Ana ci gaba da zanga-zanga a Turkiyya a dare na uku
Asalin hoton, EPA
An shiga dare na uku a zanga-zangar adawa da tsare Magajin Garin birnin Istanbul na Turkiyya.
Jam'iyun hamayya sun ce kama jargoran ƴan hamayyar kuma babban abokin adawar Shugaba Erdogan, Ekrem Imamoglu bita da ƙullin siyasa ne.
Shugaba ƙasar Turkiyyar Erduwan ya haramta yin duk wata zanga-zanga, sai dai yan ƙasar sun bijirewa umarninsa.
An sake buɗe filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan
Asalin hoton, Getty Images
An sake buɗe filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan, bayan tsaikon da aka samu wajen sufurin jirage.
An koma aiki ne bayan an dawo da wutar lantarkin, wadda dama rashinta ne ya jawo tsaikon.
Babban jami'in gudanarwar filin jirgin, Thomas Woldbye ya nemi afuwar fasinjojin, inda ya ce dole ce ta suka dakatar da aiki, domin shirin ko-ta-kwana ba zai yiwu ya zama 100 bisa 100 ba.
Ƙungiyar kamfanonin jiragen sama ta ƙasa da ƙasa ta ce matsalar lantarkin da aka samu abin takaici ne, inda ta ce bai kamata a ce Hearthrow tana ta'allaƙa ne da hanyar makamashi ɗaya tal ba kawai.
Tsaikon dai ya shafi sama da fasinjoji 200,000 ne.
Najeriya ta doke Rwanda da ci 2 da nema
Asalin hoton, X/Super Eagles
Ƴan wasan Super Eagles na Najeriya sun doke Rwanda da ci 2 da nema a wasan neman shiga Gasar Cin Kofin duniya da aka kara a birnin Kigali.
Ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ne ya zura dukkanin ƙwallayen biyu gabanin hutun rabin lokaci.
Hakan na nufin yanzu Najeriya na matsayi na huɗu a cikin ƙasashe shida da ke a rukunin C, bayan wasanni biyar-biyar.
Mashahurin ɗan leƙen asiri na duniya ya mutu
Ɗaya daga cikin ƴan leƙen asiri mafiya muhimmanci na duniya lokacin yaƙin cacar baka, Oleg Gordievsky ya mutu yana da shekara 86 a duniya, a gidansa da ke Ingila.
Oleg ya yi wa hukumar leƙen asiri ta Birtaniya MI6 aiki na tsawon shekara 11 yayin da a lokaci guda yake a matsayin ma'aikacin hukumar leƙen asiri ta Tarayyar Soviet (KGB) - inda ya tura wa Burtaniya tarin bayanan sirri.
An yaba masa bisa ƙoƙarin da ya yi na sauya alƙiblar yaƙin cacar baka ta hanyar bayanan sirri da ya riƙa bayarwa -- waɗanda ake ganin sun taimaka wajen kare ɓarkewar yaƙin makamin nukiliya.
An mayar da Gordievsky gida Burtaniya ne a shekarar 1985, lokacin da shugabanninsa a hukumar leƙen asiri ta Tarayyar Soviet suka fara zargin sa, inda aka mayar da shi Birtaniya ta ɓarauniyar hanya.
Yadda ake dafa shinkafar Larabawa 'Kabsa Rice'
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
A filinmu na girke-girken Ramadan na yau, Hannatu Abdulmalik wadda aka fi sani da 'this ray of sunshine', za ta nuna muku yadda ake yin wata shinkafar Larabawa mai suna "Kabsa Rice" da gasassshiyar kaza.
An dawo hotun rabin lokaci: Rwanda 0 - 2 Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
A karawar da ake yi ta neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya tsakanin Rwanda da Najeriya, an dawo hutun rabin lokaci inda Najeriya ke gaba da ƙallaye biyu.
Ɗan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen ne zura ƙwallayen, inda ya zura ƙwallon farko a minti 11 da fara wasa, sannan ya sake zura ƙwallo a ragar Rwanda a minti 45 + 3 da fasa.
Dattawan arewa sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara bakin aiki
Asalin hoton, X/@SimFubara
Ƙungiyar dattawan arewa ta nuna rashin jin daɗinta kan dakatar da gwamnan jihar Rivers da majalisar dokokin jihar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi.
A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Farfesa Abubakar Jika ya fitar, ya yi kira ga Tinubu da ya yi gaggawar mayar da gwamnan da mataimakinsa bakin aikinsu.
