Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Alhamis.
Mu haɗu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.
Umar Mikail ne ke fatan za mu kwana lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 27/02/2025
Usman Minjibir, Abdullahi Bello Diginza, Isiyaku Muhammed, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Alhamis.
Mu haɗu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.
Umar Mikail ne ke fatan za mu kwana lafiya.
Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce akalla mutum 70 sun rasa ransu sakamakon cutar kwalara, yayin da wasu mutum fiye da 2,000 kuma suka kamu da cutar a cikin mako ɗaya.
Cutar ta ɓarke ne a jihar White Nile da ke kudancin Khartoum babban birnin ƙasar, kuma hakan na da nasaba da wani hari da jirgi maras matuki ya kai a tashar samar da lantarkin da ke sama wa al'ummar yankin tsaftataccen ruwan sha.
Kungiyar agajin ta ce yara ne suka fi galabaita a wannan yaki da aka shafe sama da shekara biyu ana tafkawa, inda suke kamuwa da cutuka da kuma yunwa.
Fadan ya kara tsanani a jihar ta White Nile a 'yan kwanakin nan.
Asalin hoton, Bashir Ahmad
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gidansa na birnin Kaduna daga Daura na jihar Katsina, a cewar tsohon mai taimaka masa na musamman Bashir Ahmad.
Buhari ya koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina tun bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023.
Tsohon shugaban ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Gwamnan Borno Babagana Zulum, da Gwamnan Kaduna Uba Sani.
Akwai kuma sauran 'yansiyasa da tsofaffin jami'an gwamnati da suka tarɓi shugaban a gidan nasa.
Asalin hoton, Bashir Ahmad
Rundunar 'yansandan Najeriya a jihar Legas ta ce ta mayar wa kakakin majalisar dokkin jihar jami'an da ke tsaron lafiyarta.
An janye wa Mojisola Meranda jami'an tsaron ne a safiyar yau Alhamis, abin da ya ƙara ta'azzara cecekuce game da rikicin shugabancin majalisar.
Da yake magana yayin taron manema labarai bayan matakin, Kwamashinan 'Yansanda Moshood Jimoh ya ce sun janye su ne tun da farko saboda bincike.
"Yanzu haka da nake magana da ku, an kammala bincike kan jami'an tsaron da ke tare da Hon. Mojisola Miranda, kuma sun koma domin ci gaba da tsare lafiyarta," in ji shi.
A yau ne tsohon kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, ya koma zauren majalisar yana mai iƙirarin cewa ya koma kan muƙaminsa, iƙirarin da 'yanmajalisar suka musanta.
Asalin hoton, Reuters
Abdullah Ocalan, jagoran 'yantawayen ƙungiyar PKK ta Ƙurdawa da aka ɗaure a gidan yari, ya nemi mabiyan nasa da su ajiye makamansu.
Kalaman nasa da 'yanmajalisa masu goyon bayan Kurdawa suka karanto na da niyyar kawo ƙarshen shekaru sama da 40 da aka shafe ana rikici a kudu maso gabashin Turkiyya.
Rikicin ya yi sanadiyyar kashe dubun dubatar mutane, kuma ya raba wasu dubbai da muhallansu.
Ocalan mai shekara 75 ya gana da 'yanmajalisar tun da farko tsawon awanni a Tsibirin Imrali da ke kudu maso yammacin birnin Istanbul, inda aka tsare shi tun 1999.
"Babu wata hanya saɓanin dimokuraɗiyya wajen kafawa ko kuma neman wani abu na siyasa," a cewar wasiƙar da Ocalan ya aika.
Ke gwana ce a girki? Za ki iya ba mu dabarar sarrafa abincin da zai yi daɗin ci a lokacin azumi?
Kamar yadda muka saba a kowace shekara, za ku iya aiko wa BBC bidiyon girke-girkenku don koya wa mutane ta waɗannan hanyoyi.
Asalin hoton, Kano State Government
Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya ya kafa kwamatin da zai bincika yadda aka yi game da ƙorafin da wasu ma'aikatan jihar ke yi na ƙin biya ko kuma yanke musu albashi a watan Janairu.
Abba Kabir ya bayyana lamarin da "take haƙƙin ma'aikata da kuma ha'intar jama'a", kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Alhamis.
