window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Isiyaku Muhammed, Ahmad Bawage, Usmna Minjibir, da Umar Mikail

  1. Mu zama lafiya

    Ƙarshen labaran kenan a wannan shafi na ranar Litinin.

    Mu hadu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Kamfanin haƙar ma'adinai na Canada ya yi barazanar dakatar da aiki a Mali

    Wani kamfanin haƙar ma'adinai na ƙasar Canada ya yi gargadin cewa wataƙila ya dakatar da ayyukansa a ɗaya daga cikin manyan wuraren haƙar ma'adinan zinare a yammacin ƙasar Mali.

    Kamfanin Barrick Gold ya ce hukumomin sojin ƙasar sun tsawaita dokar hana fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje tare da hana jigilar kayayyaki daga cibiyar haƙar ma'adinai ta Loulo Gonkoto

    Wakilin BBC ya ce shugabannin sojin Mali sun buƙaci kaso mai tsoka a fanin haƙar ma'adinai ta ƙasar da ke samun tagomashi

    Shugaban kamfanin Mark Bristow ya kira matakin gwamnatin sojin ƙasar a matsayin abin da bai dace ba.

    Haka kuma shugabannin sojin ƙasar sun tsare shugabannin kamfanonin haƙo ma'adinai a watannin baya-bayan nan kan taƙaddama kan haraji.

  3. Bam ya kashe mutum biyu a wata Islamiyya a Abuja

    Tsangayar Sani Usman Islamiyya

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce wani abin fashewa ya kashe mutum biyu a makarantar Islamiyya da ke Abuja babban binrin ƙasar.

    Wata sanarwa da rundundar ta wallafa ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Litinin a ƙauyen Kuchibuyi da ke ƙaramar hukumar Bwari.

    "Bayanan farko-farko sun nuna wasu mutum uku ne suka kai wa shugaban makarantar Tsangayar Sani Uthman Islamiyya Mallam Adamu Ashimu ziyara, kuma su ake zargi da kai bam ɗin," in ji sanarwar.

    "Biyu daga cikin mutanen sun mutu a fashewar a farfajiyar makarantar, yayin da na ukun da kuma wata mata mai sayar da kayayyaki suka ji munanan raunika kuma suke samun kulawa a asibiti."

    Sanarwar ta ƙara da cewa 'yansanda na tsare da Mallam Adamu, sannan kuma za ta bayyana abin da bincikenta ya gano.

  4. Shugaban Ghana Akufo-Addo ya yi wa fursunoni afuwa

    Nana Akupo-Addo

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban kasar Ghana mai barin gado, Nana Akufo Addo, ya yi wa wasu mutane afuwa yayin da ya rage kwana ɗaya ya mika mulki ga magajinsa John Dramani Mahama.

    A cikin wadanda aka yi wa afuwar akwai William Ato Essein, tsohon shugaban wani banki da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 15 kan rawar da ya taka kan rugujewar bankin kasar.

    Sai dai jerin sunayen wadanda aka yi wa afuwa ya janyo cecekuce inda masu sukar gwamnati suka nuna damuwa kan waɗanda aka samu da aikata miyagun laifuka da suka haɗa da kisa, da kuma safarar mutane.

  5. Ƴanmajalisar dokokin Amurka sun hallara don tabbatar da nasarar Trump

    Capitol

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴnmajalisar dokokin Amurka sun hallara a birnin Washington domin tabbatar da nasarar Donald Trump a hukumance a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a watan Nuwaban da ya gabata .

    Suna ganawa duk da zubar dussar ƙanƙara mai tsanani a babban birnin, da matsananciyyar guguwar hunturu ta haddasa

    Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka kuma jagorar taron , Kamla Harris ta yi jawabi mai ratsa zukata a wurin.

    An dai tsaurara matakan tsaro.

    Shugaba Biden ya yi alƙawarin cewa ba za a sake samun maimaicin tarzomar da ta faru shekaru huɗu da suka gabata ba, a lokacin da dandazon magoya bayan Mista Trump suka kutsa cikin majalisar dokokin ƙasar

  6. Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya janyo ambaliya a Makka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Matsanancin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan ƙasar Saudiyya.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye hanyoyi a cikin garin Makka.

