Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Talata.
Mu kwana lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/01/2025.
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Talata.
Mu kwana lafiya.
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce mambobin rundunar tsaro ta RSF da mayaƙan ƙawayenta suna aiwatar da kisan ƙare dangi a Sudan.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ya danganta haka ne akan kisan gilla mai nasaba da ƙabilancin da aka yi wa maza da yara maza da kuma mata da aka ci zarafinsu a yankin Darfur.
Ya ce a yanzu Amurka ta sanya takunkumi ga shugaban jagoran rundunar ta RSF,Mohammad Hamdan Dagalo Musa da wasu kamfanoni bakwai na RSF ɗin game da rawar da suka taka a kisan ƙare dangin.
Wakiliyar BBC ta ce Mista Blinken ya ce wannan ba wai yana nufin cewa yana goyon bayan sojojin ƙasar Sudan ba ne.
A cewarsa rundunar RSF da sojojin ƙasar ba su cancanci su mulki alummar ƙasar Sudan ba
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa tsohon kocin tawagar Mali, Éric Chelle, a matsayin kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles.
Chelle mai shekara 47 ya jagoranci Mali har zuwa zagayen kwata fayinal a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 a Ivory Coast, kafin mai masaukin baƙi ta doke su.
NFF ta ce ta amince da naɗin nasa ne bayan kwamatinta na musamman ya bayar da shawarar yin hakan a yau Talata.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan NFF ta kasa daidaitawa da Bruno Labbadia ɗan ƙasar Jamus game da batun biyan haraji bayan sanar da ba shi aikin a watan Agustan 2024.
Kafin naɗin nasa, shugaban NFF Ibrahim Musa Gusa ya faɗa wa manema labarai cewa sabon kocin da za su bai wa aikin shi ne zai jagoranci tawagar Super Eagles ta 'yanwasan cikin gida zuwa gasar kofin Afirka ta CHAN - wadda ake gudanar da wasannin neman gurbi a yanzu.
Asalin hoton, Reuters
Masu aikin ceto a yankin Tibet na kasar China na ci gaba da neman masu sauran numfashi a mumunar girgizar ƙasa da ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 126.
Girgizar kasar ta kuma lalata gine-gine fiye da 2,000 kuma ana nuna damuwa kan wadanda suka rasa matsugunasu, yayin da ake fama da matsanancin sanyi.
Kafar yada labarai ta gwamnati ta ce gidaje da dama sun ruguje a kauyukan da ke tsaunuka kusa da garin Shigatse mai muhimanci ga mabiya adinin Buda.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya haɗu da fuskokin da ya daɗe da sani a gida wajen ƙasar a wurin bikin rantsar da sabon Shugaban Ƙasar Ghana John Mahama.
Tsofaffin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan na cikin mutanen da ya yi musabaha da su a wurin bikin.
Kazalika, ya haɗu da shugaban Ghana da ya bar gado, Nana Akupo-Addo a birnin Accra a yau Litinin.
"Ba ni da wata tantama gwamnatin John Mahama za ta kawo sauyi mai albarka," in Tinubu yayin jawabinsa a wurin biki.
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Asalin hoton, EPA
Mutum 600 ne suka isa garin Dirkou jihar Agadez.ta Nijar bayan mahukunta sun koro su daga ƙasar Libya.
Hukumomin Dirkou ne da abokan hulɗarsu na hukumar Majalisa Ɗinkin Duniya da ke kula da baƙin haure suka tarbe su.
Da yawansu sun yi zaman gidan yari na tsawon watanni a Libya ba tare da shari'a ba.
"Watana biyar a gidan kaso kafin a kawo mu Nijar," in ji wani daga cikinsu. Wani ma ya ce: "Mun sha wahala sosai. Ƙuraje sun fito min, mun sha wahala sosai."
A ranar 1 ga watan Janairu ma bakin haure kimanin 770 ne suka isa Nijar din.
