window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Isyaku Muhammad, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Juma'a.

    Za mu kawo muku rahotonnin gobe da safe a wani shafin.

    Kafin nan, Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An kashe mutane da dama bayan kai wa jirgin MDD hari a Sudan ta Kudu

    Mutane da dama sun mutu a Sudan ta Kudu sakamakon buɗe wa jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) wuta da suka yi yunƙurin kwashe dakarun sojan ƙasar.

    Ma'aikacin cikin jirgin ɗaya ya mutu lokacin da aka buɗe wa jirgin na helikwafta wuta, in ji MDD.

    Ta ƙara da cewa an kashe wani janar na Sudan ta Kudu da sauran dakaru lokacin kwashe mutanen a jihar Upper Nile.

    MDD ta ce harin da aka kai wa jirgin nata zai iya zama "laifin yaƙi".

  3. Layin lantarki na Najeriya ya samu matsala

    Lantarki

    Asalin hoton, TCN

    Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun ce sun fuskanci matsala a yau Juma'a daga babban layin wutar, abin da ya jawo jefa sassan ƙasar cikin duhu.

    Kamfanin lantarki na Kedco - da ke bai wa jihar Kano da maƙobtanta wuta - ya nemi afuwar kwastomominsa cikin wata sanarwa.

    "Muna masu baƙin cikin sanar da ku cewa an samu matsala a layin lantarki da misalin ƙarfe 2:00 na rana...abin da ya sa ba mu iya bai wa kwastomominmu wuta ba kenan," in ji Kedco cikin wata sanarwa a shafukan zumunta.

    Shi ma kamfanin lantarki na Ikeja Electric - mai bai wa jihar Legas da maƙobtanta wuta - ya fitar da irin wannan sanarwa. Sai dai dukkansu sun ƙi bayyana nau'in matsalar da aka samu, kuma ba su alaƙanta hakan da babban layin lantarki na ƙasa ba.

    Akasari irin wannan na faruwa ne idan babban layin lantarki na ƙasa ya lalace, wanda yake yawan samun matsala.

    Kazalika, kamfanin kula da rarraba wutar na gwamnati Transmission Company of Nigeria (TCN) bai ce komai ba game da matsalar.

    Rashin wutar na yau ya shafi wasu sassa, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

  4. Poland za ta bai wa dukkan mazan ƙasar horon yaƙi

    Poland

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Ministan tsaro na Poland Wladyslaw Kosiniak-Kamysz yake gaisawa da dakaru yayin yarjejeniyar sayen jiragen yaƙi

    Firaministan Poland Donald Tusk ya ce suna shirin horar da dukkan maza manya na ƙasar dabarun yaƙi.

    "Za mu yi ƙoƙarin samar da wani tsari kafin ƙarshen shekarar nan saboda kowane namiji babba ya samu horon yaƙi ko da za yaƙin ya taso," in ji shi yayin wani jawabi a majalisar dokokin ƙasar.

    "Wannan shirin zai yi daidai da barazanar da muke fusnkanta."

    Ya kuma ce yana goyon bayan Poland ta fice daga yarjejeniyar Ottawa da ta haramta amfani da abin fashewa da ake kira anti-personnel landmines a Turance, da ma wadda ta hana amfani da bam mai 'ya'ya.

    Mista Tusk ya ce yana ganin ya kamata Poland ta dinga kashe kashi 5 cikin 100 na arzikinta a kan tsaro. A wannan shekarar, gwamnati ta ware kashi 4.7 a kan tsaron, kuma shi ne mafi yawa a tsakanin mambobin ƙungiyar tsaro ta Nato.

  5. Trump na nazarin ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

    Trump da Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump y ace yana duba yiwuwar ƙaƙaba wa Rasha sababbin takunkumai da haraji sakamakon ruwan wuatr da ta yi wa Ukraine da tsakar dare.

    “Bisa ruwan wutar da Rasha ke yi kan Ukraine a fagen yaƙi yanzu, ina duba yiwuwar saka manyan takunkumai kan bankuna, da haraje-haraje kan Rasha har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta," in ji shi cikin saƙon da ya wallafa.

