window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Abdullahi Bello, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Laraba.

    Za mu kawo muku wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.

  2. Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar mutum ɗaya da Hamas ta yi garkuwa shi a Gaza

    Rundunar sojin Israila ta ce ta gano gawar wani ɗan Israilar da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da shi a harin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Wakilin BBC ya ce rundunar sojin Israilar ta ce a jiya Talata ne aka gano gawar Yousef al-Ziyani, wanda Balarabe ne ɗan Israila mai shekara 54 a garin Rafah da ke kudancin Gaza.

    Ta ce ta kuma samu shaida da ta nuna cewa watakila ɗansa da aka yi awon gaba da shi ya mutu.

    An ɗauke shi ne tare da ɗan'uwansa da ƙanwarsa, wadanda aka sako su bayan makonni ƙalilan da kai harin a kudancin Isra'ila.

  3. Gwamnan Kano ya mayar wa 'yan APC martani kan zaɓen 2027

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, Kano State Government

    Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abba Kabir Yusuf, ya ce aikin hidimta wa Kano ne a gabansa yanzu "ba neman wa'adin mulki na biyu ba".

    Gwamnan na mayar da martani ne game da kalaman da tsohon shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya yi a farkon makon nan game da shirinsu na ƙwace mulkin jihar daga jam'iyyar NNPP a zaɓen 2027.

    Kakakin gwamnatin jihar ta Kano, Sanusi Dawakin Tofa, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa gwamnan ya yi martanin ne yayin taron tallafa wa mata a fadar gwamnatin jihar.

    "Ba neman wa'adi na biyu ne ya fi damu na ba. Na fi damuwa da sauke nauyin alƙawurran da na ɗauka a wa'adin farko...kuma ina son mutanen Kano su yi min hukunci da ayyukana a ƙarshen mulkin," a cewar gwamnan.

    Jam'iyyar NNPP ta ƙwace mulkin Kano ne a zaɓen 2023 bayan APC ta yi wa'adin mulki biyu na shekara takwas ƙarƙashin Abdullahi Umar Ganduje.

  4. Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi na Kano zuwa Kaduna

    Layin dogo

    Asalin hoton, Nigeria Railway Corporation

    Bankin raya ƙasa na China ya bai wa Najeriya rancen dala miliyan 254.76 domin gina titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.

    Sanarwar da bankin ya fitar na zuwa ne gabanin ziyarar ministan harkokin wajen China a Najeriya cikin mako mai zuwa.

    Minista Wang Yi zai isa Najeriya domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da sauran manyan jami'an gwamnatin tarayya tun daga ranar Laraba.

    Aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203, ana sa ran zai laƙume dala miliyan 973 amma ya dakata saboda ƙarancin kuɗi.

    "Idan aka kammala shi, layin dogon zai haɗe Kano, mai muhimmanci a arewacin Najeriya, da kuma Abuja babban birnin ƙasar, inda zai ba wa mutane damar yin tafiya mai sauƙi," a cewar sanarwar da bankin ya wallafa a shafinsa na intanet.

    Tun da farko gwamnatin Najeriya ta ce Exim Bank na China zai ɗauki nauyin aikin a 2020, amma sai ya janye.

  5. EFCC ta tsare jami'anta 10 bisa zargin satar kayan aiki

    Jami'an EFCC

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta tsare jami'anta 10 game da zargin hannunsu a ɓacewar wasu kayayyakin aiki.

    An kama jami'an ne a makon da ya gabata, kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukan zumunta ta bayyana yau Laraba.

    "Jami'an da aka kama makon da ya gabata bisa umarnin Shugaba Ola Olukoyede, na amsa tambayoyi game da ɓatan wasu kayayyakin aiki," in ji kakakin EFCC Dele Oyewale.

    Wannan sanarwa na zuwa ne bayan hukumar ta sanar da korar jami'an nata 27 a shekarar da ta gabata saboda "zambatar mutane" da sauran laifuka.

  6. Shugaban Jamus ya gargaɗi Trump kan ƙwace iko da Greenland

    Olaf Scholz

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya gargaɗi shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, kan barazanar da ya yi ta ƙwace iko da yankin Greenland.

    Mista Scholz ya ce "kowace ƙasa na da haƙƙin kare iyakarta".

    "Ba zai yiwu a dinga sauya iyaka da ƙarfin tuwo ba," kamar yadda ya faɗa a birnin Berlin a yau. "Wannan haƙƙin yana nan kuma shi ne ƙashin bayan zamanmu lafiya."

