window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai-tsaye.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Laraba, tabawa ranar samu, 26 ga watan Fabarairun 2025, sai kuma gobe Alhamis idan Allah Ya kai mu.

    A nan muke wa juna fatan alheri tare da fatan za ku ci gaba da leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo, har ma ku yi muhawara a kai.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Komai gaggawar asara ta jira samu

  2. Jam'iyyar APC ta amince da salon shugabancin Tinubu

    Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta amince tare da bayar da goyon bayanta ga salon mulkin Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.

    Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a lokacin taron ƙolinta a yau Laraba a Abuja, inda kuma ta amince shugabanta Abdullahi Umar ganduje ya ci gaba da jan ragamarta.

    A yayin taron ne, shugabannin jam'iyyar suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayansu ga yadda shugaban ƙasar ke gudanar da mulki, tare da yabawa da ƙoƙarinsa.

    Taron wanda shi ne na ƙoli wajen ɗaukar matsaya game da harkokin jam’iyyar ya mayar da hankali ne kan nazari a game da abubuwan da suka shafi jam’iyyar, da nasarorin da ta samu da kuma ɓangarorin da take buƙatar gyara.

    A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce matakin taron kwamitin ƙolin zaburarwa ce ga gwamnatinsa, inda ya yi alƙawarin ƙara zage damtse wajen tafiyar da harkokin ƙasar.

    Tinubu wanda ya sha alwashin cewa ba zai ba wa jam'iyyar kunya ba, ya kuma tabbatar da cewa tattalin arziin ƙasar na kan hanyar farfaɗowa.

    Akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar da ba su halarci taron na yau ba, lamarin da ake alaƙantawa da fushinsu a kan yadda harkokinta ke tafiya.

    To amma kuma taron ya tattauna a kan wasu ƴaƴan jam’iyyar, waɗanda ba sa jin daɗin yadda ake gudanar da ita.

    Wannan shi ne karon farko da jam'iyyar ta APC ke gudanar da taron ƙolin, tun bayan rantsar da Shugaba Tinubu a watan Mayun 2023.

  3. Shugaban Ukraine zai kai wa Donald Trump ziyara

    Trump da  Zelensky

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump ya tabbatar da cewa takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, zai kai ziyara Washington a jibi Jumma'a domin sanya hannu a kan yarjejeniyar kasafta albarkatun kasar Ukraine.

    Mr Zelensky, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin ta share fage, sannan kuma yana fatan za a ƙulla wasu yarjeniyoyin da za su tabbatar da tsaron Ukraine bayan an tsagaita wuta tsakaninta da Rasha.

    Ya ce zai kuma yi tambaya a kan ko Amurka za ta ci gaba da ba wa Ukraine tallafi ko kuma a'a.

    Sai dai kuma Mr Trump ya nuna alamar cewa ba zai bayar da wani tabbaci a kan tabbatar da tsaron Ukraine ba, yana mai cewa ƙasashen Turai ne ya kamata su yi hakan

  4. Matatar Ɗangote ta sake rage farashin man fetur

    Hoton Dangote a matatarsa

    Asalin hoton, X/DangoteGroup

    Matatar Man Ɗangote ta sake rage farashin man fetur daga naira 890 a kan lita zuwa naira 825 - wato ragin naira 65 kenan a kan kowace lita ga 'yan kasuwa.

    A wata sanarwa da ta kamfanin ya fitar a yau Laraba, ya ce ragin zai fara aiki ne daga gobe Alhamis, 27 ga watan nan na Fabarairun 2025.

    kamfanin ya ce ya yi haka ne domin sauƙaƙa wa al'umma Najeriya, yayin da suke shirin fara azumin watan Ramadana, tare kuma da tallafa wa shirin Shugaba Tinubu na neman farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar rage wa al'ummar ƙasar nauyin kuɗaɗe da ke kansu.

    Wannan shi ne karo na biyu da matatar take rage farashin man fetur a watan na Fabarairun 2025, inda da farko ta yi ragin naira 60.

    Haka kuma a watan Disamba na 2024 lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, matatar ta rage farashin man fetur ɗin da naira 70.50, daga naira 970 zuwa 899.50 domin sauƙaƙa wa jama'a a cewar matatar.

    A sanarwar kamfanin ya yi kira ga 'yankasuwa masu sayar da man da su tallafa wa wannan yunƙurin nashi na rage wa 'yan Najeriya wahala, su tabbatar al'umma ta amfana da wannan sauƙi.