    "Rasha da Ukraine, ku zauna ku tattauna yanzun nan, kafin lokaci ya ƙure. Na gode!!!"

  6. Hisbah ta kulle shagon cacar 'betting' a Kano

    ma'aikatan Hisba

    Asalin hoton, Hisba

    Hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kulle wani shagon da ake gudanar da cacar wasanni ta zamani da ake fi sani da 'betting''.

    Mataimakin kwamandan hukumar na jihar, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ne ya tabbatar da haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Aminudeen ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bisa dokokin jihar ta Kano.

    Ya ƙara da cewa hukumar ta rufe shagon ne bayan da ta kai samame wurin.

    Mataimakin kwamandan ya ce abin akwai ban taƙaici, yayin da musulmai ke zuwa suna caca a daidai lokacin da ake tsaka ada azumin watan Ramadan.

    An fara aiki a dokokin shari'ar addinin musulunci a Kano tun 2000, kamar yadda yake a wasu jihohin ƙasar 11 da ke arewacin ƙasar, inda aka haramta karuwanci da caca da shan giya.

  7. PDP ta yi allawadai da dakatar da Sanata Natasha

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, PDP ta yi allawadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa bayan zargin shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio da cin zarafinta.

    Jam'iyyar ta bayyana takaicinta kan yadda a cewarta aka yi gaggawar dakatar da Natasha, "ba tare da an gudanar da binciken ba sani ba sabo ba kan zargin da ta yi wa shugaban majalisar."

    Wannan jawabin na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar PDP na ƙasa Debo Ologunagba, ya fitar, inda ya ce majalisar tana "amanna tare da rufa-rufa domin ba mai laifi kariya."

    "Dakatar da ita na wata shida hana mutanen Kogi ta Tsakiya wakilci ne, wanda haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya ba su."

    PDP ta ce kamata ya yi shugaban majalisar ya kare kansa daga zargin ta hanyar sauka daga jagorantar zaman tattauna batun, kasancewar shi ake zargi matuƙar "babu wani da yake ɓoyewa. Wannan ba ƙaramin abin kunya ba ne ambaton shugaban majalisar dattawa zarginsa da cin zarafi, wanda ɓata sunan majalisar ne baki ɗaya."

  8. Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin kama masu sare bishiyoyi

    Itace

    Asalin hoton, Kano State Ministry of Environment and Climate Change

    Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah wadai da wasu da suka kira 'ɓata-gari' masu sare bishiyoyi ba bisa ƙa'ida ba a kan titin Jigawa.

    Kwamishinan Muhallahi da sauyin yanayi na jihar Dakta Dahir M Hashim ya ce ma'aikatarsa ba za ta lamunci wannan abu da ya bayyana da ''ɗanyen aiki'' ba.

    ''Abu ne da ba za mu lamunta ba, a riƙa sare mana bishiyoyinmu na gargajiya, duba da muhimmancin bishiyoyi wajen kare muhalli da inganta rayuwar al'umma'', kamar yadda kwamishinan ya bayyana a shafinsa na Facebook.

    Dakta Hashim ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da hannu a wannan laifi domin gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abin da suka aikata.

    Kwamishinan ya ce duk wanda ke da buƙatar sare bishiya, dole ne ya sanar da ma'aikatar muhalli domin samun izini kafin aiwatar da hakan.

    Kwamishinan ya jaddada aniyar gwamnati n jihar na kare muhalli da ci gaba da yaƙi da duk wani aikin da zai haifar da illa ga yanayi da muhalli.

  9. Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa taliya mai inibi da kaza

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    A filinnmu na girke-girken Ramadan, mun kawo muku yadda ake haɗa salad mai inibi tare da taliya mai kaza da broccoli, da kuma samosa.

    Ku biyo mu ku ga yadda ake haɗin tare da Hindu Abdulwahab Ja'afar da aka fi sani da Chef Hindu ko kuma @halfhadian a soshiyal midiya.

  10. Za a harbe mutumin da ya kashe iyayen budurwarsa a Amurka

    ...