"Wannan gwamnatin ba za ta taɓa yarda da rashin adalci ga ma'aikatanmu ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma," kamar yadda sanarwar ta ruwaito gwamnan na faɗi.
An umarci kwamatin ya gudanar da "cikakken bincike" kan tsarin biyan albashi na gwamnatin jihar don gano "ko kuskuren na'ura ne ko kuma da gangan", sannan ya ba da shawarar matakin da za a ɗauka.
Kwamatin ya ƙunshi jami'an gwamnati 10 ƙarƙashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, wanda shi ne kwamashinan raya karkara da cigaban al'umma.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƴansanda a ƙasar Japan na zargin wata mata da sumbatar wani jami'inta ba tare da izininsa ba.
An ga matar tana goga leɓɓanta a wuyar ɗansandan wanda ke cikin tawagar masu badujala, a lokacin wani taro a bara.
Dama jami'in ɗansandan ya amince cewa zai rungumi mutane dubu ɗaya domin nuna murnar kammala aikinsa na ɗamara.
Za a iya tuhumar matar, mai kimanin shekara 50 da laifin cin zarafin lalata.
Ya zuwa yanzu ta ƙi amsa gayyatar da ƴansanda suka yi mata domin amsa tambayoyi.
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer na gab da fara tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House.
Wannan ganawa ta farko tsakanin shugabannin ƙasashen biyu, tun bayan shammatar da Trump ya yi wa ƙasashen Nato na fara tattaunawa da Rasha kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Ana sa ran Starmer zai bayyana wa Trump dalilan da suka sanya ake buƙatar samar wa Ukraine garkuwar tsaro daga Rasha kafin tsagaita wuta.
A jiya Laraba, Sir Kieir ya sanar da shirin Birtaniya na ƙara yawan kuɗin da ƙasar ke kashewa kan tsaro.
Asalin hoton, X/Lagoshouseof assembly
Ɗan majalisar dokokin Legas mai wakiltar mazaɓar Agege a jihar Legas, Mudashiru Obasa ya ce ya koma bakin aiki a matsayin shugaban majalisar.
Obasa ya bayyana haka ne a lokacin da ya shiga zauren majalisar a yau Alhamis.
Lokacin da aka tambaye shi game da tsigewar da aka masa, Obasa ya ce “Babu wanda ya tsige ni. Batun tsigewa ko ma mene ne abu ne da ke buƙatar a bi doka.”
Sai dai wasu daga cikin ƴan majalisar masu goyon bayan ƴar majalisar Mojisola Meranda, wadda aka naɗa shugabar majalisar a kwanakin baya, sun yi watsi da batun, inda suka dage kan cewa Meranda ɗin ce shugabar majalisar.
Obasa ya bayyana a harabar Majalisar ne tare da rakiyar jami’an tsaro.
Shigarsa harabar majalisar a yau Alhamis ita ce ta farko yun bayan tsige shi da majalisar ta yi a watan Janairun da ya gabata.
Wani yaro ɗan shekara 14 ya yi rashin nasara a shari’ar da ya shigar da iyayensa ƙara bayan sun ɗauke shi daga Landan zuwa Ghana domin kai shi makarantar kwana.
Yaron - wanda aka bayyana a gaban kotu a matsayin mai kunya, haziƙi, mai son dafa abinci da zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa - ya ce iyayensa ne suka yaudare shi da zuwa Afirka, inda suka ce ziyarar dubiya za su tare da shi.
Ya ce da ya san makarantar kwana za a kai shi “ba zan amince da tafiyar ba”.
Amma babbar kotun da ke Landan ta saurarin ba'asin iyayen nasa, waɗanda suka ce, sun ɗauki matakin ne sakamakon damuwar da suke da ita kan yadda tasowa cikin samun ƙwarewar aikata laifuka.
A wata rubutacciyar sanarwa da yaron ya aike wa kotun, ya ce: "Ina jin kamar ina zaune a jahannama, haƙiƙa ban yi tunanin na cancanci hakan ba kuma ina so in dawo gida, Ingila, da nan ba da jimawa ba''.
"A cikin hukuncin da ya yanke, alkalin babbar kotun Mista Justice Hayden ya ce ya gane cewa "iyayen sun yi hakan ne domin gyaruwar yaron, ba domin cutar da shi ba''.
