window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 14/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Badamasi Abdulƙadir Mukhtar

  1. Rufewa

    Masu bin wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labaran.

    Sai kuma gobe idan mai duka ya kai mu.

    Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya

  2. Ma’aikatan jam’iyyar PDP sun goyi bayan mataimakin sakataren jam'iyyar

    Ma'aikatan PDP

    Asalin hoton, @OfficialPDPNig

    Ma’aikatan jam’iyyar PDP na ƙasa sun fito fili sun bayyana goyon bayansu ga mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa Akitek Setonji Koshoedo a matsayin sabon sakataren jam’iyyar.

    Ma’aikatan sun ce sun dauki wannan matakin ne domin kawo karshen rikice-rikicen da jam’iyyar ta kwashe fiye da shekara biyu tana fama da su, tun bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar dakatar da tsige Sanata Samuel Anyanwu daga mukamin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

    A yanzu dai ma’aikatan jam’iyyar ta PDP sun fito fili suna bayyana damuwa akan wadannan rikice-rikicen inda suke neman har yanzu dai shi Sanata Nyawu ya haƙura ya bai wa mataimakinsa, Arch Setonji Koshoedo wannan matsayi.

    Ma'aikatan sun ce wannan ita ce hanya guda ɗaya kawai da suke jin za ta ɗinke ɓarakar da ake samu a jam’iyyar.

    Alhaji Gurama Bawa daraktan sashen ma’aikatan jam’iyyar PDP na ƙasa, ya shaida wa BBC ce sun shiga halin rarrabuwar kai ne tun daga lokacin da aka fara turka-turkar makomar wanda zai zama sakataren jam’iyyar na ƙasa

    Ya ƙara da cewa sun nemi tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki da ya jagoranci zaman sasantawa tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

    Kimanin ma’aikatan jam’iyyar PDP 83 ne suka soma sanya hannu kan takardar amincewa da wannan buƙata, inda suka jaddada goyon bayansu ga matsayar kwamitin amintattun jam’iyyar na ƙasa da ma gwamnonin jam’iyyar waɗanda tun da farko suka bayyana irin wannan muradi.

    Wannan na faruwa daidai lokacin da ake samun wasu jiga-jigan jam’iyyar ta PDP na ci gaba da ficewa zuwa APC mai mulki.

    A ranar Talata ma ƴan majalisar dattawa uku na jam’iyyar daga jihar Kebbi sun sauya sheka zuwa PDP baya ga gwamnan jihar Delta da ‘yan majalisarsa da suka koma APC a watan jiya.

    Wani abu da masu sharhi ke ganin rashin gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa tare da yin zaɓen sabbin shugabanninta na daga cikin manyan matsalolin da ke ci gaba da haifar da dambarwa a cikin PDP

  3. Zelensky na jiran wakilan Rasha a tattaunawar zaman lafiya da za a yi a Turkiyya

    Shugaban Ukraine Vlodymyr Zelensky, ya ce yana dakon Rashawan da za su halarci tattaunawar da za a yi a Turkiyya kafin ya yanke hukuncin matakin da ƙasarsa za ta ɗauka.

    Har yanzu ba a sani ba ko shugaban Rasha, Vladimir Putin zai halarci tattaunawar da aka tsara yi a gobe Alhamis ba.

    Mista Zelensky ya nuna alamun halartar tattaunawar, to amma koda ya je zai gana ne da wakilan Rasha idan har Mista Putin ya je wajen.

    Ukraine da ƙawayenta na ci gaba da matsa wa Rasha ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana 30 abin da Rashan ba ta ce komai ba akai.

  4. Kotun Mauritania ta tsawaita hukuncin ɗauri ga tsohon shugaban ƙasar zuwa shekara 15

    Shugaba

    Asalin hoton, AFP

    Kotun ɗaukaka ƙara a Mauritania ta tsawaita hukuncin ɗaurin da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Ould Abdel Aziz zuwa shekara 15 a gidan yari, saboda laifin ɓarnatar da dukiya da amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida ba.

    Abdel Aziz, wanda ya jagoranci ƙasar da ke yammacin Afirka daga 2009 zuwal 2019, ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin shekara biyar da aka yanke masa bayan samunsa da laifin ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnati da amfani da matsayi ba bisa ƙa'ida ba wajen arzurta kansa.