    Asalin hoton, South Carolina Department of Corrections

    Za a zartar da hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga kan wani mutu da ake tsare da shi a wani gidan yari da ke jihar South Carolina ta Amurka, bayan samun shi da laifin kashe iyayen budurwarsa ta hanyar dukan su da sanda.

    Mutumin zai kasance na farko da aka kashe ta wannan tsari a cikin shekara 15.

    A lokacin zartar da wannan hukunci kan mutumin mai suna Brad Sigmon a yau Juma'a da ƙarfe 11:00 na dare a Amurka, maharba uku riƙe da bindiga za su harbe shi a lokaci guda a kan ƙirjinsa ta hanyar amfani da wasu alburusai na musamman.

    Tsarin aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar bindiga ya tanadi cewa za a ɗaure mutumin ne a kan kujera a cikin ɗakin zartar da hukuncin, inda kuma za a sanya alamar wurin da za a harba a daidai ƙashin zuciya.

    An samu Sigmon, mai shekara 67 a duniya da laifin kisan iyayen budurwarsa David da Gladys Larke a shekarar 2001, kafin yin garkuwa da ita budurwar tasa.

    Daga baya ta samu tsira daga hannun shi yayin da ya bi ta da harbi.

    Duk da cewa an bai wa Sigmon zaɓin hukunci ta hanyar lantarki ko kuma allurar mutuwa, lauyansa ya ce ya zaɓi hanya mafi tsanani ne kasancewar bai yarda da aikin sauran hanyoyin biyu ba.

    Shi ne zai zama mutum na farko da za a zartar wa hukuncin kisa ta hanyar harbin bindiga tun shekara ta 2010, kuma zai kasance mutum na huɗu da aka taɓa zartar wa hukuncin ta wannan hanya tun bayan da Amurka ta dawo da aiwatar da hukuncin kisa a 1976.

  11. Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila zai yi ritaya

    Rear iral Daniel Hagari

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Rear iral Daniel Hagari

    Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa mai magana da yawunta, Rear iral Daniel Hagari zai ajiye muƙaminsa haka nan kuma zai yi ritaya daga aiki.

    Daɗaɗɗen kwamandan a rundunar sojin ruwa ta Isra'ila ya zamo mutumin da aka fi jin sunansa tun bayan harin da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya zamo mafarin ƙazamin yaƙin da aka tafka tsakanin ƙasar da ƙungiyar Hamas a baya-bayan nan.

    Lokacin sanar da matakin, rundunar sojin Isra'ila ta ce ya yi "aiki a ɗaya daga cikin lokuta mafiya sarƙaƙiya na yaƙe-yaƙen da ƙasar ta shiga a tarihinta, kuma ya yi aiki bisa ƙwarewa da jajircewa".

    Sai dai an samu lokuta da dama da aka samu saɓanin ra'ayi tsakaninsa da gwamnati.

    Ɗaya daga cikin irin waɗannan lokuta shi ne lokacin da Hagari ya bayyana damuwar sojojin Isra'ila kan rashin kyakkyawan tsarin tafiyar da Gaza bayan kammala yaƙi, a shekarar da ta gabata.

    Ana sa ran cewa Kanar Beni Aharon - wanda ya kasance kwamandan dakarun da ke kula da tankokin yaƙi a lokacin yaƙin Gaza - ne zai maye gurbinsa.

  12. An ƙaddamar da rundunar tsaron makarantu da gine-ginen gwamnati a Jigawa

    Umar Namadi

    Asalin hoton, Umar Namadi/X

    Gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar da cibiyar kula da ayyuka ta rundunar kai ɗaukin gaggawa ga makarantu da sauran mahimman gine-gine gwamnati.

    Cibiyar za ta zama matattarar samun bayanai da sanya ido kan duk wata barazana don kai ɗaukin gaggawa.

    Ƴanbindiga sun sha kai hari makarantu a sassan Najeriya inda aka yi garkuwa da ɗalibai ciki har da mata da dama, lamarin da ya sa hukumomi suka ɓullo da shirin tsare makarantu mai taken "Safe School Initiative".

