window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Isiyaku Muhammed, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Alhamis.

    Za mu zo wasu rahotonnin gobe da safe daga nan BBC Hausa.

  2. Mayaƙa masu iƙirarin jihadi sun kashe sojojin Benin 28

    Sojojin Benin

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin kasar Benin ta ce an kashe dakarunta 28 a wani hari da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai a arewacin kasar.

    Sojojin sun ce sun kashe masu tayar da kayar baya 40 a hare-hare ta sama da kuma ta ƙasa.

    Ana samun ƙaruwa a hare-haren da ake kai wa arewacin Benin da ke kusa da kan iyakar kasar da Burkina Fasso, da kuma Nijar.

    Ƙungyoyi da ke biyaya ga kungiyar IS da Al-Qaeda ne ke yawan kai hare-hare a yanzin.

    Miliyoyin mutane a sasan yankin Sahel sun rasa muhallansu sakamakon tashin hankalin.

  3. Amurkawa sun fara bankwana da gawar Jimmy Carter

    Jimmy Carter

    Asalin hoton, Reuters

    Amurkawa sun fara yi wa tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter bankwana, inda aka gudanar da taron addu'o'i a babbar cocin da ke Washington.

    Taron ya samu halartar jami'an gwamnati da yan'siyasa da dama.

    An rika kiɗan nuna alhini a lokacin da sojoji suka fito da akwatin gawarsa daga majalisar dokokin kasar domin kai shi cocin Washington SFX.

    Dukkanin tsofaffin shugabanin kasar da ke raye sun halarci taron addu'o'in.

    Shugaba Joe Biden, wanda ɗan jam'iyyasa ta Democrat ne kuma amininsa, ya gabatar da jawabin jinjina wa mamacin.

    Ya bayyana marigayin a matsayin "mai dattaku da kuma hali na gari wanda bai taba barin rigingimun siyasa sun karkatar da shi daga manufar gyara duniya tare da yi mata hidima ba".

    Za a wuce da gawar Jimmy Cater zuwa mahaifarsa Georgia, inda za a binne shi kusa da ƙabarin matarsa Rosalyn.

  4. Shugabannin adawa a Venezeula na jagorantar zanga-zanga kan shirin rantsar da Maduro

    Venezuela

    Asalin hoton, EPA

    Jagorar 'yanhammaya a kasar Venezeula, Maria Corina Machado, ta fito daga maɓoyarta domin shiga zanga-zangar nuna rashn amincewa da shirin rantsar da Shugaba Nicolas Maduro a gobe Juma'a.

    Magoya bayan ɗantakarar adawa, Edumundo Gonzalez, wanda ya yi ikikarim lashe zaben watan Yulin da ya gabata, sun yi zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar.

    Wakiliyar BBC ta ce tun bayan zaɓen shugaban kasar da aka yi mai cike da taƙaddama ake ta kama masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da kuma jagororin 'yan'adawa.

    Rahotonni sun ce jami'an jam'iyya mai mulki sun mamaye muhimman wuraren da za a yi zanga-zangar a birnin Caracas, kuma 'yansanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa tarukan jama'a.

  5. Gwamnatin Najeriya ta buɗe kwalejin horas da matasa kan ƙirƙirarriyar basira a kyauta

    Ƙirƙirarriyar basira

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wani shiri na horar da matasa game da sanin makamar ƙirƙirarriyar basira wato Artificial Intelligence (AI) ta intanet.

    Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha Uche Geoffrey Nnaji ya ce shirin wanda aka ƙaddamar ranar Talata, an yi masa suna AI Academy - wato kwalejin ƙirƙirarriyar basira.

    Najeriya ta ƙaddamar da shirin bisa haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ta Commonwealth.

    "AI Academy za ta horar da ɗalibai, da matasa, da ma'aikatan gwamnati wajen shawo kan matsaloli da kuma ƙirƙirar damarmaki ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira," in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa za a rufe yin rajista a shafin kwalejin ranar 30 ga watan Janairun nan.