"Ya ce ya gamsu da cewa burin da iyayen ke da shi na mayar da yaron Ghana ya kasance "saboda a bayyane take tsantsar soyayyar yaron ce ba nufin zaluntarsa ba".
Alƙalin ya ƙara da cewa yaron na cikin hadarin fuskantar babbar illa idan ya koma Burtaniya, don haka ya yi watsi da ƙarar yaron.
Asalin hoton, AFP
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya isa ƙasar Somalia inda ya tattaunawa da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na ƙasar, a wani mataki da ake kallon yana alamta gyaruwar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu bayan watanni suna takun saƙa.
Ƙasashen biyu masu maƙwabtaka sun fara samun saɓani tun bayan wani yunƙuri da Habasha ta yi na kafa filin jirgin ruwa a yankin Somaliland da ta ayyana cin gashin kanta daga Somalia, lamarin da aka yi fargabar zai jawo tashin hankali a yankin.
Mazauna yankin Mogashisu sun ce an kai hare-hare a unguwannin da suke kusa da filin jirgin sama jim kaɗan bayan shugabannin ƙasashen biyu sun tsere.
Sai dai babu tabbacin ko dai hare-haren suna da alaƙa da ziyarar ta Mista Abiy.
Rahotonni daga DR Kongo na cewa an samu fashewar wasu abubuwa biyu da kuma harbe-harben bindiga a wajen gangamin da ƴantawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a birnin Bukavu.
Jagoran ƴantawayen Corneille Nangaa, ya gabatar da jawabi a gaban cincirindon mutane a birnin Bukavu, wanda ƴantawayen suka kwace a baya-bayan nan daga hannun sojojin ƙasar.
Wasu hotunan bidiyo sun nuna yadda tarzoma ta tashi da kuma gawarwakin mutane yashe a kan titi.
Ƴantawayen dai sun ƙwace manyan birane da dama a yankin a ƴan makonnin nan.
Asalin hoton, FACEBOOK Ibrahima Kassory Fofana
Wata kotu a Guinea ta yanke wa tsohon firaministan ƙasar, Ibrahima Kassory Fofana hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari tare da biyan tarar kuɗin ƙasar, s biliyan biyu, bayan da ta same shi da laifin wadaƙa da dukiyar gwamnati da cin hanci da rashawa da kuma ɓarnatar da kuɗi.
An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis ba tare da bayyana Mista Fofana a kotu ba.
Tun bayan kama shi a 2022 bai taɓa bayyana a gaban kotun da ke yi masa shari'ar ba, to amma ya sha musanta zarge-zargen.
Tsohon firaministan na fuskantar shari'a kan zargin karkatar da wasu biliyoyin kuɗaɗe da aka ware don tunkarar annobar Covid da sauran ayyukan tallafi a ƙasar.
Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace maƙudan kuɗaɗen waje da na ƙasar daga cikin asusun bankunansa, waɗanda ta ce ba ta hanyar halal ya same su ba.
Haka kuma kotun ta ce Mista Fofana zai biya s biliyan 18 a matsayin tara na ɓata wa ƙasar suna
Tuni dai lauyoyin tsohon firaministan suka ce za su ɗaukaka ƙara game da hukuncin.
Tun bayan juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar Alpha Condé a 2021, hukumomin mulkin sojin ƙasar suka riƙa kama tsoffin ƙusoshin hamɓararriyar gwamnatin.
Kassory Fofana ya kasance firaministan Guinea tsakanin 2018 zuwa 2021 lokacin da sojoji suka ƙwace mulkin ƙasar.
Asalin hoton, Getty Images
Masu shiga tsakani daga ƙasashen Amurka da Rasha na ganawa a birnin Santambul na ƙasar Turkiyya, domin maido da hulɗar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu bayan komawar Donald Trump fadar White House a matsayin shugaban Amurka.
Ganawar na zuwa ne mako guda bayan manyan jami'an diplomasiyyar kasashen biyu, (Sergei Lavrov da Marco Rubio) sun amince a fara tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ba tare da sanya Kyiv ɗin a cikin tattaunawar ba.
Kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya jaddada cewa Rasha ba ta shirya mayar wa Ukraien yankunata da ta ƙwace.
