window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/01/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ibrahim Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Laraba 15-01-2025.

    A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku kasance da mu gobe, Alhamis 16-01-2025.

    Amma za ku iya ziyartar shafinmu na bbchausa.com domin ci gaba da karanta labarai da kallon bidiyo da muke sanyawa har ma ku yi muhawara.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Ganin ido na hana cin kai

  2. Gawawwakin masu haƙar ma'adinai da aka zaƙulo a Afirka ta Kudu sun doshi 80

    Masu aikin ceto

    Asalin hoton, AP

    Yawan mutanen da suka mutu a wani wurin hakar ma'adinai da aka daina amfani da shi a Afirka ta Kudu ya karu zuwa 78, bayan masu aikin ceto sun zakulo karin gawawwaki.

    Mahukunta na gargadin alkaluman za su ci gaba da karuwa yayin da ake ci gaba da wannan aiki a yankin da ke kudancin Johannesburg.

    Zuwa yanzu an ceto mutum 154 da ransu.

    Wakiliyar BBC ta ce yau an shiga rana ta hudu, ana aikin fito da mahakan da ke makale.

    'Yansanda sun ce mutanen da aka ceto na cikin yanayi na galabaita.

    Ana kuma kula da su kafin a gabatar da su a kotu kan karya dokoki.

  3. Jamus za ta yi dokar harbo jiragen sama marassa matuƙa

    Jirgin sama maras matuki

    Asalin hoton, EPA

    Majalisar ministocin Jamus ta amince kudurin dokar da za ta bai wa sojoji ikon harbo duk wani jirgin sama maras matuki da zai zama barazana ga ga rayuka ko kayan jin dadin jama'a.

    Dokokin da ake da su yanzu sun bai wa sojojin ikon kawar da jirgin ne ko yi masa harbin gargadi ko kuma tilasta masa sauka.

    An nemi yin wannan sauyin dokar ne wanda yake bukatar amincewar majalisar dokoki bayan damuwar da ake kara nunawa a kan yadda a kwanakin nan aka ga jiragen sama marassa matuka a kan muhimman kayayyakin jin dadin jama'a da kuma saman sansanonin soji.

    Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta ce, wadannan matsaloli sun karu tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine.

    Ta ce jirage marassa matuka da ake amfani da su domin leken asiri ko zagon-kasa ka iya zama babbar barazana.

  4. An tsare shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige

    Jami'an tsaro na shiga gidan shugaban kasa na Koriya ta Kudu

    Asalin hoton, Reuters

    An kai Shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige, Yoon Suk Yeol, inda ake tsare mutane, bayan tuhumarsa kan sanya dokar soji da ba ta samu karbuwa ba a cikin watan Disamba.

    A yau Laraba aka kama Mista Yoon bayan shafe tsawon sa'o'i na kiki-kaka a gidan gwamnati da ke Seoul.

    Rahotanni sun ce sai da masu binciken suka yi amfani da tsani suka haura katanga da karya wayar da ta kange gidan kafin a kamo shi.

    Sannan masu bincike sun ce Mista Yoon ya ki amsa tambayoyinsu.

    Wani mutum da ba a tantace ko wane ne ba ya banka wa kansa wuta a kusa da ofishin da ake bincikar Mista Yoon

  5. Ana murnar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Hoton Falasdinawa na murna

    Asalin hoton, Reuters

    Aa can ana ta budiri a Zirin Gaza, yankin da Falasdinawa suka sha luguden wuta na tsawon wata 15 da lalata musu rayuwa.

    Hotunan bidiyon da ake nunawa daga Deir Al-Balah da Khan Younis sun nuna mutane na ta bukukuwan murna da daga tutocin Falasdinu.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Cimma wannan yarjejeniya ta dindindin ta faranta wa Yahudawan Isra'ila da ke fatan ganin gwamnati ta ceto sauran mutanensu da ke hannun Hamas.

    A birnin Tel Aviv masu zanga-zanga na ta rungume juna.

    Kodayake akwai Yahudawan da suka nuna takaicin yadda aka dauki tsawon lokaci kafin a zo wannan gabar ta cimma yarjejeniya.

  6. 'Amurka za ta nuna wa China iyakarta a kan Taiwan'

    Donald Trump

    Asalin hoton, OTHERS

    Mutumin da shugaban Amurka mai jiran-gado Donald Trump, ya zaba domin nada shi Sakataren Tsaro, ya ce matukar a cikin shekaru goman nan Amurka ba ta nuna wa China cewa za ta dandana kudarta idan ta mamayi Taiwan ba, to lalle Sin din za ta iya mamayar yankin da har kullum take cewa mallakinta ne.

