Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 23 ga watan Maris 2025.
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Aliyu Jaafar da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Erdogan ya ce zanga-zangar goyon bayan magajin garin Istanbul da aka 'ɗaure ta riƙiɗe zuwa rikici.
Ya ce babbar jam'iyyar adawa ce take da alhakin lalata kayan hukuma da raunata ƴan sanda, don haka ya sha alwashin cewa za ta girbi abin da ta shuka.
Ya ce wasan kwaikwayon su zai ƙare, kuma za su ji kunya.
Tun da farko ƴan sandan Turkiyya sun sanar da kama mutane 1,100 bayan shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da kama magajin garin Istanbul, Ekrem Imamoglu a ranar Laraba bisa zarginsa da cin hanci.
Sama da masu zanga-zanga 70 aka tsare cikin dare yayin zanga-zanga a kusa da Istanbul.
Wakiliyar BBC ta ce da dama daga cikin waɗanda suka yi dandazo sun shaida cewa sun fito ne ba don neman a saki magajin gari ba kawai, sun fito ne don kare dimokuraɗiyya a Turkiyya.
Ƴan sanda sun kuma kama wasu ƴan siyasa masu tsattsauran ra'ayi da lauyoyi da kuma ƴan jarida goma yayin wani samame da suka kai birnin Istanbul da birnin Izmir da asuba.
A yau Nafisa Muhammad ko Nafeeyskitchen ta nuna mana yadda ake yin 'scotch egg' wato haɗin dunƙulen ƙwai da aka lullube da nama.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, National Police Of Ukraine
Asalin hoton, Other/Facebook
Wasu fusatattun matasa sun wawushe abincin da aka yi niyyar raba wa na watan Ramadan a jihar Gombe, wanda rahotanni suka ce ya fito daga wajen ɗan shugaban ƙasar Najeriya, Seyi Tinubu.
Seyi dai yana rangadi a wasu jihohi da ke arewacin ƙasar, inda yake haɗuwa da mazauna jihohin da kuma shugabannin siyasa wajen buɗa-baki.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna matasan na wawason katan-katan na kayan abinci daga kan wata mota da ke tsaye a bakin titi.
An hangi matasan na harba wa waɗanda ke ƙasa kayan abincin - inda suke karɓa suke kuma yin gaba.
Kayan abincin sun haɗa da buhunan shinkafa da sikari da mai da kuma gishiri.
Yayin da aka raba ɗaya daga cikin motocin ɗauke da kayan abincin, matasan sun tare guda inda suka yi wawason komai da ke cikinta.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce ta sake kama fursunoni biyar cikin 12 waɗanda suka tsere daga gidan yari da ke garin Kotonkarfe a jihar Kogi.
Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Abubakar Umar ya fitar yau Litinin, ta ce sun samu nasara sake kama mutanen ne tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro.
"Mun sake kama fursunoni biyar, muna kuma ci gaba da ƙoƙari domin ganin mun kama sauran," in ji sanarwar.
Abubakar ya ce muƙaddashin kontrola na hukumar ya bayar da umarnin yin cikakken bincike kan yadda fursunonin suka samu tserewa.
Ya kuma ce tuni aka aika ƙarin jami'an tsaro da tsaron gidan yarin da kuma dukkan gidajen yari da ke faɗin ƙasar, don kauce wa afkuwar irin haka a gaba.
"Muna yin kira ga al'umma da su kwantar da hankali da kuma bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar ba su muhimman bayanai da za su kai ga sake kama waɗanda suka rage," in ji Abubakar.
Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar yau Litinin, inda wasu fursunoni 12 daga sashen waɗanda ke jiran yanke musu hukunci, suka samu hanyar da ta kai su tserewa daga gidan yarin.
Angola ta sanar da janyewa a matsayin mai shiga tsakani a rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Tsawon shekaru biyu shugaba Joao Lourenco na ƙoƙarin kawo ƙarshen rikici tsakanin ƴan tawayen M23 da Rwanda ke goyon baya da kuma sojojin Kongo.