    Masu shigar da ƙara sun ce tsohon shugaban ya mallaki dukiya da kadarorin da suka kai darajar dala miliyan 70 a lokacin da yake kan karagar mulkin kasar.

    Yayin yanke hukuncin a ranar Laraba, kotun ta yi watsi da ƙarar da ya ɗakaka.

    Mista Aziz ya yi zargin cewa tuhumar da ake yi masa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne.

  5. Trump ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi masu maiƙo da Qatar

    Trump da sarkin Qatar

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Fadar gwamnatin Qatar ta shirya wa shugaban Amurka, Donald Trump ƙayatacciyar liyafar girmamawa.

    Donald Trump ya sanya hannu a kan jerin wasu yarjejeniyoyi da Qatar a yayin da ya ke ci gaba neman harkokin zuba jari masu maiƙo a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Yayin da ya ke zaune tare da sarki Qatar a Doha, shugaban na Amurka yarjejeniyoyin sun haɗa da ta dala biliyan 200 don sayan jiragen sama na kamfanin Boeing.

    Trump da sarkin Qatar

    Asalin hoton, Reuters

    Mista Trump na fuskantar suka saboda shirin karɓar kyautar jirgin saman ƙasaita da Qatar ta yi masa.

    Tun da farko ya gana da sabon shugaban Syria Ahmed al Sharaa a Riyadh inda ya buƙace shi ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun daidaita da Isra'ila.

    Trump da sarkin Qatar

    Asalin hoton, Reuters

    Trump da sarkin Qatar

    Asalin hoton, Reuters

  6. MDD ta ce kimanin marasa lafiya 1,000 na fuskantar ƙarancin ruwan sha a Darfur

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa kimanin marasa lafiya 1,000 ne ke fuskantar ƙarancin ruwan sha a yankin Darfur bayan da wani makamin atilari ya lalata tankar ruwan asibitin da suke kwance.

    An girke motar UNICEF a ɗaya daga cikin asbitocin da ke aiki a birnin El-Fasher na yammacin Darfur.

    Yaƙin basasar kasar da a yanzu ya shiga shekara na uku, haifar da tarin matsalolin jin kai a ƙasar.

    El-Fasher na ɗaya daga cikin yankunan Darfur da ba ya hannun mayaƙan RSF, amma kuma mayaƙan sun yi masa ƙawanya.

  7. ISWAP ta ɗauki alhakin harin Marte

    mayaƙa

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin babban hari kan sansanin sojin Najeriya da ke garin Marte a jihar Borno.

    Cikin wani sako da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram ta ce mayaƙanta sun far wa sansanin sojin gabanin asubahin ranar Litinin.

    Tana mai cewa mayaƙan nata sun yi arangama da sojojin har na tsawon sa'a guda, kafin su yi nasarar ƙwace sansanin, tare da kashe sojoji masu yawa lamarin da ta ce ya ''tilasta wa wasu tserewa''.

    Harin shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da mayaƙan suka kai garuruwan Marte da Dikwa da kuma Rann da kuma Gajiram, inda aka rasa rayukan da ba a kai ga ƙiyasta su da asarar dukiyoyi masu yawa tare da sace makamai.

  8. JAMB ta saka ranar sake jarrabawa a wasu cibiyoyin

    ..

    Asalin hoton, JAMB

    Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, Jamb ta amince da saka sabuwar ranar sake jarrabawar UTME ga wasu ɗaliban da suka yi jarrabawar a wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar.

    A wani taron manema labarai da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya gabatar a Abuja, babban binrin ƙasar ya ce hukumar ta amince da matsalolin da aka samu a jarrabawar UTME ta 2025,

    Ya ƙara da cewa ɗalibai 206.610 ne za su sake jarrabawar a cibiyoyi 65 a Legas, yayin da a Owerri ɗalibai 173,387 za su sake jarrabawar a cibiyoyi 92.

    Za a fara sake jarrabawar daga ranar 16 ga watan Mayu, inda za a aike da saƙon waya ga ɗaliban da lamarin ya shafa.