    Babban aikin cibiyar ta “Safe Schools Rapid Response Coordination Centre” shi ne tattara bayanai da kuma kai ɗauki a duk lokacin da wata matsalar tsaro ta taso a sassan jihar Jigawa.

    Cibiyar ta ƙunshi jami’an ƴansanda da na civil defence da sauran jami’an tsaro.

    Gwamnatin ta sanar da ɗaukar ɗaruruwan matasa ta hanyar haɗin gwiwa da wasu kamfanonin tsaro masu zaman kansu da cibiyoyin gwamnati, don aikin tsare makarantun firamare da sakandare da kuma asibitoci.

  13. Ana buƙatar dala biliyan 11 domin sake gina Lebanon - Bankin Duniya

    Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa aikin sake gina wuraren da aka lalata a Lebanon - lokacin yaƙin Isra'ila da Hezbollah zai laƙume dala biliyan 11.

    Yaƙin ya faro ne a wato Oktoban 2023 lokacin da Hezbollah ta fara harba makamai zuwa Isra'ila da nufin goyon bayan Hamas a Gaza.

    A watan Nuwamban bara ne dai ɓangarorin biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

  14. Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdullahi Abba Zariya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Sheikh Abdullahi Abubakar Abba Zaria wanda mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zaria ne ya yi karatunsa na firamare da sakandare da jami'a duka a birnin na Zazzau.

    Sheikh Abdullahi ya ce ya tasirantu da kakansa na wurin mahaifiya, wani shahararren malami ne inda ya zauna a zaurensa domin samun karatun al-Qur'ani.

  15. WHO za ta aike wa Najeriya maganin lalurar kuturta

    Mai lalurar

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce za ta aika magungunan cutar kuturta zuwa Najeriya, bayan magance jinkirin da aka samu, lamarin da ya sa dubban masu ɗauke da cutar a ƙasar suka shafe shekara guda ba tare da samun magani ba.

    Najeriya - wadda ta bayar da rahoton samun dubban sabbin waɗanda suka kamu da cutar - ta kasance ba ta da maganin cutar saboda riƙe magungunan da aka yi bayan ɓullo da sabbin dokokin gwaji.

    Kuturta cuta ce da ake iya maganinta da magunguna daban-daban. Kuma kasancewa Najeriya ta shafe tsawon shekara guda ba tare da maganin ba, jikin wasu masu ɗauke da cutar ya tsananta, sakamakon cutar da ke yanke yatsun hannu da ƙafa tare da shafar ƙwaƙwalwa.

    Da dama cikin marasa lafiyar an sallame su daga asibiti domin komawa gida, wani abu da ke ƙara hatsarin yaɗa cutar.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta buƙaci Najeriya ta ɗage sabbin dokokin gwajin magungunan, inda yanzu kuma ake sa ran rukunin farko na magungunan su isa ƙasar ranar Asabar daga Indiya.

    Cikin fiye da shekara 40 cutar kuturta ta ragu matuƙa a faɗin duniya. Amma Najeriya na bayar da rahoton samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar fiye da 1,000 a shekarar da ta gabata.

    Akwai fiye da mutum 10,000 da ke kamuwa da cutar cikin shekara guda a ƙasashen Brazil da Indiya da kuma Indonesia.

  16. Gwamnan jihar Sokoto ya raba kayan haihuwa da magunguna

    Gwamnan jihar Sokoto

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya raba kayan haihuwa da magunguna ga ƙananan hukumomin jihar, waɗanda kuɗinsu suka kai naira biliyan 1.5.

    A lokacin ƙaddamar da rabon a ranar Alhamis, gwamnan ya ce kayan sun ƙushi magunguna da kayan da ake buƙata lokacin haihuwa domin kare lafiyar mata a yankunan da ke da nisa da asibitoci.

    Kayan haihuwar sun haɗa da safar hannu da tabarmin haihuwa da kayan kula da jariri.

    Ahmed ya ce "wannan wani mataki ne domin tabbatar da cewa babu wata mace da ta haihuwa a cikin mummunan yanayi."