Ƙungiyar ta ce duk da cewa sashe na 305 ya ba shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta-ɓaci, "babu hujjar da za ta sa a ayyana dokar a jihar Rivers a yanzu," kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"Dole ne shugaban ƙasa ya lalubo hanyoyin da za a warware matsalar rikicin siyasar jihar Rivers ɗin, sannan ya dakatar da dakatarwar da ya yi gwamnan da mataimakinsa da majalisar dokokin jihar domin tabbatar da wanzumar dimokuraɗiyya da adalci."
Haka kuma ƙungiyar ta yi gargaɗi ga Tinubu da ya sa ido sosai domin tabbatar da ganin rikice-rikicen da ake fama da su a wasu jihohi, "irin Kano da ke fama da matsalar rikicin masarauta ba su rincaɓe ba."
Ku San Malamanku tare da Malama Falmata Umar Abdulkadir
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
A wannan mako cikin shirin Ku San Malamanku, mun kawo muku tattaunawa da Malama Falmata Umar Abdulkadir.
MDD ta ce a shekarar 2024 ce baƙin haure suka fi mutuwa a hanyar fita ƙasashen waje
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar ɗinkin duniya ta ce shekarar 2024 ce shekara mafi muni ta mutuwar baƙin haure a tarihi, inda aƙalla su 9,000 suka mutu a kan hanya a faɗin duniya.
Sai dai hukumar kula da masu gudun hijira ta duniya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar adadin ya zarce hakan saboda wasu mutuwar ko bacewar ba a samun labaran su.
A yanzu haka hukumar ta ce yawancin waɗanda suka mutun ba a gano asalinsu ba, wasu kuma cin zarafi ke ajalinsu, wasu kuma mutuwar Allah da annabi ce.
Hukumar ta ce yadda ake yawan mutuwar na nuna buƙatar da ke akwai ta tabbatar da tsarin tafiya neman mafaka, sannan a tanadi hanyoyin ceto wadanda suka maƙale.
Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta idan ta ɗauki wani mataki kan Iran - Khamenei
Asalin hoton, EPA
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce babu abin da barazanar Amurka za ta yi ma ƙasarsa.
A cikin jawabin da ya gabatar na murnar zagayowar sabuwar shekarar Farisa, ya ce Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta idan har ta ɗauki wani mataki kan Iran.
Ya ce ya kamata Amurka ta sani cewa barazanar da take na yin gaba-da-gaba da Iran ba zai zo mata da sauƙi ba.
Khamenei ya ce dukkansu ya kamata su sani cewa idan suka taƙali Iran to za su gane ba su da wayau.
Tun a farkon wannan watan ne Ayatollah ya yi watsi da takardar da shugaban Amurka ya aika masa ta neman tattaunawa kan shirin Iran din na Nukiliya.
Kotun koli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar PDP
Asalin hoton, PDP
Kotun Kolin Najeriya ta soke
hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta zartas a baya, na dakatar da na hannun damar Nyesom Wike Sanata Samuel
Anyanwu, a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa.
A wani hukunci da alkalan kotun mutum biyar suka yanke da mai shari'a Jamilu Tukur ya gabatar, kotun Kolin ya soki kotun ɗaukaka ƙara da babban Kotun jihar Enugu na shiga abin da ta kira rikicin cikin gida.
Tun a baya babban kotun da ke Enugu ya cire Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar bisa ƙarar da wani ɗan jam'iyyar PDP Mista Aniagu Emmanuel ya shigar.
Hakazalika kotun ɗaukaka ƙara a jihar ta tabbatar da hukuncin babban kotun wanda ya amince da Cif Udeh-Okoye a matsayin wanda ya maye gurbin Sanata Anyanwu a matsayin sakataren Jam'iyya.
Bayan rashin amincewa da hukuncin, Anyanwu ya ɗaukaka ƙarar zuwa kotun ƙoli.
Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun soma rikici kan matsayin sakataren jam'iyyar ne tun bayan da Anyanwu ya bar matsayin domin yin takara a zaɓen gwamnan Imo wanda ya yi rashin nasara.
Bayan rashin nasararsa, ƙoƙarin dawowa kan kujerarsa ya jefa jam'iyyar cikin rikici wanda ya kawo rarrabuwar kai tsakanin ƴan ƙungiyar.
Isra'ila ta ce za ta mamaye wasu sassan Gaza
Asalin hoton, EPA
Ministan tsaron Isra'ila ya yi barazanar mamaye wasu sassa na Gaza na din-din-din idan har Hamas ba ta sako sauran Isra'ilawa da take riƙe da su ba.
Isreal Katz ya ce ya bai wa sojojin umurnin ƙwato ƙarin wasu yankuna tare da fitarda alummar da ke wurin.