    Shugaban hukumar ya kuma nemi afuwar ɗaliban kan matsaloli da aka fuskanta a lokacin jarrabawar.

    “Na ɗauki alhakin duk abin da ya faru, kuma ina bayar da haƙuri ga ɗaliban da lamarin ya shafa'', in ji Farfesa Oyodele.

    Farfesa Oloyode ya ce matsalar na'ura da aka samu a wasu santocin jihohin Legas da Owerri sun haifar da ƙorafe-ƙorafe daga wasu ɗaliban, inda hukumar ta gano matsalar bayar fitowar sakamakon jarrabawar.

    “Matsalar ta samo asali ne daga ɗaya daga cikin kamfanonin da ke bai wa hukumarsu sadarwar, wanda jami'ansa suka kasa magance matsalar ta yadda hakan ya shafi wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar,'' in ji shugaban hukumar.

  9. Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Tripoli

    Mayaƙa

    Asalin hoton, Reuters

    An ci gaba da gwabza faɗa a Tripoli, babban birnin Libya kwanaki bayan arangama tsakanin wasu ƙungiyoyi masu gaba da juna.

    Rikicin - wanda aka bayyana da mafi muni cikin shekaru - ya ɓarke a ranar Litinin bayan kisan wani fitaccen jagoran masu tayar da ƙayar baya a wani kwanton ɓauna da mayaƙan wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai.

    Daga nan ne ake ta samun arangama a Tripoli, yayin da hukumomi suka buƙaci mazauna birnin su zauna a gidajensu.

    Ƙungiyar Ƙasashen Yankin Larabawa ta 'Arab League' ta bayyana damuwarta kan faɗan, wanda ta ce yana barazana ga rayukan fararen hula a mazauna birnin.

    Tuni Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Kasashen Larabawan suka yi kira a kwantar da rikicin a fadin birnin.

  10. Birtaniya ta yaba wa Tinubu kan tsare-tsaren tattalin arziƙi

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Bayanan hoto, Tun bayan hawansa mulki Shugaban Tinubu ya sanar da ɓullo da sabbin tsare-tsaren ingantan tattalin arzikin Najeriya

    Gwamnatin Birtaniya ta ce matakan da shugaban Najeriya bola Ahmed Tinubu ke ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar kwalliya na biyan kuɗin sabulu.

    Birtaniyan ta ce matakan da aka ɗauka musamman wajen farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, da na kuɗin shiga na daga cikin dalilan da suka aka samu ƙaruwar damar zuba jari a ƙasar.

    Jakadan Birtaniya a Najeriya Dr. Richard Montgomery ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin Najeirya da Birtaniya, ta fuskar kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, da ya gudana a Abuja babban birnin na Najeriya.

    Gwamnatin Birtaniyar ta ce la’akari da rahoton da Bankin Duniya a baya-bayan nan kan harkokin zuba jari a Najeriya ya nuna cewar darajar kuɗin ƙasar naira na farfaɗowa.

    Haka kuma rahoton ya ce ana samun ƙaruwar kuɗaɗe a asusun ƙasashen wajen na ƙasar da kuma na haraji, lamarin da ya sa ake samun buƙatar ƙara faɗaɗa harkokin zuba jari a ƙasar.

    Birtaniyan ta ce shirin bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu da suke haɗin gwiwa za a cimma shi ne idan Najeriya ta mayar da hankali kan wajen samar da daidaitacen tsari da zai haɓaka harkokin kasuwanci da janyo hankulan masu zuba jari a ƙasar.

    Sai dai ya ce ganin irin matakan da shugaban Najeriya ya ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar, yasa suka fitar da wasu ɓanagarori takwas da zasu haɗa gwiwa da Najeriya wajen ganin ta haɓaka kasuwacin da yawan masu zuba jari a ƙasar.

    Haka kuma Jakadan Birtaniyar ya ce baiwa kamfanonin ƙasar irin na su Ɗangote suka fara tace man fetur yasa an samu raguwar fitar da ɗanyen man fetur zuwa ƙasashen waje.

  11. Isra'ila ta kashe mutane 48 a arewacin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Hare-haren sama da Isra'ila ta kai arewacin Gaza da tsakar dare sun kashe Falasɗinawa aƙalla 48.