    Shugaban na mayar da martani ne ga kalaman Trump yayin taron manema labarai ranar Talata cewa ba zai iya janye yiwuwar ko zai yi amfani da ƙarfin soja ba wajen ƙwace iko da Greenland a Denmark ko kuma Panama Canal a Mexico.

    Trump wanda zai karɓi mulki a wa'adinsa na biyu ranar 20 ga watan Janairu, ya sha nuna sha'awar ƙwace yankin na Greenland.

    Shi ma Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya caccaki Trump ɗin, yana mai cewa dole ne Tarayyar Turai ta kare kanta.

  7. An umarci mutum 37,000 a Los Angeles su bar gidajensu saboda wutar daji

    Wutar daji

    Asalin hoton, EPA

    Robert Luna, shugaban 'yansandan gundumar Palisades a Loa Angeles ta Amurka, ya ba da sabbin bayanai game da wutar da ke ci ganga-ganga.

    Ya ce an wajabta wa mutum 37,000 su bar gidajensu.

    An ce aƙalla gine-gine 15,000 ne ke cikin haɗarin ƙonewa ƙurmus. Ba tare da ya fayyace bayani ba, ya ce tuni wasu mutane suka ji raunika da kuma gidajen da suka aka rasa saboda gobarar.

    Zuwa yanzu wutar da ta fara ci kunsan kwana ɗaya a Los Angeles, ya mamaye fadin kadada 2,950.

  8. 'Yansandan Najeriya sun kama saurayin da ya haɗa baki da budurwarsa don 'damfarar' iyayenta

    Mutanen da ake zargi da damfara

    Asalin hoton, NG Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Delta da ke kudancin ƙasar ta kama saurayi da budurwarsa bisa zargin haɗa baki domin damfarar iyayen yarinyar.

    Da yake gabatar da matasan da aka ɓoye fuskokinsu a wani ofishin 'yansanda, kakakin rundunar SP Bright Edafe ya ce matasan sun tsara cewa saurayin ya kira mahaifan budurwar ya ce ya sace ta kuma nemi kuɗin fansa.

    Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama matasan ne bayan mahaifiyar budurwar ta kai musu rahoton sace 'yar tata.

    A cewarsa: "A ranar 30 ga watan Disamba Princess mai shekara 21 ta je gidan saurayinta Prince kuma ta ba shi shawarar cewa su haɗa baki don neman kuɗi a wajen iyayenta.

    "Prince ya kira iyayen nata kuma ya ce musu ya yi garkuwa da ita, har ma ya nemi kuɗin fansa naira miliyan biyu."

    Matashiyar wadda ta yi magana daga baya a ofishin, ta ce sun yi niyyar su raba kuɗin ne a tsakaninsu.

  9. Ministan harkokin wajen Faransa ya caccaki Trump kan yankin Greenland

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan harkokin wajan Faransa Jean Noel Barro ya caccaki zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump kan ƙin bayyana cewa ba zai yi amfani da ƙarfin soji wajen ƙwace ikon yankin Greenland mai cin gashin kansa ba.

    Yankin dai wani ɓangare ne ƙasar Denmark.

    Sai dai ya jaddada cewa Tarayyar Turai ba za ta bar wata ƙasa ta kai wa iyakokinta masu ƴanci hari ba.

    Ya ce Turai nahiya ce mai ƙarfi, "kuma za mu ci gaba da ƙarfafa kanmu."

    A baya dai Trump ya yi magana kan ƙoƙarin da yake yi domin sayen yankin Greenland, buƙatar da mutanen yankin na Denmark suka yi watsi da ita.

  10. Transparancy ta buƙaci gwamnatin Nijar ta saki ɗan gwagwarmaya Tchangari

    Moussa Tchangari

    Asalin hoton, Moussa Tchangari/Facebook

    Ƙungiyar Transparancy International a Nijar, ta yi kira ga gwamnatin mulkin soji a Nijar ta gaggauta sakin Moussa Tchangari shugaban ƙungiyar Alternative da take tsare da shi.

    A cikin sanarwar da ƙungiyar mai rajin shugabanci na gari ta fitar, Transparency International ta nuna damuwa kan tsare Tchangari.

    A cewar ƙungiyar, hakan ya saɓa ƙa'ida.

  11. Abin da muka tattauna a kai tare da wasu ƴan adawa a Najeriya - Al-Mustapha

    Al-Mustapha

    Asalin hoton, Other

    Bayanai suna ci gaba da fitowa bayan wata ganawa da wasu fitattun ƴan siyasar Najeriya suka yi a ofishin jam’iyyar SDP a Abuja.

    Rahotanni na cewa mai yiwuwa tattaunawar na da alaƙa da yunƙurin jam’iyyun hamayya a Najeriya na ƙwace mulki daga hannu jam’iyyar APC.