Ya ce iya tsawon lokacin da Hamas ta kwashe ba tare da sako waɗanda ake riƙe da su ba, iya ƙarin yankunan da za a ƙara wa Isra'ila.
A yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta, majalisar ɗinkin duniya ta ce wannan ne lokaci mafi tsawo tun da aka soma yaƙin a 2023 da aka ƙi bari a shigar da kayyaykin tallafi yankin.
An rantsar da shugabar ƙasa mace ta farko a Namibia
Asalin hoton, AFP
An rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin shugabar ƙasar Namibia, wadda ta kafa tarihin zama mace ta farko da za ta jagoranci ƙasar.
Tshohuwar ministar harkokin wajen ƙasar ta kasance jajirtaciyyar ƴar jam'iyyar SWAPO wadda ke mulkin Namibia tun bayan samun ƴancin kai daga Afirka ta Kudu a 1990.
Da take magana da BBC, Nandi-Ndaitwah ta yarda da cewa wasu za su iya sukarta saboda jinsinta maimakon ayyukan da take yi - sai dai ta ce za ta ci gaba da yaƙi da cin zarafin jinsi.
Netumbo ta shiga cikin jerin matan Afirka ƙalilan da suka jagoranci ƙasarsu tun lokacin da Liberia ta zaɓi shugabar ƙasa ta mace ta farko shekaru 20 da suka wuce.
Sojojin Sudan sun ƙwato fadar shugaban ƙasa bayan shekara biyu ana fafatawa
Asalin hoton, SUDAN TV
Sojojin Sudan sun ce sun ƙwato fadar shugaban ƙasa da ke Khartoum daga hannun dakarun RSF.
Hotuna da bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, waɗanda kuma BBC ta tabbatar da sahihancinsu, sun nuna sojoji da ke murna suna ɗaga bindigoginsu sama, suna farinciki suna kuma durƙusawa domin yin addua.
Sojojin sun bayyana da ƙarfinsu da ƙwarin gwiwa domin ƙwato ikon babban birnin ƙasar shekara biyu bayan dakarun RSF sun fattatakesu daga ciki.
Abu huɗu daga sabbin takardu kan kisan tsohon shugaban Amurka, John F Kennedy
Asalin hoton, Getty Images
Sabbin takardun bayanai fiye da 2,000 da aka fitar da ke da alaƙa da bincike kan kisan gilla da aka yi wa Shugaba John F Kennedy sun yi fice ne ba wai kawai saboda bayanan da ke ƙunshe a cikinsu ba, har saboda bayanan da aka cire.
Kamar yadda ƙwararru suka yi hasashe, sabbin takardun bayanan da gwamnatin Trump ta saki ba su amsa dukkanin tambayoyin da ake da su ba kan wani babban lokaci mai cike da tarihi a Amurka wato kisan Kennedy a Dallas a shekarar 1963.
Sai dai a wannan karon, an haɗa da takardun da ba a ɓoye komai ba ko kuma ba a boye abubuwa sosai ba - an sanya takardun ainihi maimakon waɗanda aka kulle wasu wurare ko kuma aka bar wasu wuraren babu komai.
Wani binciken gwamnatin Amurka ya nuna cewa Lee Harvey Oswald, wani mai yawace-yawace kuma tsohon sojan ruwa a Amurka wanda a wani lokaci ya kuma tarayyar Soviet, shi kaɗai ya yi aikin a lokacin da ya harbi jerin motocin Kennedy daga wani gini da ke kusa. Latsa nan domin karanta cikakken labarin <<<<Cigaban Labari>>>>>>
Ana neman gudummawar jini 'da gaggawa' don ceto mutanen da hatsarin Abuja ya raunata
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da tattara jini ta Najeriya ta nemi 'yan ƙasar musamman mazauna birnin Abuja su bayar da gudummawar jini domin tallafa wa mutanen da hatsarin babbar mota ya ritsa da su a babbar hanyar zuwa Keffi da ke birnin.
Lamarin ya auku ne bayan wata babbar motar Dangote ta kama da wuta tare da aukawa kan motocin da ke gefen titi a ranar Laraba.
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum shida, wasu 25 sun ji raunuka inda suke jinya a asibitoci daban-daban.
"Hatsarin mai muni ya ritsa da mutane da dama, waɗanda ke buƙatar ƙarin jini da gaggawa," kamar yadda National Blood Service Agency (NBSA) ta bayyana a shafinta na dandalin X.
"Asibitoci da jami'an kiwon lafiyar gaggawa na aiki ba dare ba rana domin ceto rayuka amma kuma samun isasshen jini na da muhimmanci ga aikin nasu."