    Wani asibitin Indonesia a yankin ya ce daga cikin waɗanda aka kashen akwai ƙananan yara 22 da kuma mata 15, a garin Jabalia da kuma wasu sansanonin ƴab gudun hijira.

    Wani bidiyon da aka yaɗa ya nuna gomman gawawwaki a ƙasa.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazari a kan rahoton hare-haren nata.

    Dama dai ta gargaɗi mutanen da ke zaune a Jabalia da ƙauyukan da ke kusa da shi, su fice kafin ranar Talata bayan wata wata ƙungiyar Falasɗinawa ta ƙaddamar da harin roka a kan Isra'ila.

    Wannan na zuwa ne yayin da hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kwamitin tsaro na majalisar ya ɗauki matakin kawo ƙarshen kisan gilla a Gaza.

  12. Gwamnatin sojin Mali ta rushe jam'iyyun siyasa

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin mulkin sojin Mali ta rushe dukkan jam'iyyun siyasar ƙasar, yayin da ake ci gaba da zaman fargaba game da siyasar ƙasar tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki.

    Sanarwar da gwamnatin sojin ta fittar a talabijin ta ce ''An haramta dukkan ayyukan jam'iyyu da kuma ƙungiyoyin siyasa a faɗin ƙasar.'

    Shugaban ƙasar Assimi Goïta, wanda ya amince da rushe jam'iyyun, ya ƙwace mulki ne bayan juyin mulki kuma ya sha alwashin ci gaba da mulki har na shekara biyar kafin gudanar da zaɓe.

    Ana ganin cewa matakin zai janyo sabon bore daga jam'iyyun siyasar waɗanda ke ta neman a koma turbar dimokuraɗiyya.

    Tun a shekarar da ta gabata gwamnatin sojin ƙasar ke zartar da matakan da suke neman murƙushe ayyukan siyasa.

    A makon jiya wasu ɗauke da makamai suka yi garkuwa da jagororin adawar ƙasar biyu, bayan wata zanga-zanga.

    Hukumomi ba su ce komai ba game da kama ƴan siyasar.

  13. An yi gargaɗi kan yawaitar mutuwar leburori a Saudiyya

    Saudi

    Asalin hoton, NurPhoto/Getty

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun yi gargaɗi kan ƙaruwar mutuwar leburori baƙi masu aiki a Saudiyya, yayin da ƙasar ke shirya karɓar baƙuncin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya ta 2034.

    Human Rights Watch da takwararta ta FairSquare sun ce yanzu haka leburori na mutuwa a wuraren da ake aikin gine-gine a ƙasar, kuma suna mutuwa ne a yanyin da za a iya kauce mawa.

    Rahoton da ƙungiyoyin suka fitar a yau Laraba ya ce mafi yawan lokuta ana sanya irin wannan mutuwar leburorin ne a jerin mutuwar da ta faru sakamakon hatsari, kuma ba a biyan diyya ga iyalan mamatan.

    Dukkan ƙungiyoyin sun buƙaci hukumomin Saudiyya su tabbata sun ɗauki matakan bayar da kariya ga lafiyar ɗimbin ma'aitaka leburori da ke kwarara ƙasar domin irin waɗannan gine-gine na shirya wa gasar cin kofin duniyan.

    Human Rights Watch ta ce "Gasar cin kofin duniya ta 2034 da za a yi a Saudiyya ita ce mafi girma da tsada a tarihi, amma idan aka yi sake za ta zamo wadda aka fi tafka asarar rai kafin shirya ta, idan aka yi la'akari da miliyoyin leburori ƴan ƙasashen waje da ke tururuwa cikin ƙasar domin yin aiki a wuraren gine-gine da ake yi da suka haɗa da sabbin filayen wasa 11 da layukan dogo da kuma otel-otel.''

    Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan ziyarar da shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino, ya kai Saudiyya tare da shugaban Amurka Donald Trump.

  14. Ba za mu bari PDP ta nutse da mu ba - Sanatocin Kebbi

    Sanata Adamu Aliero a lokacin da ya kai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu ziyara a makon da ya gabata

    Asalin hoton, STATE HOUSE NG

    Bayanan hoto, Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi a lokacin da ya kai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu ziyara a makon da ya gabata

    Sanatocin Najeriya uku da suka fito daga jihar Kebbi, waɗanda suka sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki sun ce sun fita daga jam'iyyar ce sanadiyyar rikice-rikice na cikin gida.