  5. Mutane na rububin zuwa gidan makoki don cin taliya a China

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴan ina-da-abinci a China na tuɗaɗa zuwa wani gidan binne mamata domin ɗanɗana wani haɗin taliya wanda aka yi ta magana kansa a shafukan sada zumunta.

    An fi samun abincin ne a wani gidan binne mamata da ake wa laƙabi da Erlong Funeral Home a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin ƙasar China.

    Wani gidan abinci ne ke haɗa taliyar inda yake sayar da ita ga gidajen da ake zaman makoki.

    Gidan binne mamata na Erlong kan bai wa masu zaman makoki nau'uka daban-daban na taliyar a lokacin karin kumallo da kuma lokacin da rana ta ɗaga. wadda farashinta kan kai farashi kimanin dala 1.38.

    Haɗin taliyar da ya fi fice shi ne wanda ake dafawa tare da naman alade da gyaɗa.

    Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan binne mamatan ya ce tun asali akan bayar da taliyar ce ga waɗanda suka je gidan domin aiki ko kuma ke da alaƙa da mamaci.

    Sai dai a lokacin da mutanen yankin suka fara magana kan daɗin ɗanɗanon taliyar, sai aka samu mutane suka fara marmarin ɗanɗanawa ta shafukan sada zumunta.

    Wani da ya je domin ɗanɗana taliyar ya ce layin waɗanda suka je domin cin taliyar ya fi na waɗanda suka je domin nuna alhini.

    Wani da ya ziyarci abokinsa a yankin da nufin cin taliyar ya rubuta a shafin sada zumunta cewa "har yanzu ban samu ɗanɗana taliyar ba saboda mamar abokina ba ta san ɗan'uwan wani mamaci ba."

    A yanzu waɗanda suka yi sa'ar ɗanɗana taliyar na ci gaba da santi a shafukan sada zumunta kan daɗinta.

  6. MDD ta yi kira da a yi watsi da shawarar Trump kan Gaza

    Donald Trump

    Asalin hoton, OTHERS

    Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya buƘaci Ƙasashe mambobi su yi watsi da duk wani shiri na Ƙwace iko da yankunan Falasdinawa da kuma korar mutanen da ke wajen.

    Volker Turk, ya shaida wa taron hukumar cewa irin waɗannan shirye-shirye sun saɓa dokokin ƙasa da ƙasa kuma suna barazana ga duk wani shirin zaman lafiya a yankin.

    Shugaba Trump na Amurka ya bayar da shawarar cewa ya kamata a kwashe Falasɗinawa daga Gaza sannan kuma a sake gina yankin a ƙarƙashin kulawar Amurka.

    Kazalika Mista Turk, ya kuma yi kira da a gudanar da bincike na musamman a kan yiwuwar aikata laifin yaƙi da Isra'ila da Hamas suka yi.

  7. Yau Hamas za ta bayar da gawawwakin 'yan Isra'ila da take riƙe da su

    Sojojin Isra'ila ɗauke da wata gawa

    Asalin hoton, OTHERS

    Isra'ila ta ce Hamas za ta mayar da gawawwakin Isra'ilawa huɗu da suka mutu a wajenta a lokacin da take garkuwa da su a yau Laraba.

    Za a mayar da gawawwakin ne a ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma yanzu.

    Wani jami'in Hamas ya ce a madadin haka Isra'ila kuma za ta saki Falasɗinawa 600 da fursunonin da take tsare da su bayan shafe kwanaki ba ta saki ba kamar yadda aka tsara.Kazalika za a saki wasu ƙarin mata 23 da yara Falasɗinawan.

    Dukkan ɓangarorin biyu - Isra'ila da Hamas sun ce za a miƙa gawawwakin ne ba tare da wani taro ba.

    A ɓangare guda kuma wata 'yar uwar iyalin 'yar Isra'ilar dan, Bibas da aka kashe a lokacin da ake tsare da ita a Gaza, ta yi kira ga gwamnatin Isra'ila da ta ɗauki alhakin kashe 'yan uwanta da aka yi a lokacin da suke hannun Hamas.

    Ta ce ya kamata a ce hukumomin Isra'ila sun ceto 'yan uwan nata, to amma sai suka mayar da hankali wajen ɗaukar fansa.

    Ta ce yafiya na nufin mutum ya ɗauki alhakin abin da ya aikata da kuma nuna aniyar sauya hali da ɗaukar darasi daga kuskuren da mutum ya aikata.