    Ana sa ran kayan da aka raban za su taimaka wajen rage mace-macen mata masu juna biyu a jihar, wadda ke cikin jihohin da ake samun yawan mutuwar ƙananan yara da mata masu juna biyu a Najeriya.

    ...

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    ...

    Asalin hoton, Sokoto State Government

  17. Tsohon mai magana da yawun shugaban Najeriya, Doyin Okupe ya rasu

    Doyin Okupe

    Asalin hoton, Doyin Okupe/Facebook

    Tsohon mai magana da yawun shugaban Najeriya, Doyin Okupe ya rasu yana da shekara 72 a duniya.

    Cikin sanarwar ta'aziyya da fadar shugaban Najeriya ta fitar, shugaban Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da gwamnatin jihar Ogun.

    Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ɗan kishin ƙasa, wanda ya bayar da gudunmawa wajen inganta ƙasar.

    A shekarar da ta gabata ne Doyin Okupe ya ce ya yi fama da cutar kansa.

    Marigayin - wanda tsohon likita ne kafin shigarsa siyasa - ya zama jigo a jam'iyyar PDP.

    Toshon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya naɗa shi muƙamin babban mataimakinsa na musamman kan harkokin hulɗa da jama'a.

    A zaɓen 2023, ya kasance babban daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar LP.

    Sai dai daga baya ya fice daga jam'iyyar saboda abin da ya bayyana da ''sauka daga layin manufofinta''

  18. 'Dakatarwar da aka yi min ba za ta hana ni ci gaba da hidimta wa al'ummata ba'

    Natasha

    Asalin hoton, Others

    Ƴar majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta tsakiya da mambobin majalisar suka dakatar, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana dakatarwar da aka yi mata a matsayin 'zalunci'

    A ranar Alhamis ne majalisar ta amince da dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida saboda zargin ''saɓa ƙa'idar aiki'' bayan saɓanin da ya shiga tsakaninta da shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Fesbuk, Sanata Natasha ta yi zargin cewa dakatarwar da aka yi mata ba a bi ƙa'ida ba, kuma an yi hakan ne domin a rufe mata baki.

    ''Dakatarwar da aka yi min ba bisa ƙa'ida ba, ta ci karo da dokokin adalci, kuma hakan ba zai hana ni ci gaba a hidimta wa al'ummar da nake wakilta ba'', a cewar ta

    Da farko dai saɓanin ya fara ne da sauya wa ƴar majalisar wurin zama a zauren, kafin daga baya ta zarge shi da yunƙurin cin zarafinta ta hanyar lalata.

  19. Ƙwararru na fafutikar kwance katafaren bam ɗin yaƙin duniya a Faransa

    Ƙwararru a birnin Paris na ƙasar Faransa na ƙoƙarin kwance wani bam da aka dasa tun lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, lamarin ya yi sanadin rufe tashar jirgin ƙasa ta birnin mai cike cunkoson jama'a.

    Ƴansanda sun rufe titin jirgin da ke zuwa da fito daga tashar jirgin ƙasa ta Gare du Nord bayan da masu aikin kula da titin suka gano bam a kusa da turakun titin a gundumar Saint-Denis.

    Tashar na ɗaukar fasinjoji kusan 7,000 a kowace rana, daga ciki da wajen Faransa.

  20. Sudan ta shigar da UAE ƙara a Kotun Duniya ta ICJ

    Shugaban mulkin sojin Sudan

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasar Sudan ta shigar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ƙara a gaban Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta ICJ, kan zargin ta da hannu a kisan kiyashin da ƙungiyoyi ke yi kan ƙabilun da ba na Larabawa ba a yankin Darfur.

    Sudan na zargin ƙasar ta UAE da samar wa mayaƙan RSF tallafin soji da kuɗi a yaƙin basasar da gwamnati ke yi da RSF.

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - wadda a baya ta sha musanta zargin hannu a taimaka wa RSF - ta bayyana ƙarar a matsayin ''neman suna''.

    Dubban mutane ne aka kashe tare da raba miliyoyi da muhallansu tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar tsakanin sojoji da mayaƙan RSF, kusan shekara biyu da suka gabata.