    A jiya Talata ne shugabancin majalisar dattajai ya tabbatar da sauya shekar sanatocin wato Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya da Yahaya Abdullahi mai wakilartar Kebbi arewa da kuma Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta kudu.

    Sanatocin sun ce sun fice daga jam'iyyar ne saboda rikice rikicen cikin gida da suka yi wa jam'iyyar PDP katutu.

    Daya daga cikinsu, Sanata Yahaya Abdullahi ya shaida wa BBC cewa a bayyane take tun bayan zaɓen 2023, jam'iyyar PDP ta shiga ruɗani da rikici kala-kala, kuma har kawo yanzu babu alamun jam'iyyar tana ɗaukar matakin gyara matsalolin nata.

    Ya ce ''Kowa ya san dai abubuwan da suka addabi PDP, tana son ta wargaje. Ba kuwa wanda ke son ya shigo mu'amula da jama'a sai ka ga waɗanda ka zo kana son ka zauna da su kana tsammanin za a haɗa kai a ceto al'umma a gyara ƙasa, sai kansu duk ya rarrabu, abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa kullum sai ƙara lalacewa ya ke.''

    Ya yi bayanin cewa ai dama can da su aka kafa APC amma sun fice daga cikin ta ne saboda gwamnan su na wancan lokacin ya nuna baya yi da su, kuma sai PDP ta janye su, amma a yanzu yanayin ya canza domin kuwa asalin ƴan PDP su gaza ɗinke ɓarakar su ta cikin gida kuma ga shi a ''shugaban ƙasa Tinubu ya san amfanin mu, kuma shi sabon gwamna Dr Nasiru Idris Kauran Gwandu ƙaninmu ne, ya bamu girma ya bamu mutumcin mu, don haka irin wannan a kan me za mu zauna muna jayayya da shi.''

    Sanata Yahaya Abdullahi ya kuma musanta cewa akwai alƙawarin da shugaba Tinuu ya yi masu, wanda ya sa suka sauya sheka zuwa APC inda ya ce shi a yanzu babu abin da bai gani ba a rayuwa domin haka ya wuce a yi mashi alƙawari kafin sauya sheƙa.

  15. An yi musayar fursunoni tsakanin India da Pakistan

    INDIA/PAKISTAN

    Asalin hoton, Getty Images

    India da Pakistan sun yi musayar fursunoni, kwanaki huɗu bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

    India ta miƙa wa Pakistan wani sojanta da ta kama a farkon watan nan.

    Itama Pakistan ta saki wani jami'in sojin India mai tsaron kan iyaka, wanda ya tsallaka yankin Punjab makonni uku da suka wuce.

    India ta ce sojan nata ya tsallaka yankin Pakistan ne a ranar 23 ga watan Afirelu, kwana ɗaya kafin harin da ya kashe mutane 25 a yankin Kashmir.

    Harin ne kuma ya sa India ta ƙaddamar da nata na ramuwa a kan wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga a ɓangaren da Pakistan ke iko da shi a yankin Kashmir.

    Ƙasashen biyu sun yi musayar makaman roka kan junan su, kafin daga baya suka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

  16. Yansandan Najeriya su musanta zargin kai wa ƴanbindiga abinci da jirgin sama

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa cewa jirgin sama mai saukar ungulu mallakinta yana kai wa ƴanbindiga abinci a dajin jihar Kogi.

    Rundunar ta ce labarin ƙanzon kurege ne da baya da tushe bare makama.

    Kakakin rundunar, A Olumuyiwa Adejobi, ya ce bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na wani aiki ne da jami'an rundunar suka yi a yankin Obajana na jihar Kogi, kuma an cika duk wata ƙa'ida kafin ƙaddamar da aikin.

    Sanarwar da A Adejobi ya fitar ta ce “Ba kamar yadda ake yaɗa labarin ƙanzon kurege ba cewa jirgin saman mu yana kai wa ƴanbindiga abinci a cikin daji, bidiyon na wani aikin haɗin gwiwa ne tsakanin ƴansanda da ƴanbanga da mafarauta.''