    Marco Rubio, ya bayyana hakan ne a lokacin da takwarorinsa 'yan majalisar dattawa ke yi masa tambaya a lokacin zaman tabbatar da tantance shi

    Sanatan ya ce yana da nufin sa Amurka aiki tukuru a duniya, to amma zai yi hakan ne a kan abin da ya fi muhimmanci ga Amurka da kuma Amurkawa fiye da komai.

    A game da Ukraine, ya ce kar ma a yi tunanin cewa Kyiv za ta iya tura sojojin Rasha baya zuwa bakin inda suka fara mamaye.

    Ya jaddada cewa dole ne dukkanin kasashen biyu da ke yaki su sassauta matsayarsu domin kawo karshen yakin.

    A kan kungiyar tsaro ta NATO kuwa ya ce dole ne tsarin da ake bi yanzu ya sauya, dole kawayen Amurka su rika bayar da karin tallafi ga kungiyar.

  7. Ba zan taimaki gwamnatin Tinubu ba - Sarki Sanusi

    Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

    Asalin hoton, FADARKANOTADABO

    Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai taimaki wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu ba.

    Sarkin ya bayyana haka ne a wajen taron tinawa da fitaccen lauyan nan dangwagwarmaya na Najeriya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a Lagos.

    Yace, zai iya yin bayani a kan 'yan wasu abubuwa game da abubuwan da Najeriya ke ciki da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma yadda za a iya kaucewa hakan, to amma ya ce ba zai yi hakan ba, domin idan ya yi hakan zai taimake su, shi kuma ya ce ba zai taimake su ba.

    Mai martaban ya ce, ya yanke shawara cewa ba zai yi magana a kan tattalin arziki ko sauye-sauyen da gwamnatin ke yi ba ko ma ya yi bayani a kan komai, ''saboda idan na yi bayani hakan, za taimaki gwamnatin, to amma ba na son in taimaki gwamnatin nan.''

    Ya kara da cewa, ''Abokanaina ne, to amma idan ba sa yin abu kamar abokanai, ni ma ba zan dauke su kamar abokanai ba.''

    ''Ba ma su da mutane masu kima da za su zo su yi bayanin abin da suke yi ba. Ba zan taimaka ba,'' in ji shi.

  8. An samu hauhawar farashin kaya a Najeriya cikin watan Disamba - Rahoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya an samu ƙaruwar hauhawar farashin kaya a wata na huɗu a jere, a watan Disamba, inda ya haura zuwa kashi 34.80 daga kashi 34.60 cikin 100 a watan Nuwamba, kamar yadda rahoton hukumar kididdiga ta ƙasar ya nuna.

    A wani rahoto da ta fitar, hukumar ta ce ƙarin da aka samu a watan Disamba ya zo ne sakamakon karuwar buƙatar kayayyaki ne masu nasaba da bukukuwan ƙarshen shekara.

    Kayan abinci da abubuwan sha waɗanda ba na barasa ba ne farashinsu ya fi tashi a cikin watan na Disamba.

    Hauhawar farashi a Najeriya ya yi kamari bayan da Shugaba Bola Tinubu ya karya darajar naira tare da cire tallafin man fetur a shekarar 2023, matakin da ya ce an ɗauka ne domin bunkasa tattalin arzikin ƙasa.

    An ɗan fara samun sauƙi a watan Yulin shekarar da ta gabata, yayin da tasirin faɗuwar darajar naira ya fara dushewa, kafin ƙarin farashin man fetur ya sake haifar da hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya ta’azzara matsalar tsadar rayuwa mafi muni cikin shekaru da dama a ƙasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka.

  9. 'Hamas ta amince da yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta''

    Sojan Isra'ila na nuna hoton wadanda Hamas ta yi garkuwa da su

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami'in Hamas ya gaya wa BBC cewa kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinawa ta amince da yarjejeniyar dakatar da bude wuta inda ta gabatar wa masu shiga tsakani na Qatar da Masar.

    An bayyana hakan ne yayin da kafafen yada labaran Isra'ila ke bayar da rahoton cewa Hamas ta gabatar da bukatunta na yarjejeniyar a daidai karshen tattaunawar.

