yancin ɗan'adam tare da ƙara takaita wa mata damarmaki a ƙasar.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Taliban ta tsara tare da zartar da dokokin bisa fahimtarsu ta dokokin Musulunci.
Shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan, Roza Otunbayeva ya ce dokar ta bai wa jami'ai daga hukumar yaƙi da ta taɓarɓarewar tarbiyya ta ƙasar, damar kama tare da ɗaure mutanen da suka saɓa ta.
Dokar ta yi tanadin cewa dole ne mata su rufe fuskokinsu da sauran sassan jikinsu, idan za su fita daga gida, sannan su tabbatar ba su ɗaga muryoyinsu ba ta yadda wasu za su ji su.
'Yansanda biyu da farar hula ɗaya sun mutu a rikicin 'yan Shi'a da 'yansanda a Abuja
An kashe 'yansanda biyu da jikkata wasu biyu, sannan kuma wani ɗan kasuwa ya rasu bayan da aka harbe shi a wani rikici da ya tashi tsakanin da 'yan Shi'a na ƙungiyar Harka Islamiyya a Najeriya, (IMN), mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky, a kasuwar Wuse da ke Abuja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutumin da aka harbe mai suna Amiru, an harbe shi a ƙirji ne lokacin da 'yansanda suke rarakar masu zanga-zangar na Shi'a.
Jaridar ta ce wani da y ga abin da ya faru wanda ya nemi da kada a fadi sunansa ya ce an garzaya da mutumin asibitin Wuce Zone 3 inda a can ya ga 'yansanda da dama da aka jikkata a rikicin, a don haka aka nufi asibitin Maitama da shi inda a kan hanya ya cika.
Mabiya kungiyar ta IMN dai na zanga-zangar da suke yi wa lakabi da Arbaeen, wato cika kwana arba'in bayan taron Ashura.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yansandan babban birnin SP Josephine Adeh, ta fitar, ta tabbatar da kisan jami'ansu guda biyu da jikkata wasu biyu tare kuma da kona motocin 'yansanda na sintiri uku a rikicin wanda ta ce ba gaira ba dalili mabiya kungiyar suka kai wa jami'ansu hari.
A sanarwar da 'yansandan suka fitar sun ce, ''mabiya haramtacciyar kungiyar sun kai wa wajen binciken ababan hawa na 'yansanda hari haka kawai, dauke da adda da bama-bamai hadin gida wadanda aka yi da kananzir a cikin kwalba, da kuma wukake.
Rundunar ta ce an kama mutane da dama, inda kwamishinan 'yansandan birnin na Abuja Benneth C. Igweh, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu.
Aƙalla mutum 22 sun rasu bayan da motarsu ta afka rami a Pakistan
Asalin hoton, Mohammad Yousaf/AP
Mutum aƙalla 22 ne suka mutu bayan da motar safa da suke ciki ta afka wani rami a arewacin Pakistan
Jami'ai sun ce haɗarin ya faru ne a kusa da garin Azad Pattan, da ke kan iyakar lardin Punjab da Kashmir ta ƙarƙashin mulkin Pakistan.
A wani haɗarin na daban kuma aƙalla masu ziyarar ibada 12 ne suka mutu a kan hanyarsu ta komawa gida, a babbar hanyar Makran, da ke kudu maso yammacin ƙasar ta Pakistan.
Alamu sun nuna cewa direban motar da mutanen ke ciki ya kasa sarrafa motar ne, bayan da birkinta ya shanye.
Dukkanin haɗurran biyu na yau Lahadi sun faru ne bayan da a ƴan kwanakin da suka gabata wasu masu ziyarar ibada 'yan Pakistan ɗin su 28 suka mutu a wani haɗarin motar safa a Iran.
Mai manhajar Telegram zai gurfana gaban kotun Faransa yau
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Pavel Durov ya ƙirƙiro Telegram a 2013
Ana sa ran ɗan ƙasar Rashan nan, mai shafin sada zumunta da muhawara na Telegram, Pavel Durov, zai gurfana a gaban kotu a yau Lahadi.
Kafafen yaɗa labaran Faransa sun ruwaito cewa a jiya Asabar ne aka tsare hamshaƙin attajirin bayan da jirginsa ya sauƙa a filin jirgin sama na Le Bourget, da ke arewacin Paris.
Ana ganin an kama Mista Durov ne, mai shekara 39, saboda ya ƙi bayar da haɗin kai ga masu bincike kan yadda wasu masu aikata miyagun laifuka, ke amfani da manhajar ta Telegram.
Jami'an Rasha da ke ƙoƙarin samun bayanai kan dalilin kama shi, sun ce Faransa ta ƙi ba su haɗin kai.
Mista Durov, wanda aka haife shi a Rasha, kuma yake da takardar ɗan ƙasa ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Faransa, yana zaune a Dubai.
Mutum kusan miliyan 900 ne ke amfani da manhajar ta Telegram a faɗin duniya.
Kuma tana da farin jini sosai a Rasha da Ukraine da sauran ƙasashe na tsuhuwar Tarayyar Soviet.