    Cikin waɗanda aka yi zaman har da Nasir El-Rufa’i wanda a baya-bayan nan ya musanta cewa ya koma jam’iyyar PDP da kuma Hamza Al-Mustapha wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar AA a zaɓen 2023 da sauransu.

    Game da ganawar, Al-Mustapha ya bayyana wa BBC cewa a taron, kowa ya tofa albarkacin bakinsa kan halin da ƙasar take ciki, inda ya ƙara da cewa a yanzu magana suke yi ta ta samu haɗin kai da fahimtar juna.

  12. Ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a Zamfara

    Zamfara

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni na cewa ana ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan sauƙin da aka samu a ƴan watannin nan.

    Wasu mahara sun shiga garuruwa da dama na ƙaramar hukumar Maru, inda suka kashe aƙalla mutum 20 tare da yin garkuwa da gommai.

    Waɗanda BBC ta zanta da su sun ce ƴan bindigar sun shiga garuruwan ne da motoci inda suka kwashi kayan abinci da sauransu.

    Wannan dai na zuwa ne bayan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu na hallaka wasu daga cikin shugabannin ƴan bindigar a jihar ta Zamfara.

  13. Mutanen da suke juya gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Dalung

    Dalung

    Asalin hoton, NFF

    Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya a zamanin shugaba Buhari, Solomon Dalung, ya ce mutanen da ke juya gwamnati ta bayan fage waɗanda ake kira 'cabal' na mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sun fi na zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari haɗari.

    Dalung ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels a ranar Talata, inda ya ce a zamanin mulkin Buhari, wasu mutane sun riƙa juya akalar gwamnatin.

    Sai dai ya ce waɗanda suka juya mulkin Buhari ba su da ilimi da wayewa sosai, amma waɗanda suke juya gwamnatin Tinubu sun fi ilimi da sanin mulki kuma sun fi tarin buri.

    Dalung ya ce, "lallai akwai masu juya gwamnati ta bayan fage a zamanin Buhari. Amma mutanen wancan lokacin ba su da ƙwarewa sosai a kan mulki da siyasa, don haka tasirin ya taƙaitu. Amma waɗanda suke mulkin Tinubu, sun fi wayewa kuma sun fi ilimi da sanin ƙarfin mulki. Wannan ya sa gwamnatin za ta sha wahala sama da na zamanin Buhari."

  14. RSF da rundunar sojin Sudan sun kashe mutum 190 a Darfur

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar likitocin Sudan ta zargi sojojin ƙasar da dakarun RSF da kashe kusan mutum 200 a gumurzun da suke yi a wasu yankuna da ke yankin Dafur, kamar yadda jaridar intanet ta Sudan Tribute ta ruwaito.

    "Rahoton ƙungiyar ya gano an kashe mutum 190, sannan an jikkata wasu guda 106 a sanadiyar ruwan bama-bamai a tsakanin ɓangarorin biyu a kudanci da arewacin Dafur a ƴan kwanakin nan."

    Rahoton ya nuna cewa dakarun RSF sun kashe sama da mutum 30, ciki har da mata da ƙananan yara a al-Fashir, sannan sojoji sun kashe mutum 115 a Kabkabiya da wasu mutum 45 a Nyala a kudancin Dafur.

    A ƴan makonnin da ake ciki, sojojin Sudan sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a kan dakarun RSF a Dafur.

  15. Kocin Faransa Deschamps zai ajiye aiki bayan Gasar Kofin Duniya ta 2026

    Didier Deschamps

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan da ya taimaka wa Faransa lashe gasar Kofin Duniya, Didier Deschamps ya ce zai ajiye aikinsa bayan kammala gasar cin Kofin Duniya ta baɗi da za a gudanar a ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Mai 56, shi ne mutumin da ya fi daɗewa yana jagorantar tawagar ƙasar, bayan da ya fara aikin a 2012.

    Ya taimaka wa Faransa lashe gasar Kofin Duniya ta 2018, da aka buga a ƙasar Rasha, sannan ya kai tawagar ƙasar wasan ƙarshe a gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.

    Kafin nan a 2016 ya taimaka wa ƙasar kai wa matakin wasan ƙarshe a gasar nahiyar Turai ta EURO 2016.

    "Zuwa 2016, komai zai ƙare. Na cimma burikana," kamar yadda Deschamps ya shaida wa kafar yaɗa labaran Faransa ta TF1.

    "Na cimma muradina, na buri da fatan kai Faransa babban mataki a fagen tamaula''.

