Najeriya za ta ƙaddamar da taurarin ɗan'adam saboda tsaro
Gwamnatin Najeria ta bayyana cewa za ta ƙaddamar da tauraron ɗan'adam guda huɗu da za su taimaka wajen lura da yanayin ƙasa da kuma yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da su.
Wadannan taurarin dan'adam ɗin za a yi amfani da su wajen nazarin dazuka da kai kawon jama’a da kuma wadda za ta ɗauko hotunan tekuna da tsaunuka da kuma gano sauran ma’adinai.
Ministan sadarwa da fasahar zamani na ƙasar Uche Nnaji ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron majalisar zartaswa ta ƙasa da ya shafi kirkira da fasahohin zamani karo na ashirin da biyu, wanda ya gudana a babban birnin ƙasar Abuja.
Gwamnatin dai ta ce za ta ƙaddamar da waɗannan taurarin ɗan'adam ne domin gudanar da muhimman ayyukan da suka shafi saka ido a kan yankuna da wuraren da ke fama da matsalar tsaro da kuma ɗaukar muhimman hotunan ƙasa da suka shafi tsaunuka da ruwan ƙasar da ma sauran su