    Rundunar ta ce ta gudanar da aikin ne a ranar Asabar 10 ga watan Mayun 2025 a jihar Kogi.

    Ta kuma yi bayanin cewa an shigar da jirgin sama mai saukar ungulun ne a cikin aikin domin tallafawa jami'an rundunar da takwarorin su a aikin su na fatattakar ƴanbindiga.

    Rundunar ƴansandan Najeriyan ta yi Allah wadai da masu yaɗa wannan labaran ƙanzon kurege, tare da jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da aikin ta a cikin ƙwarewa da bin doka.

  17. Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya

    Majalisa

    Asalin hoton, Others

    Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka mai neman tabbatar da tsarin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya.

    Wannan na daga cikin aikin da majalisar ke yi na gyaran wasu sassa shida na kundin mulkin ƙasar, waɗanda a baya suka gaza tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.

    Zaman majalisar na ranar Talata wanda shugabanta Abbas Tajudeen ya jagoranta ya yi muhawara a kan ƙudirin sannan ya cimma matsayar yin watsi dashi kamar yadda ya yi wa sauran ƙudirorin da aka gabatar da su tare.

    Sai dai ana sa ran batun zai ƙara tasowa a zaman majalisar wakilan na yau Laraba domin sake tafka muhawa da ɗaukar matsaya a kai.

    Wasu daga cikin ƴan majalisar da suka yi muhawara a kan ƙudirin sun ce a yanzu haka jam'iyyun siyasar Najeriya suna da irin nasu tanadi na tantance karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya, kuma akwai hukumar tabbatar da daidaito, wadda ke aikin da ake neman ƙudirin ya yi.

  18. Brazil za ta ƙarfafa kasuwanci da China

    Shugaban Brazil ya ce yana fatan bunkasa huldar diflomasiya da kasuwanci da kasar China, yayin da yake ci gaba da ziyarar aiki a birnin Beijing.

    A wani taron manema labarai, Luiz Inacio Lula da Silva ya ce baya shakkar ramuwar gayya daga Washington.

    Gwamnatin Trump ta yi ta kokarin yin fancale, ga aniyar China ta karfafa tasirin ta a yankin kudancin Amurka.

    Jiya Talata ne shugaban Chinan Xi Jinping ya shaidawa taron shugabannin kasashen yankin cewa lokacin hada kai ya yi, domin tunkarar masu son yi wa duniya karfa karfa a fannin kasuwanci, wani shagube da ake ganin ya yi wa Amurka.

  19. Boko Haram ta kashe sojoji huɗu a wani sabon hari a Borno

    NA

    Asalin hoton, AFP

    Mayaƙan IS sun ƙara kai wa sojojin Najeriya hari, karo na biyu a cikin kwanaki biyu.

    Rundunar sojin Najeriya ta ce maharan sun kashe dakarunta huɗu a wani sansanin su da ke kusa da garin Rann da ke kan iyakar ƙasar da Kamaru a ihar Borno.

    A ranar Litinin ma IS ta kai hari a wani sansanin soji da ke yammacin Borno, a garin Marte, inda aka bayar da rahoton kisan sojojin Najeriya da dama.

    Masu sharhi sun ce a baya bayan nan mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun canza salon kai hare-hare, ciki harda amfani da jirgin sama marar matuƙi.

  20. An sassauta yaƙin kasuwaci tsakanin Amurka da China

    US-CHINA

    Asalin hoton, Getty Images

    Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da China domin sassauta yakin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ta fara aiki.

    Hukumar shige da fice ta China ta sanar da fara aiki da yarjejeniyar da aka cimma da masu shiga Tsakani, Switzerland a karshen makon da ya gabata.

    Amurka ma ta fara aiwatar da yarjejeniyar.

    Wannan ne karon farko da bangarorin biyu, suka amince su yayyafawa zukata ruwa bayan shafe watanni suna ja in ja, kuma dukkan bangarorin biyu sun amince su zaftare kashi 115 na harajin da suka laftawa junansu.

    Yarjejeniyar ta kwanaki casa'in za ta ba da damar tattaunawa don cimma yarjejeniya ta ka'in da na'in.