    Yafiya ba ta da amfani idan ba a binciko kura-kuran da aka yi ba, sannan kuma jami'an da suka yi ba daidai ba su amsa laifinsu.

  8. Dubban mutane za su iya mutuwa a Sudan - MDD

    wasu mata da 'ya'yansu

    Asalin hoton, MSF / Mohamed Zakaria / Reuters

    Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce dubban mutane za su iya mutuwa bayan an tursasa musu janyewa daga sansanin ‘yan gudun hijira na Zamzam da ke yammacin Sudan.

    Akwai kusan mutum dubu 500 da ke zaune a sansanin wanda ƙazamin faɗa tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF ya raba da muhallinsu.

    Tuni ƙungiyar likitoci masu taimako ta duniya, ta Medicins San Frontiers (MSF) ta dakatar da ayyukanta a wajen tun a ranar Litinin.

    Ana fama da matsananciyar yunwa a sansanin.

    Ministan harkokin wajen gwamnatin Sudan ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar a ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a yankin har cikin watan azumi.

  9. Mali ta riƙe shugabannin kamfanin haƙar ma'adanai na Australia kan haraji

    Gwal a hannun wani

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kamfanin haƙar ma'adanai na Australiya ya ce zai biya gwamnatin Mali harajin dala miliyan 160. Sanarwar na zuwa ne bayan da ba zato ba tsammani aka tsare shugaban kamfanin da wasu ma'aikatansa biyu tsawon kwana goma a lokacin da suka kai ziyara ƙasar da ke yammacin Afirka domin aiwatar da wasu tsare-tsaren kamfanin.

    Kamfanin ya yi alƙawarin fara biyan dala miliyan tamanin nan take, yayin da zai cika sauran cikin 'yan watanni masu zuwa.

    Mali na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samar da ma'adanai a Afirka.

  10. Karon farko ƙyanda ta kashe yaro a Amurka cikin shekara 10

    Cikin wani mai ƙyanda

    Asalin hoton, getty

    Wani yaro da ba a yi wa riga-kafi ba a jihar Texas ta Amurka ya rasu sakamamakon kamuwa da cutar ƙyanda - wannan shi ne karon farko da cutar mai saurin yaɗuwa ta yi kisa a Amurka tun shekara ta 2015.

    Tun daga farkon shekarar nan ta 2025 an samu mutane sama da 130 da suka kamu da cutar a yammacin jihar ta Texas da kuma jihar New Mexico mai maƙwabtaka

    Jami'ai sun ce yawancin waɗanda suka kamun yara ne da matasa masu shekara goma sha, waɗanda ko dai ba a yi musu riga-kafi ba ko kuma ba a san matsayinsu ba game da riga-kafi (walau an yi musu ko ba a yi musu ba).

    Wurin da cutar ta fi ƙamari shi ne Gaines, inda wuri ne da ake da Kiristoci masu bin ɗariƙar Menno waɗanda galibi ba su cika yarda da rigakafi ba.

  11. 'Yansandan Najeriya sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo

    'Yansandan Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Ƴansanda a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya sun ce sun yi nasarar ceto mutum uku da wasu 'yanbindiga suka yi garkuwa da su.

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta bayyana cikin wata sanarwa a shafinta na X cewa ta kai samamen ne bayan kai hari a ƙauyen Agede da ke Ibadan babban birnin jihar a ranar Talata.

    "Samamen da muka kai tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na yankin sun ba mu nasarar ceto mutum uku; Olori Hakimat Sadia, da Olori Rakyat, da Monsuru Ganiyu," a cewar sanarwar.

    Ta ƙara da cewa an sace su ne daga fadar basarake Tajudeen Inaolaji a ranar Litinin, kuma sun yi nasarar kama ɗaya daga cikin masu garkuwar.

  12. APC ta amince Ganduje ya ci gaba da jagorancinta

    Abdullahi Umar Ganduje

    Asalin hoton, OTHERS

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da salon jagorancin shugabanta, Abdullahi Umar Ganduje.

    A taron da jam'iyyar ta kammala yau Laraba a Abuja, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun yaba da rawar da Ganduje ya taka tun bayan naɗa shi kan muƙamin a watan Agustan 2023.

    Hakan na nufin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano zai ci gaba da jagorancin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa, inda za a zaɓi cikakken shugaba.

    A watan Agustan 2023 ne kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo na ƙasa, bayan ajiye aikin shugaban jam'iyyar da ya gabace shi, Sanata Abdullahi Adamu.