    Haka kuma an ga yadda wasu maza suka riƙe da hannu domin ceto yaran da suka maƙale sanadin ambliyar ruwan a unguwar Al-Awali.

    Sai da aka soke jigilar wasu jiragen sama a birnin Jeddah, inda aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya janyo hukumomin Saudiyya suka rufe makarantu a daukacin ƙasar.

  7. EFCC ta kori ma'aikatanta 27 saboda 'zambatar' mutane

    Ola Olukoyede

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta kori ma'aikatanta 27 a shekarar 2024 saboda zargin aikata zamba da sauran laifuka.

    Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya amince da matakin.

    "Duk wani zargi da aka yi wa wani ma'aikacin hukumar, sai an bincika shi, ciki har da na dala 400,000 da ake yi wa wani ma'aikaci da ba a gano shi ba zuwa yanzu," a cewar sanarwar.

    Ya ƙara da cewa EFCC "na sane da ayyukan sojan gona da ɓata sunan da wasu ke yi da ta hanyar amfani da sunan shugaba [Olukoyede] domin zambatar manyan mutanen da ake zargi", wanda shi ma ake kan bincikawa.

  8. 'Yansandan Abuja sun kama mutum 50 da zargin sace murafen kwatami

    Murafan kwatami

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen binrin Abuja ta ce ta kama mutum 50 da take zargi da ɓallewa tare da sace murafe na kwatami a kan titunan birnin.

    Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukan zumunta ta ce tsararren samame da ta kai ne ya ba ta nasarar kama mutanen, inda kuma dakarunta suka ƙwato murafe 25.

    Birnin na Abuja ya daɗe yana fama da waɗannan sace-sace, inda ake yawan cire murafen da ke tsakiya ko gefen titi domin sayarwa.

    "Bincike ya tabbatar cewa masu satar na aiki ne a matsayin wani gungu da ke sayar da murafen ga dillalan ƙarafa," in ji sanarwar wadda ta lissafo sunayen mutum 50 ɗin.

    Daga cikin abubuwan da ta ce ta ƙwace a hannun mutanen har da turakun lantarki masu amfani da hasken rana na gefen titi, da ababen hawa uku, da rodin gina gadodji, da sauran abubuwan da suke amfani da su wajen lalata kayan gwamnati.

  9. MDD ta fara nema wa Sudan tallafin dala biliyan huɗu

    Yara a Sudan

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta kaddamar da shirin neman agajin dala biliyan hudu ga kasar Sudan.

    Tana son ta taimaka wa mutane miliyan 20 da ke matukar bukatar agaji, bayan shafe watani fiye da 18 ana yaƙin basasa.

    Jami'ar kula da ayyukan agaji ta MDD, Clementine Nkweta Salami, ta ce fiye da rabi daga cikinsu yara ne.

    Ta yi kira a kawo karshen rikicin tare da yin sassauci ga dokokin takaita zirga-zirga domin a samu damar kai kayan agaji ga wadanda ke matukar bukata.

    An ayyana yunwa a yankuna biyar, inda mutane fiye da miliyan takawas ke gab da fadawa cikin yunwa.

  10. Iswap ta kashe sojojin Najeriya shida a jihar Borno, in ji rahoton AFP

    Mayaƙan Iswap

    Asalin hoton, AFP

    Mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State sun kashe sojojin Najeriya shida yayin wani hari da suka kai kan sansaninsu da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, a cewar rahoton kamfanin labarai na AFP.

    AFP ya ambato jami'an sojin Najeriya biyu na cewa maharan na ƙungiyar Islamic State West Africa Province (Iswap) sun far wa sansanin da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ranar Lahadi da tsakar dare.

    Rahotonni sun ce sun cinna wa sansanin wuta tare da ababen hawan da ke cikinsa.

    "An kashe mana sojoji shida a harin na Iswap da suka kai sansanin bayan zazzafar musayar wuta," kamar yadda ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa wa AFP.