An haramta amfani da manhajar a Rasha a 2018, saboda Mista Durov ya ƙi bayar da bayanan masu amfani da manhajar, amma kuma a 2021 aka ɗage wannan haramcin.
Telegram na ɗaya daga cikin shafukan sada zumunta da muhawara da suka fi fice a duniya, bayan Facebook da YouTube da WhatsApp da Instagram da TikTok da Wechat.
Maimartaba Sarkin Ningi ya rasu yana da shekara 88
Asalin hoton, NINGI EMIRATE/FACEBOOK
Maimartaba Sarkin Ningi da ke jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu, yana da shekara 88.
Sakataren masarautar, Alhaji Usman Sule, Magayakin Ningi, shi ne ya bayyana labarin rasuwar a wata sanarwa, inda ya ce, Allah Ya yi wa Sarkin rasuwa ne yau Lahadi da Asuba a Kano.
Sanarwar ta kara da cewa za a yi jana'izar Sarkin mai daraja ta daya, yau da karfe hudu na yamma a fadarsa da ke Ningi.
Bayanai sun nuna cewa ya rasu ne, a wani asibiti a Kanon, kwana biyu bayan ya dawo Najeriya daga Saudiyya inda ya je domin duba lafiyarsa.
An haifi marigayi Alhaji Yunusa Danyaya a shekarar 1936, a garin Ningi kuma ya zama sarki a shekarar 1978.
Shugabannin Brazil da Colombia sun nemi a fitar da bayanan zaɓen Venezuela
Asalin hoton, Reuters
Shugabannin Brazil da Colombia sun sake kira ga hukumomin Venezuela su wallafa cikakken bayanin sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi mai cike da ce-ce-ku-ce.
A sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugaba Luiz Inacio Lula da Silva da Gustavo Petro sun ce ita ce hanya daya tilo da za ta kawo zaman lafiya da karshen takaddamar da ake yi kan sahihancin zaben.
Su dai hukumomin Venezuela sun dage cewa Shugaba Nicolas Maduro ne ya yi nasara a zaben, amma sun ki wallafa sakamakon zaben domin ganin ainahin kuri'un da kowane dan takara ya samu tsakaninsa da abokin hamayyarsa Edmundo Gonzalez.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hare-hare kan mayaƙan Hezbollah a Lebanon
Asalin hoton, EPA
Sojojin Isra'ila sun ce sun kaddamar da hare-hare kan mayakan Hezbollah a kudancin Lebanon.
Kakakin rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari shi ne ya sanar da haka ga manema labarai.
Hagari, ya ce sojojin sun kai hari Lebanon bayan gano shirin kungiyar Hezbollah na kai mummunan hari kan farar hula a Isra'ila.
Ana ta bangaren kungiyar ta Hezbollah, ta ce ta kai harin makamin roka 3 da jirage marassa matuka zuwa Isra'ilar.
Ta ce harin kashin farko ne na hare-haren da za ta kai kan kisan kwamandanta da Isra'ilar ta yi a watan jiya.
An yi ta jin karar jiniyar ankarar da jama'a kan kai hari a arewacin Isra'ila, inda tuni aka ayyana dokar ta-baci yayin da hukumomin tsaron kasar suka shiga taron gaggawa.
Ƴansandan Jamus sun kama mutumin da ake zargi da kisa da wuƙa
Asalin hoton, OTHERS
'Yan sandan Jamus sun cafke wani mutum da ake zargi da daba wa mutane wuka a daren juma'a a yammacin birnin Zolinhen.
'Yan sandan sun ce mutumin mai shekara 26 da kan shi ya je ya mika kanshi a wajensu, tare da ikirarin shi ne ya aikata harin.
Mutane uku ne suka mutu wasu 8 suka jikkata a lokacin da aka kai harin ana tsaka da bikin cikar birnin Solingen shekara 650 da kafuwa.
Kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS ta dauki alhakin kai harin, koda yake ba a tabbatar da hakan ba.
To amma kuma mutumin da aka kama da laifin kai harin dan asalin Syria, wanda kum ake zarin yan da alaka da kungiyr ta IS.
Shugaban sojin Sudan ya yi watsi da tattaunawar zaman lafiya
Asalin hoton, AFP
Shugaban sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya yi watsi da tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta a Switzerland, ta neman kawo karshen yakin da suke yi da rundunar RSF.
Da yake magana a Bahar Sudan inda gwamnatinsa ke gudanar da mulki bayan mamaye babban birnin kasar Khartoum da RSF ta yi, Al-Burhan, ya sha alwashin ci gaba da yakin ko da za a dauki shekara 100 ana yi.
Wannan sanarwar dai ta dakushe duk wani fata da ake da shi na tsagaita wuta tsakanin bangaren gwamnati da na Muhammad Hamdan Dagalo wato Hemeti da suka kwashe sama da shekara daya suna yaki.
Buɗewa
Assalamu alaikum jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke
kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran
sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Lahadi.
Ni ne Muhammad Annur Muhammad, zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba in Allah Ya yarda.
Mu fara da wannan karin maganar - Komai ya samu shamuwa watan bakwai ne ya jawo mata