  13. Rundunar ƴansandan Najeriya ta kama 'yanbindiga 20 a jihar Taraba

    Bindiga ƙirar AK-47

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Taraba ta ce ta kama mutum 20 da take zargi da fashi da makami a jihar.

    Rundunar ta wallafa hakan ne a shafinta na X, inda ta ce ta kama su ne a yau Laraba bayan ta kai samame maɓoyarsu da ke wata gonar shinkafa a yankin Wamunchi.

    Sun kuma ce sun yi nasarar ƙwato makamai ciki har da bindiga ƙirar AK-47 ɗaya, da ƙunshin harsasai bakwai, da bindigar harba-ruga uku, da kwari da baka, da kuma babur ɗaya.

    Rundunar ƴansandan Najeriyar ta kuma ce jami'anta a faɗin ƙasar sun zage damtse wajen yaƙi da manyan laifuka, kamar garkuwa da mutane, da fashi da makami, da ta'addanci da sauran laifuka.

  14. Ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutum 30 a Afghanistan

    Ambaliya a Afghanistan

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ambaliya da aka yi a Afghanistan a shekarar da ta wuce

    Hukumomi a Afghanistan na ci gaba da neman mutanen da ruwa ya tafi da su bayan wata ambaliya a jiya Talata.

    Hukumomin sun tabbatar da cewa mutum 34 ne suka mutu a lokacin da ake ruwan saman mai ƙarfi da ƙanƙara, sai dai sun ce adadin zai iya ƙaruwa.

    Akasarin waɗanda abin ya shafa na zama ne a tsaunukan da ke lardin Farah.

    Masu binciken kimiyya sun ce Afghanistan na fama da matsalar sauyin yanayi, inda fari da kuma ambaliya ke haddasa raguwa wajen ayyukan noma.

    Aƙalla kashi 80 na mutanen da ke yankin na dogaro ne da noma.

  15. 'Yansandan Kano sun kama mutum 17 da zargin shirya zanga-zanga

    'Yansandan Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya a jihar Kano ta ce ta kama mutum 17 kan zarginsu da aikata daba da kuma shirya zanga-zanga.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce bayanan sirri da ta tattara ne suka ba ta nasarar kama mutanen, amma ba ta bayyana dalilin shirya zanga-zangar ba.

    Sai dai bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa wasu matasa sun taru a kusa da gidan sarki na Nassarawa, wanda Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ke ciki, kafin 'yansanda su tsarwatsa su da safiyar yau Laraba.

    "Bayan samun bayanan sirri game da shirin zanga-zangar tayar da fitina da wasu ke yi, 'yansanda tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro sun fita wasu muhimman wurare a ƙwaryar birnin Kano domin daƙile zanga-zangar," a cewar sanarwar.

    Har yanzu batun masarautar Kano na ci gaba da jan hankalin mazauna jihar, inda Aminu Ado da Muhammadu Sanusi ke bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano.

  16. Ficewar ƙasashen AES daga Ecowas ya ƙara wa sojin Najeriya nauyi - Air Marshall Hassan

    Shugabannin rundunar sojin sama ta Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Airforce

    Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya Air Marshall Hassan Abubakar ya ce ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga ƙungiyar Ecowas ta ƙara ɗora wa rundunar sojin Najeriya nauyi.

    Ficewar ƙasashen na Alliance of Sahel States (AES) daga tsarin aiwatar da tsaro ya birkita alƙiblar tsarin gaba ɗaya, a cewarsa yayin da yake magana yayin wani taron kwamandojin sojin sama a Abuja yau Laraba.

    Ya ƙara da cewa hakan zai shafi rundunar haɗin gwiwa ta Multinational t Task Force (MNJTF) kai-tsaye, wadda ke yaƙar ƙungiyoyin Boko Haram da Iswap a Najeriya, da Nijar, da Chadi, da Kamaru.

    "Matakin da suka ɗauka na fita [daga Ecowas], da kuma Chadi da ke tunanin ficewa, zai shafi ikon MNJTF na gudanar da ayyukanta," kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito shi yana faɗa.

    "Saboda haka nauyin da ke kan rundunar sojin Najeriya domin tallafa wa MNJTF zai ƙaru, wanda zai buƙaci cikakken martani da tsari daga rundunar sojin sama ta Najeriya."