    Ministan ya ce masu sha'awa na iya a ziyartar wannan adireshin an domin yin rajista.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Hankula sun kwanta a Chadi bayan hari kan fadar shugaban ƙasa

    Mahamat Idriss Deby

    Asalin hoton, Reuters

    Al'amura sun daidaita a Ndnjamena babban birnin Chadi bayan wani hari da jami'an tsaro suka dakile a harabar fadar shugaban kasa a jiya Laraba da dare.

    Kakakin gwamnatin kasar ya ce maharan na dauke da miyagun makamai kuma an kashe 18 daga cikinsu, yayin da aka kama shida.

    Haka kuma, an kashe jami'in tsaro daya. Yanzu an tsaurara matakan tsaro a kewayen fadar shugaban kasar.

    Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce lauyan gwamnati zai yi ƙarin haske kan lamarin, sai dai ya ce da akwai yiwuwar lamarin na taaadanci ne.

  7. China ta yi alƙawarin taimaka wa Najeriya a fannin tsaro da tattalin arziki

    Najeriya da China

    Asalin hoton, Ministry of Foriegn Affairs

    Najeriya da China sun amince su ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin makamashi, da tsaro, da harkokin kuɗi, kamar yadda ministocin harkokin wajen ƙasashen suka bayyana yau Alhamis.

    Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi na ziyara a Najeriya ne a wani ɓangare na ziyarar aiki a ƙasashen Afirka huɗu domin faɗaɗa tasirin ƙasarsa a nahiyar.

    Mista Wang ya ce China za ta duba buƙatar da Najeriya ta gabatar mata ta faɗaɗa yarjejniyar amfani da takardun kuɗin ƙasar na Yan.

    A ɓangaren tsaro kuma, Wang ya ce China za ta dinga goya wa Afirka baya kodayaushe a zauren tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

    "Za mu yi aiki tare da Afirka wajen inganta tsaro da kuma cim ma zaman lafiya ta hanyar ayyukan more rayuwa," in ji shi.

    China

    Asalin hoton, Ministry of Foriegn Affairs

  8. Rasha ta ce tana bibiyar barazanar Trump ta ƙwace Greenland

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai magana da yawun ƙasar Rasha, Dmitry Peskov ya ce Rasha na bibiyar batun da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka ya yi na yiwuwar yin amfani da ƙarfin soji wajen ƙwace tsibirin Greenland daga hannun Denmark.

    Peskov ya ce yankin ya kasance ɗaya daga cikin muradan Rasha na ƙasa da na son zaman lafiya".

    Rasha ce dai ƙasa ta uku ta Turai bayan Faransa da Jamus da ta fito ta nuna rashin amincewa da barazanar da zaɓaɓɓen shugaban Amurka ya yi ranar Talata.

    Babban jami'in kula da harkokin waje na tarayyar Turai Kaja ya bayyana cewa "dole ne mu martaba ƙima da martabar Greenland", sannan shugaban Jamus, Olaf Scholz ya bayyana cewa "bai kamata a ƙwace iyakokin da ƙarfin tuwo ba."

  9. Shugaban mulkin sojin Nijar ya yi garambawul a gwamnatinsa

    Janar Tiani

    Asalin hoton, ORTN

    Shugaban mulkin sojin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi garambawul ga majalisar gwamnoni ƙasar.

    Janar Tiani ya cire gwamnonin jihohin Damagaram da Dosso tare da maye gurbinsu da wasu.

    A yayin garambawaul ɗin, shugaban mulkin sojin ƙasar ya sauya ƙaramin gwamnan gundumar Tassara tare da naɗa sabon jakada a ƙasar Tchadi da kuma sabon babban Daraktan kamfanin sadarwa na ƙasa .