A watannin baya-bayan nan ƴan tawayen M23 sun ƙwace wasu yankuna masu arziƙin ma'adinai.
A makon da ya gabata, Qatar ta sanar da karɓar baƙuncin shugaban Rwanda Paul Kagame da takwaransa na Congo Felix Tshisekedi.
Asalin hoton, Reuters
Adadin mutanen da suka jikkata a harin makami mai linzami da Rasha ta kai birnin Sumy na Ukraine, ya kai 65, ciki har da yara 14, a cewar jami'ai.
Wata sanarwa da suka fitar, ta ce an kai harin ne da misalin karfe 2 na rana agogon ƙasar - a wuri kuma da ke cunkoson jama'a.
Sun ƙara da cewa tuni aka kaddamar da bincike kan harin.
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a kafofin sada zumunta sun nuna yadda harin ya lalata gine-gine da kuma hayaki da ke tashi sama daga gidaje.
Asalin hoton, Official news of Sumy Regional State istration/Telegram
Asalin hoton, Getty Images
Jami'an kiwon lafiya na yankin Falasɗinu sun ce harin Isra'ila na ranar Litinin ya kashe sama da mutum 20 a Gaza.
Wannan na zuwa ne sa'oi kaɗan bayan sojojin Isra'ila sun kai wani hari a babban asibitin da ke Khan Younis, inda suka kashe aƙalla mutum biyu, ciki har da wani babban kwamandan Hamas, Ismail Barhoum da wani hadiminsa.
Ana tunanin Barhoum na cikin jagororin siyasa na Hamas biyu da suka rage a Gaza.
Isra'ila dai na cigaba da kai zafafan hare-hare ta sama da ta ƙasa a Gaza, sannan kuma ta hana shigar da magunguna da sauran kayayyakin buƙata zuwa zirin.
Asalin hoton, FB/Natasha Uduaghan
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC ta karɓi ƙorafi daga wasu daga cikin mutanen yankin Kogi ta Tsakiya, inda suke buƙatar hukumar ta shirya musu zaɓen kiranye ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa ta Najeriya.
Wata mai suna Charity Ijese ce ta miƙa ƙorafin a madadin ƴan mazaɓar a ofishin hukumar da ke birnin Lokoja a jihar Kogi, sannan babbar sakatariyar hukumar a jihar, Mrs. Rose Anthony ta karɓa ƙorafin a hukumance.
A cikin takardar ƙorafin, sun rubuta cewa, "mu da muka sanya hannu a wannan ƙorafin halastattun masu kaɗa ƙuri'a ne a mazaɓar Kogi ta Tsakiya, don haka muke so mu yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba mu dama."
Asalin hoton, Getty Images
Shugabar hukumar yaƙi da cutar AIDS ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu kusan mutum miliyan tara da za su kamu da cutar ta HIV nan da shekara huɗu masu zuwa saboda dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa a ɓangaren kiwon lafiya.
Da take jawabi a Geneva, Winnie Byinyama, ta ce za a samu sabbin masu kamuwa da cutar aƙalla guda 2,000 kullum saboda janye tallafin - ta ce tuni dubban likitoci da sauran ma'aikatan jinya sun fara rasa aikinsu.
Sai dai duk da haka ta yaba da gudumawar Amurka wajen tallafa wa ayyukan kiwon lafiya a duniya a gomman shekaru da suka gabata.
Amma ta ce yadda kwatsam aka dakatar da tallafin ba tare da shiri ba, ya fara kawo tsaiko a ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da cutar ta HIV.
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Babbar jam'iyyar adawa a ƙasar Turkiyya, Republican People's Party (CHP) ta bayyana Magajin Garin Istanbul, Ekrem Imamoglu, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓen ƙasar da ke tafe nan da shekara uku masu zuwa.
