Sai da safe
Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafin na ranar Juma'a.
Muna tafe da wasu sababbin rahotonnin da suka shafi rayuwarku gobe da safe.
Kafin lokacin, kuna iya duba ƙasa domin ganin yadda duniyar ta kasance a Juma'ar.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/02/2025
Usman Minjibir, Annur Mohammad, Isiyaku Muhammed, Haruna Kakangi, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafin na ranar Juma'a.
Muna tafe da wasu sababbin rahotonnin da suka shafi rayuwarku gobe da safe.
Kafin lokacin, kuna iya duba ƙasa domin ganin yadda duniyar ta kasance a Juma'ar.
Asalin hoton, @OfficialBenKalu
Kwamatin da ke aiki kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar wakilan ƙasar ya ce ƙudirori da aka gabatar na ƙirƙiro jihohi 31 ba su cika sharuɗɗa ba.
Shugaban kwamatin kuma mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Okezie Kalu, shi ne ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin wani taron horarwa a jihar Akwa Ibom da ke kudancin ƙasar.
Mista Kalu ya ce duk da cewa buƙatun da aka gabatar sun nuna sha'awar al'ummomi na samun jiha, ba su cika sharuɗɗan da kundin mulki ya tanada ba.
"A dalilin haka, mun tsawaita wa'adin karɓar ƙudirorin zuwa 5 ga watan Maris na 2025. Amma za a iya ƙara wa'adin bayan kammala wannan taron idan muka fahimci akwai sauran ƙalubale," in ji shi.
"Amma a sani cewa babu ko ɗaya daga cikin waɗanda aka kawo mana da ya cika sharuɗɗan da Sashe na B na kudnin mulki ya shimfiɗa."
Ɗaya daga cikin likitocin da suke kula da lafiyar Fafaroma Francis ya ce duk da sauƙin da yake samu har yanzu rayuwarsa na cikin haɗari.
Farfesa Sergio Alfieri ya ce akwai yiwuwar zai kai mako mai zuwa a asibiti.
Likitan ya ƙara da cewa mara da zuciyar jagoran ɗariƙar Katolika mai shekara 83 suna nan lafiya ƙalau.
Asalin hoton, TCN
Kamfanin kula da rarraba lantarki a Najeriya na Transmission Company of Nigeria (TCN) ya ce wasu sassan Abuja babban birnin Najeriya za su afka cikin duhu a ƙarshen mako saboda gyara da zai yi a kan na'urorinsa.
Wata sanarwa a ranar Juma'a ta ce za a gudanar da aikin ne na shekara-shekara a ranar Asabar da Lahadi, wanda zai jawo ɗaukewar wutar na wasu awanni.
"Za a yi aikin daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 4:00 na yamma a ranakun," a cewar sanarwar da kakakin TCN, Ndidi Mbah, ya fitar.
"Yankunan Garki Area 1, da Asokoro, da Apo Legislative Quarters, da Apo Resettlement, da Gudu, da Apo Mechanic, su ne za su rasa wutar a ranakun Asabar da Lahadi na tsawon awa bakwai," in ji shi.
Asalin hoton, EFCC
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ta ce ta miƙa wa 'yan ƙasar waje kuɗinsu dala 127,892 (ko kuma naira miliyan 70.60) da ta ƙwato daga hannun 'yan damfara.
An miƙa kuɗaɗen ne a hukumance yau Juma'a yayin taron manema labarai ga wakilan ƙasashen Amurka, da Sifaniya, da Switzerland waɗanda aka damfara daga Najeriya.
Charles Smith, wanda jami'in hukumar tsaro ta FBI ne a Amurka, ya karɓi dala 26,581 (naira N40,602,841.46) a madadin 'yan Amurka da aka damfara.
Bugu da ƙri, EFCC ta miƙa motoci biyu na alfarma, da wani gida da ke Unguwar Maigero a jihar Kaduna domin mayar wa mutanen.
Jakadan Switzerland ma a Najeriya, Andreas Baum, ya karɓi dala 100,011.43 don mayar wa 'yan ƙasarsa da aka damfara a Najeriya.