    Rahoton Isra'ilar na nuna cewa bukatun na Hamas a kan zirin hanyar nan ne mai matukar muhimmanci a Gaza - wadda take a tsakanin iyakar Gaza da Masar, batun da ya kasance ake ta takaddama a kansa a yarjeniyoyin baya.

    Zuwa yanzu ba a fitar da sanarwa a hukumance ba ta amincewa da yarjejeniyar daga dukkanin bangarorin.

  10. An gurfanar da Shamsiyya a kotu bisa zargin satar wayoyi a Kano

    ...

    Asalin hoton, FB/Nigeria Police

    Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta gurfanar da wasu matasa da ta kama a jihar, gaban kotu, bisa zargin su da satar wayoyi.

    A makon da ya gabata ne rundunar ta sanar da kamen matasan bayan ƙorafe-ƙorafe da ta ce ta samu daga mutane da dama.

    Mai magana da yawun rundunar ƴansandan a jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an gurfanar da matasa, waɗanda suka haɗa da maza huɗu da mace ɗaya, wadda ake kira Shamsiyya.

    SP Abdullahi Kiyawa ya kuma ce ƴansanda sun kama ƙarin wasu mutum huɗu da suke da alaƙa da tawagar.

    Kiyawa ya ce mutum 86 ne suka kai ƙarar waɗanda ake zargi, wanda hakan ya sa Kwamishinan ƴansandan jihar, Salman Dogo Garba ya kafa runduna ta musamman domin bin diddigi, inda suka samu nasarar kama waɗanda ake zargi, kuma aka ƙwato wasu wayoyin.

    Lamarin ƙwace da satar waya a Kano - jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya - babbar matsala ce da ke addabar al'umma.

    An samu rahotanni da dama na yadda masu satar waya kan kai hari tare da illata mutane a lokacin da suke yunƙurin aiwatar da ɓarnar a jihar ta Kano.

  11. An haramta amfani da jirage marasa matuƙa a arewa maso gabashin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Najeriya (operation Hadin Kai) da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar ta haramta amfani da jirage marasa matuƙa a yankin.

    Kwamandan rundunar sojan sama, Air Commodore UU Idris, wanda ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa, ya ce amfani da jirage marasa matuƙa ba tare da izini ba yana haifar da barazana a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

    Ya bayyana cewa hukumomin gwamnati da wasu masu zaman kansu sukan yi amfani da jiragen ba tare da izinin ɓangaren sojin sama na rundunar ta Operation haɗin kai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ƴanbingdiga sun fara ƙwarewa wajen amfani da jiragen sama marasa matuka wurin kai hare-haren kan dakarun soji da kuma muhimman ababen more rayuwa na ƙasa.

    ''Cikin ƴan kwanakin nan, an samu rahotannin ganin jirage mara matuƙa a wasu wurare da ke kusa da fagen daga. A ranar 7 ga watan Janairun 2025, wani fasinja da ke cikin wani jirgin sama mai zaman kansa daga Maiduguri zuwa Monguno an kama shi da wani jirgi mara matuki a wani bincike da aka gudanar kan jirgin, inda aka ƙwace jirgin mara matuƙi, kuma a halin yanzu ana cigaba da bincike.'' in ji sanarwar.

  12. Wajibi ne Boko Haram ta dakatar da kashe-kashen da take yi - Amnesty

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar Amnesty International ta kira ga mayaƙan Boko Haram da su daina far wa mutane suna musu kisan kiyashi.

    Ƙungiyar ta bayyana haka a wani martani da ta yi kan kashe sama da mutum 40 da mayaƙan suka yi a wasu garuruwa da ke jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar 12 ga watan Janairu.

    A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya fitar, ya ce, "Ƙungiyar Amnesty tana alla-wadai da kashe fararen hula da ƴan Boko Haram suka yi, wanda ya ƙara nuna yadda rashin girmama ƴan'adam da dokokin duniya da ƙungiyar ke yi. Dole Boko Haram ne a hukunta ƴan Boko Haram da suka yi shekaru suna azabtar da mutane, da yi wa dokokin duniya karan-tsaye.

    Sanarwar ta ce bincike Amnesty ya nuna cewa mayaƙan Boko Haram sun yi wa manoman ƙawanya ne, sannan suka ware mazan, suka buɗe musu wuta, "sannan suka bi waɗanda suka yi yunkurin tserewa suna harbinsu."

    "Bayan kashe fararen hula, Boko Haram na cigaba da yin garkuwa da mata da ƴan mata da sace-sace. Yadda suke cigaba da gudanar da wannan ta'asar na nuna akwai buƙatar a ƙara ƙaimi domin kare rayuwa da dukiyar al'umma."