Sojojin Isra'ila sun ce uku daga cikin gawarwaki huɗu na ƴan ƙasar - da Hamas ta mayar daga Gaza a ranar Alhamis - Hamas ce ta kashe su, yayin da suka ce na huɗun ya rasu ne sakamakon harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Hamas ta miƙa gawarwakin inda Isra'ila ta saki fursunoni fiye da 600, kuma ita ce musaya ta ƙarshe a matakin farko da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.
Hamas ta ce a shirye take ta tattauna mataki a mataki na biyu a na yarjejeniyar - wadda za ta ƙunshi sakin duka Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su domin janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza.
Asalin hoton, ORTN
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta gabatar da wani ƙudiri na yanke wani kaso na albashin ma'aikatan ƙasar domin yin wani asusu na musamman domin samun kudaden gudanar da wasu ayyukan gwamnati.
Manufar asusun shi ne tattara kuɗaɗe daga al'ummar ƙasar domin tallafa wa ayyukan gwamnati, musamman fannin tsaro da sauran muhimman ɓangarori da ke fuskantar gazawa da taɓarɓarewa tattalin arziki tun bayan juyin mulkin 2023.
Wannan batu ya janyo zazzafar muhawara a ƙasar musamman tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago, waɗanda ke ganin matakin a matsayin wata hanya ta tatsar ma'aikatan.
A baya-bayan nan dai hukumomin asusun suka sha caccaka a shafukan sada zumunta bayan, wasu bayanai da shugaban asusun ya fitar kan kuɗaɗen da ya ce asusun ya ce ya kashe, ciki har da amfani da intanet, ta kimanin saifa miliyan 45 a ofishin gidauniyar cikin wata shida.
Asalin hoton, Getty Images
Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhamad Sa'ad Abubakar III na sanar da fara duba watan Ramadan daga gobe Juma'a 28 ga watan Sha'aban, wanda ya yi dai dai da 29 ga watan Janairun 2025.
Cikin wata sanarwa da shugban kwamitin harkokin addini na fadar mai Alfarmar, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar ranar Alhamis ya ce idan aka ga watan a sanar da fadar mai alfarmar ta hanyar wasu lambobin waya da ya bayar.
Sanarwar ta ƙara da cewa idan ba a ga watan a ranar Juma'a ba, to ranar Lahadi za ta kasance 1 ga watan Ramadan na wannan shekara.
A ranar Laraba ne dai hukumomin Saudiyya suka da fara duba watan Ramadan ɗin daga gobe Juma'ar.
A kowace shekara idan watan azumi ya zo mata da dama kan shiga tunanin waɗanne irin abinci za su dinga tsara wa iyalansu don buɗa baki.
Haka ake fama duk shekara, kuma ba wai don ba su iya girkin ba sai don neman sabbin girke-girken da za a dinga gigita maigida da su.
To a sauƙaƙe kamar yadda muka saba a wannan karon ma BBC Hausa za ta zo maku da hanyoyin burge masu gida cikin sauƙi, tare da taimakon mata 'yan uwanmu.
Ke gwana ce a girki? Za ki iya ba mu dabarar yadda za a sarrafa abinci na zamani ko na gargajiya da zai yi daɗin ci a lokacin azumi?
To ga wata dama ta samu. Ki aiko mana da bidiyo na haɗaɗɗen abinci kala ɗaya wanda bai wuce minti biyu ba.
Asalin hoton, Getty Images
Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar janar Olufemi Oluyede ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kuɗin alawus na kullum da ake RCA da ake ba sojojin Najeriya, wanda yanzu ake ba su naira 1,500.
Da yake yi wa sojojin sashe na 81 jawabi a Legas, Oluyede ya ce za a ƙara alawus ɗin zuwa naira 3,000 daga wata mai zuwa.
Baya ga ƙarin na RCA, babban hafsan ya ce rundunar sojin ƙasan Najeriya za ta fara ba sojoji lamunin kuɗi a kan kuɗin ruwa na kashi 3, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ba sojoji shawarar su nemi bashin kuɗin, domin a cewarsa biyan ba zai zama musu matsala saboda babu ruwa mai girma a ciki.
A game da tsarin gidaje, janar ɗin ya ce za su faɗaɗa shirirnsu na lamunin gidaje a Abuja da Ibadan da Jos da Fatakwal da Owerri da Akwa Ibom.
Ya ce a tsarin, sojoji za su iya samun gida a kan kuɗi naira miliyan 8 zuwa sama.