Sai kuma muƙaddashin jakadan Sifaniya a Najeriya, Maria Velasco, da ya karɓi dala 1,300.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Firaministan Birtaniya Keir Starmer da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ba su taɓuka komai ba wajen kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine.
Da yake magana yayin wata hira da kafar talabijin ta Fox News, an tambayi Trump kan ganawar da zai yi Mista Starmer da Macron, sai ya ce: "Ba su yi komai ba...ba su tattauna da Rasha ba!".
"Ba su yi komai ba," kamar yadda ya maimaita.
"Macron abokina ne", in ji Trump, yana mai cewa cewa "Starmer mutumin kirki ne" amma kuma babu wanda ya yi wani abu game da Rasha.
Asalin hoton, Nigeria Police
Mutum huɗu sun mutu sakamakon rikici game da wani fili tsakanin garuruwa biyu na jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne tsakanin mazauna ƙauyukan Ogwor da Umuobor saboda wani yanki da ake kira Elueke.
Rahoton ya ce gwamnatin jihar ta ayyana yankin a matsayin "ba na kowa ba" a farkon watan Janairu, kuma ta umarci duka ƙauyukan su ƙaurace wa yankin.
"Daga cikin mutum huɗu da aka kashe, an ce uku sun je nome doya ne a yankin ranar Laraba, kafin a kashe wata mace a ranar Litinin," a cewar Chinasa Okorie, shugaban cibiyar Akaeze Development.
Sai dai kakakin rundunar 'yansanda a jihar, Joshua Ukandu, ya ce kisan wata mace kawai suka sani a ranar Litinin da ta gabata, amma ya ce suna ci gaba da bincika lamarin.
Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce dakarunta sun yi nasarar kama ƙauyukan Nadiyivka da Novosilka da ke kudancin yankin Donetsk na Ukraine, a cewar rahoton kamfanin labarai na Tass.
A gefe guda kuma, rundunar sojin Ukraine ta ce "Rasha ta yi yunƙuri sau uku don auka wa Novosilka" cikin wani saƙo a dandalin Telegram, amma ba ta ambaci ko Rashar ta yi nasara ba.
Saƙon ya ce Nadiyivka na cikin wuraren da "sojojin abokan gaba suke yawan kai hare-hare".
Lamarin na zuwa ne bayan rundunar sojin Ukraine ta mayar da martani kan wani hari da Rasha ta kai da sojoji marasa matuƙa 160.
Likitoci masu yin tiyata a Birtaniya sun ƙirƙiro wata sabuwar dabara ta ceto idanun yara kanana da aka haifa da matsalar kwayoyin halitta da ke haifar da makanta.
An yi gwaji kan yara huɗu da suka fito daga ƙasashen Turkiyya da Tunisia da Amurka, inda aka musanya masu ƙwayoyin halittar da ke haifar da makantar.
Wakilin BBC ya ce an haifi dukkan yaran da lalurar da za ta sanya su rasa duka ganinsu cikin shekara biyu zuwa uku.
Bayan shekara biyar wani sabon bincike ya nuna cewa yaran sun ci gaba da gani, suna iya rubutu da karatu.
Asalin hoton, PA Media
Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy, ya gargaɗi Rwanda kan abin da ya kira mummunar abin da za ta fuskanta saboda rawar da take takwa a rikicin da ake yi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
Ya ce aikace-aikacen dakarun Rwanda a gabashin Congon tsabagen keta dokokin ƙasa da ƙasa ne.
Ya ce irin wannan ne zai sa rikicin ya bazu zuwa wasu ƙasashen yankin.
Asalin hoton, PRESIDENCY NG
Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta shigo da tan-tan na abinci zuwa ƙasar daga ƙasashen waje, wanda wasu ke cewa hakan ne ya haddasa saukar farashin abinci a kasuwannin ƙasar.