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan ƙasa ke ta kiraye-kirayen ganin a dakatar da naɗe-naɗen sojoji domin ba su damar komawa a fagen daga inda aka fi bukatarsu.

    Sai dai wasu na ganin naɗa sojojin zai taimaka ga kula da harkar tsaro a wasu yankunan kamar na Dosso da ke fuskantar barazanar 'yan bindigar Lakurawa a makonni bayan nan.

  10. Cutar zubewar gashin kai cikin hanzari ta ɓulla a ƙauyukan Indiya

    Hukumomin lafiya a Indiya sun ƙaddamar da bincike bayan mazauna ƙauyuka a jihar Maharashtra sun shiga wani yanayi na zubewar gashin kansu haka kawai.

    Waɗanda lamarin ya shafa sun ce sun ji ƙaiƙayi mai tsanani a jikinsu cikin kwana uku zuwa huɗu yayin da gashin nasu ke zubewa.

    Cutar ta firgita mazauna yankunan, inda wasu ke yi mata laƙabi da "cutar sanƙo".

    Likitoci na zargin gurɓacewar ruwa za ta iya zama dalili kuma tuni suka fara ɗaukar samfur daga yankin domin gudanar da gwaji, ciki har da na gashi da fatar mutanen.

  11. NAPTIP ta kuɓutar da mutum 285 da aka yi safararsu zuwa Kano a 2024

    Waɗanda aka kuɓutar

    Asalin hoton, NAPTIP

    Hukumar yaƙi da safarar mutanen da Najeriya, NAPTIP, reshen jihar Kano ta ce ta kuɓutar da wasu mutum 285 da aka yi yunkurin safararsu tare da kama masu safarar 22 a shekarar 2024.

    Kwamandan hukumar a reshen jihar, Abdullahi Babale ne ya bayyana haka cikin wata hira da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN a Kano.

    Babale ya ce daga cikin mutum 285 da aka kuɓutar, 78 maza ne, yayin da 97 daga ciki mata ne, da ƙananan yara 110.

    Yayin da babban jami'in hukumar a jihar Kano ya ce sun kama mutum 22 bisa zargin hannu a laifin ciki har da maza takwas da mata 14.

    Abdullahi Babale ya ce laifukan da ake zarginsu sun haɗa da cin zarafin ƙananan yara da tilasta musu aikin ƙarfi, da cin zarafi ta hanyar lalata da sauran laifuka ƙarƙashin dokokin cin zarafin ɗan'adam.

  12. Ƴan sintiri sun ceto mutum 63 a hannun masu garkuwa a Sokoto

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, fb/Ahmed Aliyu

    Tawagar ƴan sintiri a jihar Sokoto ta ce ta kuɓutar da mutum 63 daga hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, a jihar mai fama da matsalar ayyukan ƴan bindiga.

    Wata sanarwa da ta samu sa hannun Garba Mohammed, mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar ta ce tawagar ta ƙunshi jami'an ƴansanda da jami'an tsaro ƙarƙashin gwamnatin jihar Sokoto.

    Bayanin ya bayyana cewa an kuɓutar da mutanen ne a tsawon kwana huɗu, daga ranar Lahadin da ta gabata.

    Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

    Haka nan a baya-bayan nan an samu ɓullar wata ƙungiyar ƴan bindiga da ake kira Lakurawa.

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta tsananta ayyukan yaƙar ƴan bindiga tun bayan ɓullar ƙungiyar ta Lakurawa a ƙarshen shekarar da ta gabata.

  13. An zaɓi babban hafsan sojin Lebanon a matsayin sabon shugaban ƙasar

    Janar Joseph Aoun

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Lebanon ta zaɓi babban hafsan sojin ƙasar, Joseph Aoun a matsayin sabon shugaban ƙasar, domin cike gurbin muƙamin da aka shekara biyu babu shi a ƙasar.