  17. An sasanta rashin jituwa tsakanin Isra'ila da Hamas game da tsagaita wuta

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wasu Isra'ilawa kenan da suka taru domin zanga-zangar alhinin mutuwar iyalan Bibas

    Jami'an Isra'ila da na ƙungiyar Hamas sun ce masu shiga tsakani sun sasanta rashin jituwar da aka samu ta baya-bayan nan a yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Isra'ila ta jinkirta sakin Falasɗinawa 600 ranar Asabar da ta wuce domin nuna fushinta kan abin da ta ce "wulaƙanta mutanen da Hamas garkuwa da su" yayin sakinsu. Hamas ta ce hakan yin hakan karya sharuɗɗan yarjejeniyar ne.

    Ana tsammanin yanzu za a saki fursunonin da kuma wani rukunin, ƙila a yau Laraba ko kuma Alhamis, a madadin mutumu huɗu da Hamas ta saka.

    Hakan zai share wa jakadan Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff fage, wanda ya ce zai je yankin domin jawo ɓangarorin su fara tattaunawar zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar.

    Labarin ya zo ne yayin da dubban Isra'ilawa suka taru a Rishon LeZion domin kallon jana'izar Shiri Bibas da 'ya'yanta biyu - waɗanda Hamas ta bayar da gawarsu a makon da ya gabata.

  18. Saudiyya ta umarci a fara duba watan Ramadana daga ranar Juma'a

    Jaririn wata

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Ƙolin Saudiyya ta nemi 'yan ƙasar su fara duba jaririn watan watan Ramadana daga yammacin ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu.

    Hakan ya yi daidai da 29 ga watan Sha'aban na shekarar Hijira ta 1446 a kalandar Musulunci.

    Shafin Inside the Haramain ya ruwaito cewa an umarci duk wanda ya ga watan ya kai rahoto ga reshen kotun mafi kusa da shi.

    A Najeriya ma za a fara duba watan ne daga Juma'a, saboda ya yi daidai da ranar ƙarshe ta watan na Sha'aban.

    Ganin sabon watan na nufin Musulmai za su fara ibadar Azumin Ramadana mai girma, inda za su shafe kwana 29 ko 30 suna guje wa ci ko shan wani abu tun kafin fitowar rana har zuwa faɗuwarta.

  19. Ƙasar Kuwait za ta tallafa wa yaran Kaduna 200,000 da ba su zuwa makaranta

    Yara a Damasak

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin ƙasar Kuwait ta jaddada aniyarta ta tallafa wa yara 200,000 da ba su zuwa makaranta a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

    Jakadan Kuwait a Najeriya, Salim Almuzayen ne ya sanar da yunƙurin yayin taron Ranar Ƙasa ta Kuwait karo na 64 da aka gudanar a Abuja, kamar yadda kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

    Almuzayen ya yi bayanin cewa shirin zai taimaka wajen samar da ingantaccen ilimin firamare ga yara musamman masu larura ta musamman, da mata, da ma manya a Kaduna.

    "Hakan na nuna ƙwarin daɗewar alaƙa [tsakanin Najeriya da Kuwait] da kuma irin yadda za mu ci gaba da aikin haɗin gwiwa tun daga shekarun 1960 - lokaci da aka gina makarantar Al-Sabah a Kaduna," a cewar jakadan.

  20. Mun ninka kason kuɗaɗen jihohi sau uku saboda cire tallafin man fetur - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya sa gwamnatinsa ta ninka kuɗaɗen da take bai wa jihohi daga asusun tarayya sau uku.

    Da yake magana yayin taron shugabannin jam'iyyarsu ta APC a Abuja ranar Talata da dare, Tinubu ya lissafa abubuwan da ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnatinsa damar yi.

    "Babu ta yadda za a yi Najeriya ta ɗore matuƙar ba a daina biyan tallafin [man fetur] ba," in ji shi.

    "Mun ninka kaso na kuɗin da jihohi ke samu sau uku. Muna da isassun kuɗin da za mu bai wa ƙananan hukumomi. Mun kafa hukumar Nelfund da za ta dinga biyan kuɗin karatun 'ya'yanmu.

    "Za mu iya saita makomar ƙasar nan. Abubuwan da ke faruwa a duniya na burge ni, ba don komai ba sai yadda suke koya mana darasi cewa mu 'yan Najeriya za mu iya gina kanmu kuma mu taimaka wa Afirka ta ci gaba."

    Matashiya: Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, wanda ya sa farashinsa ya tashi daga ƙasa da N200 zuwa sama da N1,000 a yanzu.