A cikin wata hira da manema, Ministan aikin gona da samar da abinci na ƙasar Farfesa Abubakar Kyari, ya ce duk da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abincin lokacin da farashinsa ya tashi, daga baya ta yi watsi da batun.
Sai dai ya ta'allaƙa saukar da farashin abincin na yanzu ne da yadda jama’a da yawa suka koma gona a daminar bara.
A cewarsa noman da aka yi ne ya yi kyau, wanda shi ne ya sa kayan abincin ya yawaita, sannan ya yi kira ga ƴankasuwa su yi ramgwame domin jama'a su mora.
Asalin hoton, NPF
A Najeriya rahotanni na cewa jami’an tsaro a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar, sun kama wani mai safarar makamai ga ƴanbindiga.
Mutumin mai suna Hamza Suruddubu, ana zargin shi ne da samar wa ƙasurguman ƴanbindigar nan Bello Turji da Boka da kuma Halilu Buzu manyan makaman da suka haɗa da bindigogi da sauran makamai da sauransu.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya kuma ta ce dakarunta sun kashe masu kai hare-hare a faɗin ƙasar har 82 tare da kama 198, kana sun samu nasarar ceto mutum 93 da aka yi garkuwa da su.
Asalin hoton, Getty Images
Fadar Vatican ta ce Fafaroma Francis - da aka kwantar a asibitin birnin Rome na tswon mako guda - na samun sauƙi.
Mai shekara 88 na fama da ciwon sanyi a huhunsa.
An garzaya da fafaroman zuwa asibiti bayan da ya fuskanci matsalar numfashi. Yana dai fama na lalurori masu yawa.
A ranar Alhamis majalisar malaman coci-coci suka sanar da cewa fafaroman na ci gaba da samun sauƙi.
Asalin hoton, Ademola Adeleke/Facebook
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce babu gudu babu ja da baya kan zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari'a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurinta na shirya sabon zaɓen na ƙananan hukumomi.
Ministan ya ce zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da gwamnan ya gada - waɗanda ƴan jam'iyyar APC ne shi kuma ɗan PDP- wa'adinsu bai ƙare ba, don haka bai kamata a cire su ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Olawale Rashed ya fitar, Adeleke, ya ce sun shirya tsaf, kuma babu gudu babu ja da baya kan gudanar da zaɓen.
"Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen jihar da su yi biyayya ga tsare-tsaren dimokuraɗiyya. Mu dai muna amfani da doka da oda ne. Don haka za a yi zaɓe, kuma ina kira ga dukkan ƴan jihar da su gudanar da zaɓen cikin lumana, domin Osun jiha ce da aka santa da zaman lafiya."
Asalin hoton, PA Media
Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas cewa za ta ɗanɗani kuɗarta kan abin da ya kira "zalunci da mugunta" da suka yi na saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan gwaje-gwajen binciken gawarwakin da Isra'ila ta yi ya nuna gawar da aka dawo da ita daga Gaza a ranar Alhamis ba ta ƴar Isra'ila Shiri Bibas da aka yi garkuwa da shi ba ne.
Hamas ta ce da alama an yi kuskuren sanya gawar Shiri Bibas cikin waɗanda aka binne cikin ɓaraguzai bayan wani harin Isra'ila ta sama a Gaza, wanda ta ce shi ne ya kasheta tare da ƴaƴanta biyu maza biyu ƙanana.
Gwajin ya tabbatar da gawarwakin yaran nata biyu da aka mayar ranar Alhamis.
Sai dai Isra'ila ta ce gwajin da aka yi ya nuna cewa ƴan ta'adda ne suka kashe su.
Tuni dai Hamas ta fitar da sunayen mutum shida masu rai da za a sako ranar Asabar
Asalin hoton, UNESCO
Yau ce ranar harshen uwa da Hukumar raya al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO.
Hukumar ta ware duk ranar 21 ga watan Feburairun kowace shekara domin tunawa da harsunan uwa a duk faɗin duniya.
Akwai dai aƙalla harsuna 7,100 da ake magana da su a duniya, sai dai galibinsu ba su da tsarin rubutun zube inda ba a cika amfani da su shafukan sada zumunta ba.