    Ɗaya jami'in ya ce jirgin sojin sama da aka aika daga binrin Maiduguri, mai nisan kilomita 100, shi ne ya kori maharan.

    "Hare-hare ta sama ya kashe 'yanbindigar da yawa, ya lalata motoci da makamansu," in ji majiyar ba tare da bayar da yawan adadi ba.

  11. An ƙaddamar da shirin ciyar da masu ciki da yara kyauta a Indonesia

    Indonesia

    Asalin hoton, EPA

    Ƙasar Indonesia ta ƙaddamar da wani shiri na musamman domin ciyar da masu ciki da yara ƙanana kyauta a ƙasar.

    Ƙasar ta kasafta kashe dala miliyan 4.3 domin gudanar da ciyarwar ne da zimmar magance matsalolin rashin abinci mai gina jiki.

    Shirin na cikin manyan alƙawuran da Shugaban Ƙasa Prabowo Subianto ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓensa.

    Shirin zai kuma ƙunshi ciyar da ɗalibai ƴan makaranta, sannan an ɗauki wuraren abinci kusan 200 domin aikin dafa abincin.

    Sai dai masana tattalin arziki na sukar lamarin, inda suka ce hakan zai sa ƙasar ta riƙa kashe maƙudan kuɗaɗe.

  12. Kotu ta bayar da sammacin kama tsohuwar shugabar Bangladesh

    Bangladesh

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kotu a ƙasar Bangladesh ta bayar da sammacin kama tsohuwar Shugabar Ƙasar, Sheikh Hasina, wadda ta samu mafaka a ƙasar India.

    Masu gabatar da ƙara sun bayan ita, an kuma bayar da sammacin kama wasu mutanen guda 10, ciki har da tsohon mai ba shugaban ƙasar shawara kan tsaro.

    Ms Hasina ta tsere ne zuwa India bayan zanga-zanga ta ɓarke a ƙasar a watan Agustan.

    Aƙalla mutum 500 ne ake zargin cewa jami'an tsaron ƙasar sun sace a shekara 15 da ta yi tana mulkin ƙasar.

    A watan Disambann bara ne ƙasar ta buƙaci India ta mayar da tshohuwar firaiministan domin ta fuskanci shari'ar zargin da ake mata.

  13. Za a gurfanar da tsohon shugaban Faransa kan zargin karɓar na-goro daga Gaddafi

    Sarkozy da Gaddafi

    Asalin hoton, EPA

    Za a gabatar da tsohon Shugaban Ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy a wata kotu a Paris bisa zarginsa da karɓar cin hanci daga tsohon Shugaban Ƙasar Libya, marigayi Muammar Gaddafi.

    Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa mutanen biyu sun shiga yarjejeniyar ce a lokacin da Sarkozy yake ministan harkokin cikin gida, inda ya karɓi na-goron ya yi amfani da su a yaƙin zaɓensa na zama shugaban ƙasa a 2007.

    Shi kuma sai ya yi alƙawarin taimakon Gaddafi domin a wanke shi daga irin kallon da masa da kuma wariyar da ake masa a ƙasashen duniya.

    Sai dai Sarkozy ya musanta zargin, inda ya ce wasu ƴan Libya ne suka ƙirkiri zancen domin a ɓata masa suna saboda gudunmuwar da ya bayar wajen kifar da gwamnatin Gaddafi a 2011.

  14. Dakarun Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗanbindiga, Sani Rusu a Zamfara

    Tsaro

    Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria

    Dakarun haɗin gwiwa na Operation Fansar Yamma da ke yaƙi da ƴan fashin daji a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa sun hallaka wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Rusu.

    Jami'in hulɗa da jama'a na dakarun, Laftana Kanal Abubakar Abdullahi ne ya tabbatar da lamarin.

    Ya ce rundunar ta ce ta samu nasarar murƙushe shi ne yayin wani samame da suka kai ta ƙasa da sama zuwa matattarar ƴan bindiga da ke ƙauyen Bamamu a ƙaramar hukumar Tsafe cikin jihar Zamfara, inda suka kashe ƙarin wasu mutanen da kuma ƙwato tarin makamai.