Mutanen da suka yi ta aika saƙonnin neman taimako saboda mawuyacin halin da suka fada a gidan yarin Gatrone da dama sun koma gida ɗauke da larura, yayin da mutum ɗaya ya rasu.
Jimillar 'yan Nijar 1,300 ne suka isa ƙasar bayan koro su daga Libya, a cewar wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou.
Wani jami'in barikin da ya karɓi mutanen, Abare Abba Gana, ya ce dukka mutanen maza ne.
Asalin hoton, Getty Images
Wakili na musaman na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Afghanistan ya nuna damuwa kan rahotannin kame da korar da ake yi wa ƴan Afghanistan a ƙasar Pakistan.
Richard Bennett ya ce ya kamata a ba ƴan Afganistan da ke yankin kulawar da ta kamata.
Tun farko ofishin jakadancin Afghanistan da ke Islamabad ya ce an tsare ƴan Afgahnistan kusan ɗari takwas a babban birnin ƙasar ciki har da waɗanda suka yi rajista da hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Gwamnatin Pakistan ta ce ta ƙaddamar da shirin korar ƴan Afghanistan da ba a yi wa rajista ba.
Yan Afghanistan fiye da dubu ɗari bakwai ne aka tilastawa komawa ƙasarsu a cikin shekara guda.
Asalin hoton, Reuters
Sabon Shugaban Ghana John Mahama ya yi alƙawarin yaƙi da cin hanci da kuma ƙirƙirar ayyukan yi ga matasa yayin jawabinsa na shan rantsuwar kama aiki.
Da tsakar ranar yau aka rantsar da John Mahama a birnin Accra yayin wani biki, inda aka rantsar da mace ta farko Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Jane Naana Opoku Agyemang.
Akwai shugabannin ƙasa da dama da suka halarci taron, ciki har da Bola Tinubu na Najeriya, da shugabannin mulkin soja uku na Afirka.
Wa'adin mulkn Mahama na biyu ba zai kasance mai sauƙi ba saboda halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, wanda ya jawo karɓar bashin dala biliyan uku daga asusun lamuni na IMF.
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yansandan Najeriya ta sanar da cewa ta kama mutum 751 da take zargi da aikata laifukan zamba ta intanet a 2024.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, shi ne ya bayyana alƙaluman, inda ya ce sun yi sa'ar hukuncin kotu da ya ɗaure 14 daga cikinsu.
Ya ƙara da cewa akwai lamurra 508 da suke ci gaba da aiki a kansu zuwa yanzu.
Adejobi ya kuma bayyana cewa sun ƙwato jimillar kuɗi dala 840, 000 na mutanen da aka damfara, yayin da aka riƙe jimillar naira miliyan N914 da wasu dala 115,000 a asusun bankuna daban-daban, ciki har da na crypto.
Haka nan, rundunar ta yi nasarar ƙwato ababen hawa 26, da gidaje 16, da filaye 39, in ji Mista Adejobi.
Asalin hoton, OTHERS
Yarinyar nan mai shekara 14 da ƴansanda suka tuhuma da kashe abokin mijinta bayan zuba musu guba a abinci a jihar Jigawa ta amsa laifinta a gaban alƙali
Al'amarin dai ya faru ne a ranar Lahadin 15 ga watan Disambar 2024 a ƙauyen Bakata da ke ƙaramar hukumar Kiyawan jihar Jigawa.
Yarinyar dai ta saka wa mijinta da abokansa guba a taliya, kuma nan da nan suka fita daga hayyacinsu, inda aka kai su asibitin garin Jahun inda a nan ne ɗaya daga cikin abokan mijin ya mutu.
Yarinyar ta amsa laifin saka gubar, sai dai kuma ta ce tsohon saurayinta wanda ɗanuwanta ne ya ba ta gubar domin ta saka wa mijin nata da abokansa a abinci.
Sai dai tsohon saurayin ya ce ba ya garin lokacin da yarinyar ta je garin. Yanzu haka yarinyar tana tsare a hannun ƴansanda inda shi kuma saurayin ke tsare a gidan yari. Alƙali ya ɗaga shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairun 2025.