    Har yanzu Faransa ba ta fara wasanta na neman gurbin Gasar Cin Kofin duniya ta 2026 ba, yayin da rukunin da take ciki ya dogara da sakamakon wasan kwata fayinal da ƙasar za ta kara da Croatia cikin watan Maris.

  16. Gagarumar gobara ta kori dubban mutane a California

    Wutar daji

    Asalin hoton, Getty Images

    Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta ƙone gidaje ƙurmus a yankuna da dama yayin da take ƙara matsowa zuwa birnin.

    Mutane sun riƙa ficewa daga motoci suna arcewa a guje domin tsira da rayukansu, wasu sun bayyana lamarin a matsayin tamkar a fim.

    A cikin sa'o'i kaɗan, iska mai ƙarfin gaske ta ruruta wutar dajin zuwa yankuna da dama na jihar California.

    Aƙalla mutum 30,000 ne aka bai wa umurnin ficewa daga yankin yayin da gobarar ke bunƙasa, daga fili mai girman eka 10 zuwa 3,000.

    Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya ce ƴan kwana-kwana sun riƙa umartar mutane su fice daga motocinsu domin tsira daga wutar.

    Wutar daji

    Asalin hoton, Getty Images

    Wutar daji

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jerin gwanon motoci suna tserewa daga yankin a baya can kuma hayaƙi ya turnuƙe
    Wutar daji

    Asalin hoton, EPA

  17. Daga almajiranci na zama shugaban NNPC - Kyari

    Mele Kyari

    Asalin hoton, NNPC Limited/X

    Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce yana godiya ga Allah da ɗaga darajarsa daga wanda ya taɓa karatu a makarantar tsangaya ta amajirai har ya kai ga zama shugaban NNPCL a Najeriya.

    Mele Kyari ya bayyana haka ne a shafinsa na X, a saƙonsa na godiya ga Allah bisa cika shekara 60 a duniya.

    A cewarsa, "cikin ikon Allah, a yau nake cika shekara 60 a duniya, duk da na riga na kai tun a baya idan aka yi la'akari da watan musulunci. Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar zama shugaban kamfanin makamashi mafi girma a Afirka."

    Kyari ya ce yana godiya ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ma Najeriya bisa wannan damar da ya samu.

    "Idan na waiwayi baya, nakan tuna gwagwarmayar da na sha. Nasarori da ƙalubale waɗanda Allah ne kaɗai ya san yadda na samu nasarar kai wa ga matakin da nake ciki yanzu."

    Ya ce yanzu ya ƙara samun ƙarfin gwiwar hidimta wa ƙasarsa, sannan ya yi godiya da malamansa na tsangaya da na boko da sauran ƴan uwa da abokan arziki, tare da neman yafiya ga duk waɗanda ya saɓa musu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Amurka ta sanya wa shugaban dakarun RSF takunkumi

    RSF

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin shugaba Joe Biden na Amurka ta sanya wa shugaban sojin dakarun ƴan tawayen RSF na Sudan takunkumi, kan zargin dakarunsa da aikata kisan ƙare dangi.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce an ɗauki matakin ne kan Mohamed Hamdan Dagalo da aka fi sa ni da Hemeti, kan rawar da yake takawa wajen azabtarwa da kashe ƴan Sudan a yaƙin da dakarunsa ke yi da gwamnati.

    Blinken ya ce RSF suna kashe yara maza da manya, da cin zarafin mata ta hanyar lalata musamman ga tsirarun ƙananan ƙabilun ƙasar ta Sudan.

    An kuma sanya takunkumi kan kamfanonin RSF da dama da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da takunkumi kan masu taimaka musu da makamai.

    Tun a shekarar 2023 ce yaƙi ya ɓarke tsakanin gwamnatin Sudan ƙarƙashin jagorancin Abdul Fatta al-Burhan da ƴan tawayen RSF.

  19. IC ta maka tsohon kwamishinan El-Rufai a kotu

    IC

    Asalin hoton, TWITTER/NASIR ELRUFA'I

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya IC ta maka kwamishina a tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi.

    Jami'in shari'a na hukumar IC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka Bashir Sa'idu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa.

    A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohuwar gwamnatin da almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.

  20. Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

    Tsaro

    Asalin hoton, DEFENCE HQ/X

    Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kan sojojinta a jihar Borno.

    A wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce an kashe sojoji guda shida, sannan wani kwamandan ƴan sa-kai ya jikkata.

    Sai dai Buba ya ƙara da cewa a gumurzun, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan Boko Haram 34, sannan sun ƙwato wasu makamai.

    Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya. A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar da ke jihar Borno.