    A jawabainsa na farko, sabon zaɓaɓɓen shugaban ya alƙawarta sake fasalta birnin Beirut da kudancin Lebanon bayan yaƙin Hezbollah da Isra'ila.

    Janar Aoun ya kuma ce zai yi ƙoƙarin tabbatar da ƙasar na da dokokin bai ɗaya dangane da makamai.

    Sabon shugaban ƙasar zai fuskanci tarin ƙalubale a gabansa, ciki har da lura da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma kafa gwamnati da za ta iya aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

  14. Amurka da karrama gawar Jimmy Carter da jana'izar ban girma

    Jimmy Carter

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta karrama tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Jimmy Carter, da jana'izar ban girma a birnin Washington.

    Da misalin ƙarfe 2:00 na rana agogon GMT ne za a ɗauki gawarsa daga harabar majalisar dokokin ƙasar - inda aka ajiye ta domin jama'a su yi mata bankwana - a kai ta babbar majami'ar ƙasa, inda shugaba Biden zai gabatar da jawabi wa gawar marigayin, wanda shi ma ɗan Democrat ne.

    Ana sa ran duka tsoffin shugabannin ƙasar da kuma shugaban ƙasar mai jiran gado, Donald Trump za su halarci taron da ake sa ran mutum 3,000 za su halarta.

    Daga nan kuma za a ɗauki gawar zuwa Georgia domin binneta a garinsa na Plains.

  15. An gano ƙanƙara mai shekara fiye da miliyan ɗaya a duniya

    Kankara

    Asalin hoton, PNRA_IPEV

    Masana kimiyya a nahiyar Turai sun gano ƙanƙarar da watakila ake ganin ita ce mafi daɗewa a duniya a yankin Antarctica.

    Tawagar masu binciken ta haƙo silindar ƙanƙarar mai tsawon kusan kilomita uku wanda ke ɗauke da tsohon kumfa da kuma ɓurɓushi da aka daina ganin irinsa tun fiye da shekara miliyan guda.

    Masanan na fatan cewa yin nazarin tarihin yanayin zafi da matakan iskar gas zai taimaka musu wajen hasashen sauyin yanayi a nan gaba.

    Tuni dai masu binciken suka yayyanka ginshiƙin ƙanƙarar zuwa sassa masu tsayin mita ɗaiɗai domin faɗaɗa bincike a cibiyoyin bincike a faɗin nahiyar Turai.

  16. 'Yansanda na neman wasu mata malaman coci da aka sace a Anambra

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar yansandan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta kaddamar da farautar wasu mata biyu malaman coci da aka sace a garin Ufuma da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar.

    Cikin wata sanarwar da kakakın rundunar 'yansandan jihar Tochukwu Ikenga ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata da maraice, lokacin da malaman cocin biyu ke komawa daga wani horon kwarewa da suka halarta a Ogboni.

    Kwamishinan yansandan jihar, Nnaghe Oibono Itam, da mataimakinsa sun halarci wurin da lamarin ya faru tare da bayar da umarnin gaggauta nemo inda matan biyu suke, a cewar kakakin yansandan jihar.

    Hakan na zuwa ne yan kwanakı bayan wani fitaccen malamin coci a jihar Father Emmanuel Opimma, da aka fi sani da Ebube Murinso, ya yi kira ga gwamnan jihar Anambra, Charres Soludo ya kawo ƙarshen matsalar tsaron da jihar ke tuskanta.

    Yayin jawabinsa na sabuwar shekara, Father Obimma, ya bukaci Gwamna Soludo ya sauka daga muƙaminsa idan ba zai ya daƙile masu aikata laifukan da ke ci gaba da yaɗuwa a jihar ba.

  17. Ƙura ta lafa a Chadi bayan kai hari fadar shugaban ƙasar

    Fadar shugaban ƙasar Chadi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙura ta fara lafawa a N'Djamena, babban birnin ƙasar Chadi, bayan da jami'an tsaro suka daƙile wani hari a fadar gwanatin ƙasar cikin daren da ya gabata.