Yanzu haka dai Ekrem Imamoglu yana tsare a hannun hukumomi, inda gwamnatin Turkiyya ke tuhumarsa da cin hanci da taimakon ƙungiyar ta'addanci, duk da cewa ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
An tsayar da shi ne bayan wata ƙuri'ar jin ra'ayi, wadda jagoran jam'iyyar ya ce kusan mutum miliyan 15 sun kaɗa.
Hakan na zuwa ne duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale a kan Imamoglu na tuhume-tuhumen da yake fuskanta.
Haka kuma Jami'ar Istanbul ta sanar da cewa za ta soke digirinsa saboda wasu kura-kurai da ta ce ta gano.
Idan aka tabbatar da matsalar, takararsa ta shugaban ƙasa za ta fuskanci tsaiko, saboda kundin tsarin mulkin Turkiyya ya ce dole shugaban ƙasa ya zama yana da shaidar karatu a babbar makaranta.
Amma dai lauyoyin Ekrem Imamoglu sun ce za su ɗaukaka ƙara.
Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa, Alhaji Shehu Musa Gabam ya yi watsi da yunƙurin haɗaka tsakaninta da sauran jam'iyyun adawa da nufin tunkarar zaɓen 2027, sannan ya bayyana cewa babu wani mutum da aka yi wa alƙawarin samun tikitin takarar shugaban ƙasa.
Wannan na zuwa yayin da ake ganin tagomashin jam'iyyar ta SDP ya karu sakamakon sauya sheƙar da wasu manyan 'yansiyasa a ƙasar ke yi zuwa cikinta.
Asalin hoton, Getty Images
Idan ƙungiyar Chelsea da ke Ingila ta fasa sayen Jadon Sancho na dindindin, dole za ta biya ƙungiyar Manchester United kuɗi har fam miliyan biyar.
Ɗan wasan mai shekara 24 ya koma Chelsea ne a matsayin aro daga Machester United na shekara ɗaya a watan Agustan bara, inda a cikin yarjejeniyar aka amince Chelsea na da zaɓin sayensa a kan tsakanin fam miliyan 20 zuwa miliyan 25 matuƙar kulon ɗin ba ta haura ta 14 ba a teburin gasar Premier ta Ingila a kakar bana ba.
Yanzu dai Chelsea ce ta huɗu, kuma saura wasa tara kakar ta ƙare.
Yanzu dai shawara ta rage ga Chelsea, inda take da zaɓin ko dai ta saye shi, ko kuma ta mayar da shi kulob ɗinsa, ta biya makudan kuɗin.
Da farko dai Chelsea ta nuna sha'awar riƙe ɗan wasan, amma yanzu rahotanni na nuna cewa hankalin ƙungiyar ya fara rabuwa kan cigaba da riƙe shi.
Ɗan wasan ya fara ƙwallo a Chelsea da ƙafar dama, amma daga bisa abubuwa suka sauya, inda a wasa 18 da suka gabata, sau ɗaya kawai ya taimaka aka zura ƙwallo.
Rahotanni dai na cewa tuni Chelsea ta fara zawarcin wani ɗan wasan gefen da na gaba.
Asalin hoton, Reuters
An kama masu zanga-zanga sama da 1,100 tare da tsare su saboda gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kama Magajin Garin Istanbul, Ekrem Imamoglu.
An kama Imamoglu ne a ranar Laraba ta makon jiya, inda gwamnatin ke tuhumarsa da cin hanci da taimakon ƙungiyar ta'addanci.
Haka kuma an tsare masu zanga-zangar sama da 70 a Kocaeli da ke kusa da Istanbul.
Haka kuma ƴansanda sun kama wasu ƴansiyasa da lauyoyi da aƙalla ƴanjarida guda 10 a wani samame da suka kai a unguwar Izmir da ke Istanbul.
Asalin hoton, Shekarau New Media Facebook
Ɗaya daga cikin jagororin siyasa a arewacin Najeriya, tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ba lallai ne haɗakar da wasu manyan ƴan siyasar ƙasar ke yi don tunkarar zaɓen 2027 ta yi wani tasiri ba.