Haka ma hukumar raya al’adun ta UNESCO ta ce akwai kimanin harsuna 3000 da ke fuskantar barazanar ɓacewa a duniya.
Asalin hoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyarsa ce za ta doke manyan jam'iyyun APC da PDP domin samun nasara a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wurin babban taron jam'iyyar NNPP a Abuja a ranar Alhamis, inda ya ce ƴan Najeriya ba sa jin daɗin yadda gwamnati take gudana a yanzu.
"Na yi amannar cewa idan za a yi zaɓe sahihi a ƙasar nan, jam'iyyarmu ce za ta samu nasara, domin za ta kayar da APC da PDP da duk sauran jam'iyyun ƙasar nan," in ji shi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A game da batun cewa NNPP ta dare gida rabu, Kwankwaso ya ce babu wani rikici a jam'iyyar, inda ya ce "bai kamata a yi maganar ba ma, domin na san akwai masu samun abinci a sanadiyar wannan saɓani. Amma su sun san wasa suke yi."
Kwankwaso ya yaba wa ƴan Najeriya bisa ƙaunar da suka nuna masa ba, inda ya ce, "ƴan Najeriya ba sa jin daɗi. Akwai talauci a ƙasar, akwai matsalar tsaro, sannan ababen more rayuwa sun taɓarɓarewa, kuma ba ma ganin wata huɓɓasar magance su," in ji shi.
Asalin hoton, Reuters
Nan gaba ne shugabannin ƙasashen Larabawa za su yi taro a Riyadh na ƙasar Saudiya domin tattauna tsare-tsaren sake gina Gaza.
ƙasashen Larabawa sun nuna rashin amincewarsu kan ƙudurin Donald Trump na cewa Amurka za ta mallaki Gaza tare da rarraba Falasɗinawa zuwa wasu ƙasashen Larabawa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa raba Falasɗinawa da muhallansu ya saɓa wa doka kuma hakan daidai yake da shafe su daga doron ƙasa.
Shugabannin Larabawan za su kuma duba waye ya kamata ya biya kuɗin sake gina Gazar da kuma tafiyar da shugabancinta bayan kammala yaƙi.
Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Mexico sun ce sun kama wani ƙasurgumin mai harƙallar ƙwayoyin Sinalowa, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi daba masu ƙarfi a ƙasar.
Hosé Ángirl Canobiyo da aka fi sani da "El Gürito", ana da yaƙinin shi ke shirya yadda ƙungiyar ke safarar Fentanyl zuwa Amurka.
Sannan mahukunta Mexico sun ce shi ke jagorantar ba da tsaro ga ɗaya daga cikin yaran madugun ƴan ƙwaya da ke gidan yari, Huwakin "El Chapo" Guzmán.
Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar CG Musa ya nanata buƙatar da ke akwai na haɗin gwiwa tsakanin sojoji da kafofin watsa labarai domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Musa ya bayyana haka ne a wani taro da ƙungiyar ƴanjarida ta ƙasar reshen jihar Kaduna ta shirya, inda ya ce ƴanjarida na da rawar da za su taka wajen wayar da kan al'umma ta hanyar watsa labarai masu muhimmanci, da ma haɗin kan ƙasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Janar Musa, wanda Birgediya Janar Mohammed Kanah ya wakilta, ya ce "haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ƴanjarida na da matuƙar muhimmanci, domin aikinmu na da muhimmanci sosai wajen gina ƙasa da saita ta.
"A daidai lokacin da sojoji suke bayar da tsaro da tabbatar da tsaro, su kuma ƴanjarida su ne suke sa ido, da bin diddigi domin tabbatar ana aikin yadda ya dace. Sai dai haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu na fuskantar ƙalubale, ciki har da yaɗa labaran ƙarya."
Domin magance wannan matsala, Janar Musa ya yi kira da a ƙara fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu, sannan ya buƙaci a ci gaba da horar da ƴanjarida.