Asalin hoton, Reuters
Katafaren kamfanin Meta Amurka da ya mallaki Facebook ya sanar da cewa zai cire manhajar da ke binciken gaskiya daga ayyukansa tare da maye gurbinta da tsarin da ake kira "community notes" irin na shafin X.
Za a fara aiwatar da sauye-sauyen a Amurka kuma za su shafi Facebook da Instagram da kuma Threads.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, shugaban Meta, Mark Zuckerberg, ya ce lokaci ya yi da za a dawo da 'yancin fadin albarkacin baki, kuma masu binciken kwakwaf sun zama "masu nuna son zuciya a harkar siyasa".
Matakin na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki ƙalilan zababben Shugaban Ƙasa Donald Trump ya sha rantsauwar kama aiki.
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, Manuel Photography
Asalin hoton, EPA
Ɗansiyasar Faransa mai ra'ayin rikau, Jean Mari Le Pen, ya rasu yana da shekaru 96.
A shekarar 1972 ne Le Pen ya kafa jamiyyar National Front domin nuna matuƙar adawa kan shige da fice da aikata laifuka.
Marigayin ya shafe tsawon shekaru a matsayin jigon da ke kawo rarrabuwar kawuna a Faransa.
Duk da cewa mutum ne mai gajaren hakuri amma yana da kishin kasa da kuma kwarjini.
Ya riƙa janyo cecekuce kan kalaman da ya yi kan wariyar launin fata da kyamar Yahudawa.
Bai taɓa lashe zaɓe ba amma ya taɓa kaiwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasa, inda ya sha kaye a hannun Jack Chirak.
Marigayin ya samu saɓani da ƴarsa, Marine Le Pen wadda ta karɓi ragamar shugabancin jamiyyarsa kuma ta sauya mata suna zuwa National Rally.
Asalin hoton, Getty Images
Masana kimiyya a ƙasar Austria sun samar da wata hanyar daƙile yaduwar ƙwari ta yadda mazansu za su ɗura wa matan guba a lokacin saduwa.
Hanyar na aiki ne ta yadda mazan ke ɗauke da guba a cikin maniyyinsu, wadda aka samo daga gizo-gizo da kuma wasu halittun ruwa.
Nazarin wanda aka yi a Jami'ar Macquarie, wanda aka gwada a kan wani nau'in ƙuda, ya sanya tsawon rayuwar matan ƙudajen ya ragu da kusan kashi biyu cikin uku.
Yanzu suna yin gwajin a kan sauro a ƙoƙarin rage yaɗuwar cuta.
Ana hasashen tsarin zai rage yawan matan sauro da kashi 40 zuwa 60 cikin 100.
Asalin hoton, Atiku Abubakar
Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soki jam'iyyar APC bisa kalaman da sakataren watsa labaranta na ƙasa, Felix Morka ya yi game da bayanin sabuwar shekara na tsohon ɗantakarar jam'iyyar LP, Peter Obi, inda Obi ya ce kalaman tamkar barazana ce ga rayuwarsa.
Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce, "Wannan barazanar, da cigaba da riƙe ɗan gwagwarmaya Mahdi Shehu, abin takaici ne, kuma tamkar kama hanyar mulkin kama-karya ne, inda ake shaƙe ƴan hamayya."
Ya ce kalaman sakataren watsa labaran na APC cewa Obi "ya wuce iyaka", "ba su da muhalli a cikin al'ummar da ke da girmama ƴancin furta albarkacin baki. Don haka ya kamata APC ta bai wa Obi da ƴan Najeriya haƙuri."
"Dimokuraɗiyya ta gaskiya tana girmama adawa da suka mai ma'ana, domin ana amfani da adawar irin su Peter Obi ne a matsayin gudunmuwarsu wajen ciyar da ƙasar gaba.