Shekarau ya bayyana haka ne a zantawarsa da BBC, inda ya ce saɓanin haɗakar da suka jagoranta a 2015 da ta kai ga kawar da mulkin PDP a shekara 16, a yanzu ƴan siyasa ne kawai ke ganawa a tsakaninsu, ba da yawun jam'iyyunsu ba.
A game da zargin ko dai yana yi wa APC aiki ne, Shekarau ya ce ba haka ba ne, "ai idan ina so zan yi aiki da APC, zan je kai-tsaye ne. A cikin shugaban ƙasa da gwamnoni babu wanda idan ina son ganinsa ba zan iya ba."
"Ni dai shawara na bayar cewa yunƙurin nan zai yi nasara ne kawai idan an jawo jam'iyyun hamayya an tafi tare da su," in ji shi.
Asalin hoton, Nigeria Correctional Service
Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere bayan sun fasa wani gidan yarin gwanmatin Najeriya da ke garin Kotonkarfe a jihar Kogi.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna ɗaya daga cikin waɗanda suke tsere.
Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami'an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar ranar Litinin.
Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, "sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne. Dole a gudanar da bincike mai zurfi, sannan a kamo fursunonin da suka tsere, sannan a gano waɗanda suke da hannu," in ji Fanwo.
Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga kafofin sadarwa na yankin Falasɗinawa na nuna cewa hare-haren Isra'ila ta sama a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza sun kashe aƙalla mutum biyar.
Isra'ila ta kai hare-haren ne a kusa da wata makaranta da ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke ƙara matsa lamba wajen kai hare-hare, inda yanzu haka akwai dubban sojoji da suke jiran umarnin kutsawa zirin na Gaza.
A ranar Lahadi ne dai Isra'ila ta kai hari a wani asibitin Gaza, inda ta kashe wani babban jami'in Hamas da yake jinya a asibitin.
Asalin hoton, X/@SimFubara
Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalaya Fubara ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa yana da alaƙa da ƙungiyoyin ƴanbindiga da ke fasa bututun man fetur, inda ya ce hotuna da bidiyo da ake yaɗawa ƙarya ne.
Ya ce ana yaɗa labaran na ƙaryar ne domin a tayar da zaune tsaye a jihar, sannan a ɓata masa suna, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Fubara ya bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Nelson Chukwudi ya fitar, inda ya ce Fubara na alla-wadai da yada labaran na farfaganda.
"Gwamna Fubara ba shi da wata alaƙa da ƙungiyoyin ƴanbindiga masu fasa bututun mai, kuma bai taɓa tunanin ƙulla wata alaƙa da su ba, sannan kuma ba zai taɓa alaƙa da ɓatagari da suke barazana ga zaman lafiya da tattalin arzikin jihar Rivers ba," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Fubara ya nanata shirinsa na tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, inda ya ƙara da cewa ba a cin moriyar gwamnati ba tare da zaman lafiya ba.
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya yi alla-wadai da harin ƴanbindiga a wani masallaci da ke garin Kokorou a Jamhuriyar Nijar, inda suka kashe masallata masu dama.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Sharif ya bayyana harin a matsayin "abin takaici", sannan ya ƙara da cewa "musamman ganin yadda aka kashe mutane suna sallah a watan Ramadan mai alfarma. Wannan ya ƙara nuna cewa ta'addanci ba shi da addini, kuma babu tausayi a ciki," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "a madadin ƴan ƙasar Pakistan, muna alla-wadai da wannan harin na dabbanci, sannan muna taya ƴan Jamhuriyar Nijar baƙin ciki da jaje," in ji shi.
Rahotanni dai na cewa aƙalla mutum 44 ne ƴanbindiga suka kashe, sannan suka jikkata gommai a harin, wanda suke kai a wani masallaci da ke garin na Kokorou.