  15. Trump ne zai iya kawo ƙarshen yaƙin da muke yi da Rasha - Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya jaddada cewa Donald Trump ne kaɗai zai iya bayar da tabbacin samar da tsaron da zai iya kaiwa ga kawo ƙarshen yakin da ƙasarsa ke yi da Rasha.

    A wata hira da aka yi da shi, Mista Zelensky ya yaba da tasirin shugaban Amurkan mai jiran gado, ya kuma yi nuni da cewa yana da damar da zai iya dakatar da mamayar da Rasha ke ci gaba da yi.

    Wannan na zuwa ne bayan Mr Trump ya yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, ba tare da bayar da cikakken bayanin matakan da zai ɗauka ba.

  16. Kalli yadda dusar ƙanƙara ta lulluɓe wasu biranen Amurka

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Dusar ƙanƙara ta lulluɓe wasu sassa na ƙasar Amurka, inda miliyoyin mutane suke fuskantar barazanar zaman kulle.

    Mazauna yankin Syracuse da New York ne suka fi fuskantar matsalar, sannan yankunan Lowville da yankunan arewacin jihar Nebraska ma suna haka.

    Hukumomi a ƙasar sun sanar da cewa tsanantar ƙanƙarar zai jawo tsaiko ga harkokin sufuri a ƙasar.

  17. Kalli yadda wani ƙarfen da ba a san mai shi ba ya faɗo daga sararin samaniya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Ƙwararru daga hukumar kula da sararin samaniya ta Kenya na ƙoƙarin gano asalin wani ƙarfe da ya faɗa kan wani ƙauye a ƙasar.

    Babu wanda ya jikkata bayan faɗowar tarkacen a yankin Shrubland da ke ƙauyen Makuku mai nisan kilomita 120 daga Nairbo, babban birnin ƙasar ta Kenya.

  18. Majalisar Venezuela ta buƙaci a kama jagoran ƴan adawar ƙasar

    Venezuela

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban majalisar dokokin ƙasar Venezuela ya sake nanata kira da a kamo jagorar ƴan adawar ƙasar da ke gudun hijira.

    Jim kaɗan bayan an rantsar da shi ne Jorge Rodriguez ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar da ta ba da umarnin tsare Edmundo Gonzalez, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa, idan har ya taka ƙafarsa a ƙasar Venezuela.

    Tun da farko dai Mista Gonzalez ya yi jawabi ga taron magoya bayansa a birnin Montevideo, inda ya sha alwashin ci gaba da fafutukar komawa Venezuela.

    Ya ce Gwamnati na iya rufe sararin samaniya, ta rufe manyan tituna, ta rufe hanyoyin shiga Caracas, amma hakan ba zai iya "dakushe nasarar da muka riga muka samu ba."

  19. Ban sauya jam'iyya ba - El-Rufa'i

    El-Rufai

    Asalin hoton, Kaduna state government

    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce batun sauya jam'iyyar da ake yaɗawa ya yi ba gaskiya ba ne.

    El-Rufai ya yi wannan jawabin ne biyo bayan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya fice daga Jam'iyyar APC, ya koma Jam'iyyar PDP

    A wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, El-Rufai ya ce, "ku yi watsi da duk ƙarairayi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa game da jam'iyyar siyasar da nake ciki. Tuni na umarci lauyoyina su yi abin da ya dace dangane da wasu yaɗa labaran na ƙarya."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. An harbe ƴan Isra'ila uku a Gaɓar Yamma

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    An harbe wasu ƴan Isra'ila guda uku a wani hari da aka kai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Mata biyu waɗanda suka kai shekara 60 suna cikin waɗanda aka harbe.

    Rundunar tsaron Isra'ila ta ce wasu ƴanbindiga ne suka buɗe wuta kan motocin fararen hula guda uku a lokacin da suke wucewa ta wani ƙauyen yankin mutanen Falasɗinu mai suna Al-Funduq wanda ke kusa da garin Yahudawa na Kedumim.

    Tuni jami'an tsaron Isra'ila suka kafa shingayen bincike a yankin da zimmar kama waɗanda suka kai harin.