    Kakakin gwamnatin ƙasar, Abderaman Koulamallah ya ce maharan na ɗauke da ƙananan makamai.

    Mista Koulamallah ya ce sojojin ƙasar sun kashe mutum 18 daga cikin maharan tare da kama shida dada cikinsu, yayin da soja guda ya rasa ransa.

    Abderaman Koulamallah ya ce babban mai shigar da ƙara na ƙasar zai bayar da cikakken bayani kan maharan, amma ya ce ba ya tunanin harin na ta'addanci ne kamar yadda aka yi hasashe tun da farko.

    Tuni aka tsaurara matakan tsaro a harabar fadar gwamnatin ƙasar.

  18. Majalisar dokokin Lebanon za ta zaɓi sabon shugaban ƙasa

    Majalisar dokokin Lebanon na taro domin zaɓae sabon shugaban ƙasa.

    Hakan na zuwa ne bayan janyewar ɗan takarar da ke samun goyon bayan ƙungiyar Hezbollah mabiya Shia, da ta fuskanci koma-baya sakamakon yaƙi da Isra'ila a shekarar da ta gabata.

    Babban sojin hafsan sojin ƙasa na ƙasar, Joseph Aoun ne ɗan takarar da mafiya yawan 'yansiyasa ke goyon baya, to sai dai yana buƙatar kashi biyu cikin uku na ƙuri'un 'yan majalisar 128.

    To amma a zagaye na biyu ana buƙatar rinjaye kawai ake buƙata.

    Sabon shugaban ƙasar zai fuskanci tarin ƙalubale, ciki har da tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a kan iyakokin ƙasar.

  19. Biden ya soke ziyararsa ta ƙarshe saboda gobarar daji a California

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Joe Biden ya soke wata ziyara da ya yi niyyar kai wa Italiya - wadda ita ce ziyarsa ta ƙarshe zuwa wata ƙasa a matsayin shugaban Amurka - domin mayar da hankali kan gobarar daji da ke ci gaba da yi wa jihar California barazana

    Aƙalla wutar daji shida ce ke cigaba da ruruwa a yankin Los Angeles na Amurka, yayin da ta baya-bayan nan ta tashi a unguwar Hollywood Hills.

    Mutum biyar aka tabbatar da mutuwarsu yayin da aka kwashe fiye da mutum 130, ciki har da wasu jaruman Hollywood masu yawa.

    Wani jami'i a hukumar kashe gobara ta jihar, ya shaida wa BBC cewa ''babu wani ci gaba'' da ake samu a ƙoƙarin kashe gobarar, saboda ƙarfin iskar da ke kaɗawa a yankin.

    Ya ƙara da cewa wutar da ke ci a unguwar Hollywood Hills, na faɗaɗa cikin sauri, yayin da hayaƙinta ya isa birnin Studio City mai makwabtaka.

  20. Tinubu ya yi alhinin sojojin Najeriya da suka mutu a harin Damboa

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar dakarun ƙasar, da aka kashe a harin da mayaƙan Boko Haram ta kai wani sansanin soji da ke ƙauyen Sabon Gida, cikin ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno.

    Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce Tinubu ya jajanta wa rundunar sojin ƙasar sakamakon mutuwar dakarunta shida a harin.

    Haka kuma shugaban ƙasar, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa harin, domin ɗaukar matakan hana faruwar makamancinsa a nan gaba''.

    A ranar Asabar ne mayaƙan ISWAP suka ƙaddamar da hari da asuba kan sansanin sojin inda suka yi arangama da sojoji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin ƙasar shida da mayaƙa fiye da 30.

    Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sojojin ƙasar bisa jajirewar da suka yi, har ta kai ga sun samu nasarar daƙile harin harin, tare da kashe gomman mayaƙan ƙungiyar.