Ya ƙara da cewa ba su san me Morka yake nufi da ya ce Obi ya shirya ɗanɗana ƙudarsa ba, "ya kamata jam'iyya mai mulki ta fayyace me yake nufi, domin ba za a aminta da irin waɗannan kalaman ba."
Asalin hoton, Murtala Sule Garo/Facebook
Tsohon ɗantakarar mataimakin gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo ya ce adawar siyasar da ke tsakanin tsofaffin gwamnoni na hana jihar ci gaba.
Garo ya kuma yi kira ga jagororin siyasar jihar su mayar da kubensu, tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ciyar da jiharsu gaba.
Garo ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ya ce, "babu daɗi ganin jihohi irin Zamfara da ba ta kai Kano ba, tsofaffin gwamnoninta suna ajiye bambancin siyasa suna haɗuwa domin ciyar da jihar gaba. Mu a nan Kano, da wahala ka samu tsofaffin gwamnoni sun haɗu domin tattauna hanyoyin da za a magance matsalolin jihar."
"Ina kira ga tsofaffin gwamnoninmu, idan har da gaske suna ƙaunar Kano, su haɗa kai. Ba a samun ci gaba da rabuwar kai. Dole jagororin siyasar jihar su ajiye bambancin siyasa su yi aiki a tare domin ci gaban jihar."
Asalin hoton, Nigeria Police
Ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja ta ce an gano masu sayen murafan ƙarfe na hanyoyin ruwan titunan Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ministan Abuja, Lere Olayinka ya fitar, ya ce wani kamfanin sarrafa ƙarafa mai suna Abuja Steel Company, na cikin waɗanda ake zargi da sayen ƙarafan da ake sacewa.Sanarwar ta ce kamfanin yana kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ne, sannan an gano wasu daga cikin 'ƙarafan da ake nema'.
"Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda suke da hannu wajen sacewa da sayarwa da ma sayen ƙarafan."
Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda aka kama ɗin suna bayar da haɗin kai a binciken da ake yi, "sannan tuni Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayar da umarnin musanya murafan."
Asalin hoton, REUTERS/KCNA
Koriya ta Arewa ta bayar da cikakkun bayanai game da abin da ta bayyana a matsayin sabon makami mai linzami mai cin matsakaicin zango wanda ta gwada da sanyin safiyar Litinin.
Kafofin watsa labaran gwamnatin ƙasar sun ce makamin ya yi tafiyar kilomita 1,200 kafin ya faɗa a cikin tekun Japan.
Pyongyang ta ce ba kasafai ne za a iya gano makamin a lokacin da yake tafiya a iska ba kuma an yi shi ne don razana abokan hamayyarta.
Amurka da Japan sun yi alla-wadai da gwajin makamin wanda ke zuwa makonni biyu kafin a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka.
Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Amurka ta saki wasu fursunoni 11 ƴan asalin ƙasar Yemen daga gidan yarin Guantanamo Bay ta kuma aika da su Oman.
Yanzu fursunoni 15 ne kawai suka rage ana tsare da su a gidan yarin.
Wakilin BBC ya ce daga cikin mutum 15 da suka rage a Guantanamo, biyu an yanke musu hukunci sannan bakwai ana tuhumarsu da aikata laifuka ne.
A shekarun baya fursunonin da aka tsare a gidan yarin sun kai 800.
Asalin hoton, X/DEFENCE HQ
Rundunar tsaron Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan harin da ƙungiyar Iswap ta kai wa sojojin ƙasar a sansaninsu da ke jihar Borno, a arewa maso gabashin ƙasar.
Rahotanni sun ce harin na mayaƙan Iswap ya yi ajalin aƙalla sojojin Najeriya shida a sansanin sojojin da ke Damboa a ranar Lahadi, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito, inda ta ce tsagin Boko Haram na Iswap na Boko Haram ne ya kai harin.
Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da harin, amma bai yi bayani kan adadin waɗanda aka kashe ba.
Sai dai ya ƙara da ecwa, "mun fara bincike kan lamarin. Za mu fitar da sanarwa game da harin nan kusa," kamar yadda ya bayyana wa BBC.