  13. Nijar ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfanin China don bunƙasa ɓangaren albarkatun man fetur

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da WAPCO-Niger, wani reshen kamfanin man fetur na ƙasar China (CNPC), don karfafa tsaro ga kayayyakin albarkatun man fetur,

    Shafin yaɗa labarai mai zaman kansa, Air info da ke birnin Agadez ya rawaito cewa “Haɗin gwiwar na ƙunshe da muhimman ginshiƙai da suka haɗa da tabbatar da ingantaccen tsaro a wuraren haƙo da kuma sarrafa ɗanyen mai, da aiwatar da ingantaccen shirin tsaro na ƙwararru da kafa tsarin haɗin gwiwa na kut-da-kut a tsakanin cibiyoyin biyu," an ruwaito ma'aikatar tsaro tana cewa.

    Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-hare a kan bututun Niger da Benin, wanda ke nuna buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin kare wadannan muhimman ababen more rayuwan.

    Hakan ya biyo bayan babban yunƙurin da gwamnatin mulkin sojin ke yi na inganta ƙawance da wasu ƙasahen duniya, musamman bayan yanke hulɗa da Faransa da Amurka.

  14. Matakan gwamnatin Tinubu nake suka ba shi ba – Ndume

    OTHERS

    Asalin hoton, Ndume

    Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce yana girmama Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, don haka ba ya sukarsa.

    Ndume ya bayyana haka na a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Talata, inda ya ce shi matakan shugaban ne yake suka, ba wai shi shugaban ba.

    "Ba na sukar shugaban ƙasa, matakansa nake suka. Ba wai gwamnatinsa nake suka ba, gwamnatinmu nake suka. Ni ba na sukar manya saboda mahaifina soja ne, kuma a bariki mun san muhimmancin girmama na gaba. Don haka ina girmama shi, amma ina da saɓani da shi kan wasu matakai," in ji shi.

    A game da wani bidiyon da aka gani suna raha, Ndume ya ce shugaba Tinubun ne, "ya ce ba na zuwa fadar gwamnati, sai na ce masa shi ne bai nemi ba, sai ya ce in zo a daren ranar. Har ma ya ce zai zo auren ƴata."

    Ndume ya ƙara da cewa, "na faɗa masa cewa idan ya mayar da hankali kan abubuwa biyu: tsaro da jin daɗin al'umma bayan an tabbatar da kasafin kuɗin bana, to ƴan Najeriya za su dara."

  15. Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kashe sojoji 25 a Burkina Faso

    Burkina Faso

    Asalin hoton, AFP

    A ranar 15 ga Janairun 2025 ne ƙungiyar IS mai ikirarin jihadi ta ce ta kashe sojoji 25 a arewacin ƙasar Burkina Faso.

    Mayaƙan sun kashe sojojin ne a wani harin ƙunar baki da suka kai kan sojoji kamar yadda suka bayyana a tasharsu ta Sahel Province ta Telegram a ranar 14 ga Janairu.

    Ta ce a ranar 1 ga Janairu ne mayaƙanta suka yi wa sojojin ƙasar harin ƙunar bakin wake, suka kashe guda 25, sannan sauran suke tsere, sannan suka ƙona motocin sojojin guda biyar, sannan suka ƙwace makamai.

    Mayaƙan IS dai suna addabar yankin ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar ne.

    Sai dai za a iya cewa an samu ragowar harkokin ƴan ƙungiyar a ƴan watannin da ake ciki, inda suka ɗauki alhakin hare-hare guda biyar ne kawai a tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba, idan aka kwatanta da hare-haren da suka yi a tsakanin watan Janairu da Maris na bara, inda suka kai hare-hare aƙalla 27.

  16. Gwamnatin Najeriya za ta miƙa kula da lantarki ga jihohi

    Lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya, hukumar kula da harkokin lantarki ta ƙasar, ta ce ta fara yunƙurin miƙa ragamar aikin kula da harkokin wutar lantarki ga jihohin ƙasar.

    Matakin dai zai bai wa jihohin waɗanda a yanzu su goma ne, damar sa ido da tsawatarwa kan yadda ake tafiyar da harkokin samarwa da raba wutar lantarki a cikin jihohinsu.

    Matakin dai ya samo asali ne sanadin dokar gudanar da ayyukan wutar lantarki wadda ta bai wa jihohin Nijeriya ƙarin iko kan harkokin samarwa da dakon lantarki har ma da rarraba ta a ƙasar.