Ta nemi "dukkan waɗanda suka cancanci bayar da gudummawar jini su ziyarci wuraren bayar da jinin da ke faɗin Abuja", ko kuma a tuntuɓi ofishinta da ke lamba 39 Abidjan Street, Zone Wuse, ko kuma ta lambar waya 07088370905.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Majalisar zartawar Isra'ila ta kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.
Matakin zai ƙara harzuƙa yan kasar da suka kwashe kwanaki uku suna zanga-zangar nuna adawa da matakin Firaminista Benjamin Netanyahu na korar shugaban hukumar leken asiri Ronen Bar.
Mutanen biyu dai sun samu saɓani ne tun bayan harin da Hamas ta kai a watan Oktoban 2023, inda suke zargin juna da gazawa.
Akwai bincike da Shin Bet ke gudanarwa kan ikirarin cewa wasu makarabban firaministan sun yi ta neman alfarma a madadin ƙasar Qatar.
Kotu ta ɗage shari'ar Nnamdi Kanu bayan cigaba da zama a yau Juma'a
Asalin hoton, Reuters
Jagoran haramtacciyar ƙungiyar 'yan'aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB) ya sake bayyana a gaban babbar kotun tarayya yau Juma'a a Abuja babban birnin Najeriya.
Sai dai ɗaya daga cikin lauyoyinsa Aloy Ejimakor ya ce kotun ƙarƙashin Mai Shari'a James Kolawole ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 29 ga watan Afrilu da kuma 2 da 6 ga watan Mayu na 2025.
Ci gaba da shari'ar ta Nnamdi Kanu na zuwa ne bayan Alƙaliyar Alƙalai Kudirat Kekere-Ekunnyefere ta saka Mai Shari'a James Kolawole Omotoshi a matsayin sabon alƙalin da zai saurari shari'ar bayan Kanu ya yi ƙorafi kan Mai Shari'a Binta Nyako.
An yi hasashen za a yi bitar tuhuma bakwai da gwamatin Najeriya ke yi wa Kanu yayin ci gaba da shari'ar, waɗanda suka jiɓanci tayar da fitina da kuma ta'addanci.
A watan Disamban 2023 ne Kotun Ƙoli ta umarci Kanu ya koma babbar kotun ta tarayya domin kare tuhumar da ake yi masa bayan Binta Nyako ta yi watsi da takwas cikin 15 da gwamnati ta gabatar a 2021.
Gwamnatin Najeriya ta kai Kanu kotu ne bayan kama shi a wata ƙasar waje a 2021, kuma har yanzu mambobin ƙungiyarsa da gwamnati ta haramta na ci gaba da neman ɓallewa daga Najeiriya domin kafa ƙasar Biafra.
Kwankwaso ya caccaki Tinubu kan saka dokar ta-ɓaci a jihar Rivers
Asalin hoton, X/Rabiu Kwankwaso
Jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Shugaban Ƙasa Bola Tinubu game da dokar ta-ɓaci da ya saka a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.
CIkin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis da dare, Kwankwaso ya siffanta matakin na Tinubu "mai haɗari ga dimokuɗiyya".
A ranar Juma'a ne Tinubu ya sanya dokar da ta dakatar da Gwamna Fubara, da majalisar dokokin jihar tare da maye gurbin gwamnan da kantoman riƙo saboda abin da ya kira "rashin doka da oda" sakamakon rikicin siyasa tsakanin Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.
"Ina ganin rikicin siyasar da ake ciki a Rivers bai isa ya sa a ayyana sashe na 305(1) na kundin tsarin mulki ba," in ji shi.
"Abin da ya fi damu na ma shi ne yadda majalisun dokokin ƙasa suka amince da buƙatar shugaban ƙasa. Na yi fatan ba za su yarda da wannan abu da ya karya doka ba...Wannan mataki nasu zai kawo wa dimokuraɗiyyarmu cikas."
Rashin lantarki ya tilasta rufe babban filin jirgin sama na Landan
Asalin hoton, Reuters
An rufe Heathrow da ke yammacin London - tashar jirgin sama mafi cunkuso a nahiyar Turai - sakamakon gobara da aka samu a kusa da cibiyar lantarki da ke kusa da filin jirgin saman.
Filin jirgin zai kasance a rufe har zuwa 12:00 na dare a yau Juma'a saboda matsalar lantarkin.
Wakilin BBC ya ce babu wata sanarwa kan lokacin da za a iya dawo da lantarkin a Heathrow kuma filin jirgin ba shi da wani zaɓi illa daukar matakin rufewa domin kare lafiyar fasinjoji da ma'aikatansa.
A bara fasinja miliyan 83 ne suka bi ta filin jirgin saman na Heathrow.