  17. Ƴan gwangwan sun ce za su tsaftace sana'ar

    Gwngwan

    Asalin hoton, Ahmed Wakili

    Ƙungiyar ƴan gwangwan masu saye da sayar da tsofaffin ƙarafa a Najeriya sun ce za su ɗauki matakan tsaftace hakar a ƙasar.

    Sun bayyana hakan ne biyo bayan samun ƙaruwar rahotannin sace-sacen ƙarafa da kadarorin gwamnati da sauransu a faɗin Najeriya.

    Shugabannin ƙungiyar sun ba da sanarwar ɗaukar matakan yi wa mambobin su rijista da ba su kaya na bai -ɗaya, da sharaɗin wanda yake tsaya musu a harkar.

    A baya-bayan nan dai an kama wasu mutane da dama a Abuja bisa zargin satar murafan magudanan ruwa.

    Gwangwan

    Asalin hoton, Ahmed Wakili

  18. CBN ya ci tarar bankuna saboda rashin saka kuɗi a ATM

    CBN

    Asalin hoton, CBN/X

    Babban bankin Najeriya CB ya ci tarar wasu bankunan kasuwanci na Najeriya saboda samun kuɗi a na'urorin cire kuɗi na ATM ɗinsu a lokacin bukuwan ƙarshen shekara.

    Babban bankin ya tarar naira miliyan 150 ne kan kowane banki da ya samu da laifin, kuma bankunan sun haɗa da Fidelity da First Bank Plc da Keystone da Union da Globus da Providus da Zenith Bank da UBA da Sterling tarar naira miliyan 150.

    A wata sanarwa da aka miƙa wa bankunan, an ce za a zare kuɗaɗen ne kai tsare daga asusun ajiyan bankunan da ke babban bankin," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    "CBN ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen cin tarar duk wani bankin da ya karya dokar tabbatar da yalwatar kuɗaɗe," kamar yadda mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na bankin, Hakama Sidi Ali ya tabbatar.

    Ya kuma ƙara da cewa za su cigaba da bibiyar masu ɓoye tsabar kuɗaɗe a bankuna da masu POS.

  19. Amurka za ta cire Cuba daga ƙasashe masu ɗaukar nauyin ta'addanci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Joe Biden zai cire ƙasar Cuba a matsayin ƙasa mai ɗaukar nauyin ta'addanci a wani ɓangare na yarjejeniyar sakin fursunoni, in ji fadar White House

    Jim kaɗan bayan haka, Cuba ta sanar da cewa za ta saki fursunoni 553 da ake tsare da su saboda "laifuka daban-daban".

    Ana tunanin za su haɗa da waɗanda suka halarci zanga-zangar ƙin jinin gwamnati shekaru huɗu da suka gabata.

    Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya sake mayar da ƙasar cikin jerin ƙasashe masu ɗaukar nauyin ta'addanci a kwanakin ƙarshe na wa'adin shugabancinsa na farko a shekarar 2021, inda ya haramtawa Amurka bayar da agajin tattalin arziki da kuma fitar da makamai zuwa ƙasar.

    Amma a ranar Talata, wani jami'in gwamnatin Biden ya ce binciken da aka gudanar bai nuna wani shaida da ke goyon bayan hakan ba.

    Cuba ta ce matakin da Biden ya ɗauka mataki ne " kan madaidaiciyar hanya " duk da ce matakin "na wani ɗan lokaci ne".

  20. Boko Haram sun ƙona coci da gidaje a Borno

    Zulum

    Asalin hoton, Governor Zulum/Facebook

    Mayaƙan Boko Haram sun kai wani hari a garin Shikarkir da ke ƙaramar Chibok ta jihar Borno, inda suka ƙona wani coci da gidajen mutane.

    Sun kai wannan harin ne kimanin awa 24 bayan sun kai wani harin a ƙauyen Bazir, inda suka kashe mutum biyu tare da ƙona wani cocin daban.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno, ASP Nahum Daso ne ya tabbatar da harin Bazir a tattaunawarsa da Daily Trust, amma ya ce bai da masaniya kan harin na Shikarkir.

    Wani wanda aka ƙona masa gida mai suna Malam Daniel Shikarkir, ya ƙara da cewa, "Kafin su kawo hari, sun kai irin wannan harin a ƙauye da ke kusa da mu, yanzu haka yan garin sun watse, suna neman mafaka a wasu wuraren."